BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ke wai ba Ammah ne kekiran kiba kikatsaya yatsine fuska tayi kyaleta kawai bawani akyaleta tashi muje,,,,,,,,
Nasan wani abin take nema Sai kiji dadin bata amsa,,,,,,,,,,,,,
Mikewa tayi suka nufi dakin Ammah
Suna shiga suka sameta itada yaranta rabi’ah da hafsat suna zaune
Afalo Sallama sukayi basusami amsawa hakan baida mesu ba suka zauna,,,,,,,,,,,,
Juyowa tayi ta kallesu gidan ubanki ne nan dazaki isoh tun safe bakizo kin gaishe niba,,,,,,
Maciya amana ko yanzu kuma dawani cin amana uwartaki ta aikoki,,,,,,

Ko uwarki bata isa tazonan gidan,,,,, tanuna batasan inanan ba,,,,,
Balle ke karamar marar kunya,,,,,,,
Iya bacin rai ransu yakai kololuwa wajan baci,,,,,
Hameedah ce cikin bacin rai tabude baki zatai magana s damke hannun ta hanna tayi da karfi kallon ta tayi ta girgiza Mata kayi kawar da kanta tayi cikin takaici na hanata ramawa da hanna tayi

Juyawa tayi ta fuskanci Amma kingama akwai Abu me mahimmanci da mukeyi tafada hadeda wani murmushi wanda Ammah takasa tantance namiye shi,,,,,,,,
Sake baki tayi Dan uwarki aibake nakira ba,,,,,
Rashin kunyan ki haryakai ki Har yakai agaban idanuwamu kiyiwa mahaifiyar mu raini,,,
Hafsat ce tatashi da niyyar dukanta,,,
Ammah tahanata kull karki tabata kibarni da uwarta zanyi ni,
Jan hannun hameedah tayi wadda ga baki daya ji take kaman ta fashe tsabar bakin ciki,,,,,,,,,
Janta tayi Har sunzo bakin kofa Ammah tace shegiya mai bakin jini,,,,,,
Saurin tura hameedah waje tayi tadawo cikin dakin wani kallon kaskanci tabi hafsa dashi,,
Wato kece Har zaki dakeni ko tabani wallahi saina miki shegen duka,,,
Sannan tajuya gun Ammah da gabaki daya al’ajabi yahanata cewa komai,,,,,,
Idan Har zaki iya duban idona kice mun mai bakin jini kamata yayi ki fara aurar da nagabanki wanda duk cikinsu bbu wacce bata bani sama da shekara ba tukunna kisamo bakin gori,,,,,,,,,

Tana fadin Haka tajuya tafice tabarsu cikin jimami
Samin hameedah tayi tsaye tana jiranta a bakin kofa,,, dayake taso biyota Amma takulle kofan,,

Murmushi tabita dashi saurin kawar da kanta tayi tafice fuuuuuuu
Binta hanna tayi abaya Har suka shiga dakin mama ganinsu Ahaka yasa anty takirasu tana tambayarsu,,,,,,,

Hanna taso boye Mata amma hameedah takwashe komai yafada mata ran anty yabaci Amma Sai ta danne kawai Dan yanada kyau tun yanzu afara koya musu yin hakuri kafin auransu

Ahaka yaya jalal yashigo yasamesu,
Kallon hanna yayi wai Ina kuka shiga ne kam tun safe,,,, gidan anty fa mukaje,,, shine ba gayyata yafada tareda zama kan kujera,,,,, yaya daga makaranta fa muka wuce,,,,, Haka suka zauna sukayi ta tadi Dan Har sunmanta da bakin cikin da Ammah ta durka musu

Sallar magrib ne ta tashe su sukayi sallar suka dawo akasake sabon hira,,,,,,,,,,,,,,
Saikusan 9