BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

kasa daurewa yayi, wayarshi yajawo yakuma kiranta tana d’auka takara akunne kamar azabar dataji dafarko ta’karaji nanma wani nishi tayi saiga santaleliyar yarinya, tana fad’owa ta kyanyara kuka, shima namijin datafara haihuwa kukan yake.

Jabir yaji and’au waya yanata hellow hellow yaji shiru sai kukan jarirai yakeji, ai take ya’karama motarsa gudu.

Nusaiba kuwa lokacin sukayi sallama da Abdul d’inta yatafi danta shedamashi tabaro auntynta kamar batajin dad’i.

Aiko tana shiga tundaga falo tafara jiyo kukan jarirai ai dagudu tanufi d’akin dataji kukan tana zuwa tafad’a d’akin batare da tunanin komeba.

Toxali tayi da santala-santalan baby’s sunata tsala kuka, Hassana kuma tana dur’kushe kusa dasu lokacin ko cibi ba’a yankemasuba.

Nusaiba cikin tsananin mamaki tace “aunty haihuwa, kuma twowins mashaAllah,

Murmushi Hassana tayi tagayamata inda zata d’auko mata zare da reza tayi karanbani ta yanke cibi tasa zare ta daure, sannan tasakasu cikin zani tashiga kewaye tahad’a ruwan zafi wanka kawai tayi tafito.
Lokacin nusaiba tagama gyara gurin tsaf tasa morning wash tayi morping tafesa freshener lokaci d’aya d’akin yad’au kamshi.

Lokacin da jabeer ya’karaso sai taradda Hassana yayi fess da ita ba ‘katon ciki, wani farinciki ya mamayeshi lokacin dayaga baby’s d’inshi sunata wutsil-witsil cikin zanensu.

Godiya yayima Allah sannan yabugama mamanshi, bajimawa sai gata tazo ita ta wanke baby’s lokacin labarin haihuwar Hassana yagama zaga Dangi,

Daga can gidan su Hassana akasamo wacce ke kula dasu kullum zatayima baby’s wanka tayima Hassana, har kwana bakwai.

Ranar suna ansha shagali, yara sun amsa sunansu Hassan da Hussaina.

Hussaina kuwa saida tayi kuka dan tunowa da ‘yar’uwarta da yanzu itace zata haifama jabeer wannan baby’s d’in.

** ** **

Bayan wata d’aya da haihuwar Hassana akayi bikin nusaiba, inda aka kaita unguwar g r a gidanta yahadu Bakin iya had’uwa, Hassana ansha hidimar biki dan sune ‘kirjin biki kome za’a itace gaba.

Nusiba kuwa sai nan-nan take da ‘yan’biyu hotuna kau sunshasu, dan yaranne dole su burgeka yara yan wata d’aya amma idan ka gansu zakace sunyi wata ukku jikinnan nasu 6ul-bul mashaAllah.


Alhmdlh anan nakawo ‘karshen wannan littafi nawa, gaisuwar bar girma gareku masoyana aduk inda kuke Zee Elkaseem (Mmm khady) tana tare daku sai munhad’u a sabon littafina bayan Sallah idan me kome me Kowa ya kaimu

Love u all my Fan's ❤❤❤

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button