AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Tana fad’in haka ta maida hankalinta kan wayarta wacce suke chat itada Hafiz suna tattauna yanda za’ayi su had’u dan tun ranar da daddy yahanasu fita tasanar dashi, shikuma kullum sai yakirata yakai sau goma yanamata magiya akan dan Allah tayi dabarar dazasu had’u koda na minti biyar ne.
Sauke ajiyar Zuciya Hussaina tayi, tace “amma Hussaina idan kikayima jabeer haka kinci amana, kinriga kinsan irin so da ‘kaunar dayake nunamaki, zeyi wuya kisamu namijin daze soki kamar jabeer.
“Ba wani wuya, Hussaina tafad’a saboda nadad’e dasamun wanda ya mayemin gurbinsa, cike da mamaki Hussaina ta kalleta wannan wanene wanda yayi ‘karfin halin raba Zukatan dasuka dad’e suna maradin zama abu guda,
“Murmushi Hussaina tayi tare da mi’kewa tsaye tayi taku biyu zuwa ukku sannan tajuyo ta kalli Hassana wacce kebinta da ido tana jiran jin amsarta “Ba wani bane kinsanshi, Hafiz Wanda muka had’u dashi gurin dinner itama Hassana mi’kewa tayi ta isa inda Hussaina take cike da mamaki “indai Wannan Hafiz d’in kike nufi wlh inabaki shawara da kada kiyi sakin na hannu kamun na guje danni wannan Hafiz d’in da kike gani kwata-kwata be kwantamin araiba da ganinshi yafi kama da yan abi yarima asha kid’a,
Hannunta takai kan kafad’ar Hussaina ta dafata “sister iname baki shawara kada kibari jabeer ya su6uce maki dan samun namiji kamarsa a wannan zamanin sai antona……
“Ke dakata, hussaina tafad’a cikin d’aga murya, kada ki kawomin ‘kabli da ba’adi nace banison jabeer idan ke kinasonshi ki aureshi mana wani yahanaki, “Hmm aini tun farko bani yace yansoba, amma in bancin haka banga abin ‘ki gareshiba.
“Mtsswww, Hussaina taja wani dogon tsaki sannan tanufi bedroom tabar Hassana nan tsaye cike da mamakin hali irin na ‘yar’uwarta.
Hussaina kuwa tana shiga d’aki kiran Hafiz yashigo wayarta, cike da farinciki ta d’auka bayan ta sumbaci wayar dan a kullum ‘karajin son Hafiz takeyi cikin zuciyarta.
“hellow babyna,
“uhm my dear ya kake tafad’a cikin shagwa6a.
“Eh to gaskiya ba lafiya…
“subhannallah meyasameka tafad’a tare da gyara zamanta.
“kin’ki muhad’u dan baki d’auki son danikemaki a bakin komeba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke “Haba my dear dan saboda wannan zakace bakada lafiya, indai wannan ne ka kwantar da hankalinka yau idan nafito islamiyya zamu had’u.
“Wow babyna amma naji dad’i, ‘karfe nawa kuke fitowa?
‘Karfe hud’une mukoma shidda, kaga wannan lokacin ya ishemu mud’an gaisa.
“Eh to hakane amma kinsanfa nayi missing d’inki sosai.
“Hmm sai munhad’un kawai tafad’a
“Owk bye “muaaah yasakar mata wani kiss ta wayar sannan ya tsinke kiran, wani dad’i taji ya ziyarci zuciyarta rungume wayar tayi cike da Farin ciki, harta ‘kosa Hud’u na yamma tayi sufita zuwa islamiyya.
Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????
Page————————-7
Da misalin ‘karfe hud’u saura minti goma Hussaina tagama shirinta tsaf na islamiyyah cikin uniform kalar ruwan ‘kasa,
“Kallon yar’uwarta tayi wacce ke ‘ko’karin d’aura farin d’an kwali, tace Hassana kiyi sauri kinga bana bu’katar zuwa a makare, kallo kawai Hassana tabita dashi “Tofah yau kuma kece me cewa bakison makara ince kullum saina gama shiryawa sannan inyi zaman jiranki,
“Naji dan Allah yanzu dai kitaho mutafi kina ‘kara tsyar damu, ……
Dai-dai lokacin kuma wayarta tayi ringing dubawa tayi jiki na kyarma takai dubanta ga Hassana wacce tagama shirinta tsaf tana jiran sutafi.
Sunan Hafiz tagani yana yawo kan wayar, dama kuma kobata dubaba tasan shine dan tsakanin ‘karfe ukku da Rabi zuwa yanzu ‘karfe hud’u yayimata kira yakai tara,
“Hellow yanzu zamu fito daga gidan, tafad’a tana kallon Hassana ta wutsiyar ido,
“To babyna dan Allah kiyi sauri wlh na matsu na ganki dan bakisan yanda nakejibane shiyasa kikai har yanzu baki fitoba.
“Sorry dear ina hanyafa nace ka saurareni mana.
“To shikenan ina gurinda nagayamaki,
To sainazo tafad’a tare da kashe wayar.
Tana juyowa suka had’a ido da Hassana saida gabanta yayi ‘yar ‘karamar fad’uwa saboda kallon tuhumar dataga tana mata.
Nunawa tayi kamar batasan kome kenanba tace “muje ko kada mu makara naga yau baki bu’katar muyi latti,
“Owk muje to.
Haka suka jero gwanin ban sha’awa kome nasu iri d’aya ga tsananin kamanni dasuke farinsu d’aya tsawonsu d’aya haka zubin jikinsu d’aya, suna matu’kar kamanni wanda hakan kesawa mutane da dama basa gane Hassana basa gane Hussaina, hatta da iyayensu basu cika ganesuba saita gurin halinsu daya bam-bamta.
A falo suka tarar da Momy, cikin ladabi suka isa gabanta “Momy mutafi islamiyyah
“To Allah bada sa’a Yakuma tsareku, Allah yayimaku Albarka, Adawo lafiya.
Amsawa sukayi da Ameen sannan suka fice, suna fita sukasamu me napep suka gayamashi sunan islamiyyar daze kaisu,
Sun fara tafiya Hussaina ta Kalli Hassana tace “sister dan Allah kiyimin taimako d’aya sonike inje gidansu zuby kuma kinsan gida baza’abarni infitaba inaso me napep ya saukeni acan sai awuce dake islamiyya idan antaso kimin waya sai muhad’u mutafi gida.
Da Hassana kamar bazata Aminceba saikuma tace “to shikenan Amma dan Allah kada ki wuce lokacin tashinmu islamiyya, kinsan dai daddy ba sauki.
“InshaAllah kinamin waya zanzo, “to shikenan.
Hassana aka fara saukewa islamiyya sannan aka wuce da Hussaina unguwar Barhim dake wajen Gari, dai-dai inda Hafiz yagayamata yananan nan kuwa tasameshi.
Tana fitowa daga napep ta hangoshi tsaye jikin motarshi ya hard’e duka hannayenshi a ‘kirji, sanye yake cikin bakin wando, da yellow riga, sai ba’ka’ken takalmi, sannan ya d’ora wani ba’kin glass Wanda ya’kara fitowa da ainafin kyawunsa.
Yana hangota yafara jefarta da ‘kawataccen murmushinsa, itama maida mashi martani tayi harta isa gurinshi suna musayar murmushi.
“Welcome babyna yafad’a tare da rungumata a jikinshi, saurin tureshi tayi tana waige kada ace mutane suna kallonsu. {Hmm Hussaina kenan idan mutane basu ganinku ai Allah yana ganinku}
“kada kidamu babyna ba mutane sosai a unguwar, kodama wani yaganmu ba wanda ze shiga harkarmu, amma tunda naga kamar kina tsoro shigo daga ciki, “dadai yafi, tafad’a
Sannan yabud’emata motar tashiga shima yashiga.
Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????
Page————————-9
Bayan shigowar jabeer suka gaisa da Momy sannan tashige d’akinta tabasu guri, Hassana ce tacika gabanshi da kayan ciye-ciye dana sha, sannan tad’an zauna domin su gaisa, lokacin Hussqina tana zaune tabi ta had’e girar sama data ‘kasa sai danne-danne take a wayarta,
Shiru ya gifta nayan wasu mintoci, Hassanace ta katse shirun ta hanyar cewa “Yaya jabeer ina wuni,
“lafiya lao ya Amsa yana ‘karemata kallo, a zuciyarshi yana cewa wannnan itace hassanar kokuwa Hussainar ce, saida yaji tami’ke tsaye tana cewa “to nikam nashiga daga ciki sannan yagane ashe ga mutunniyar tashi nan gabanshi wacce tunda yashigo ko kallo be ishetaba, taunar cingam kawai take sannan hankalinta duka yana kan wayarta tana ibadar wato chat da Hafiz.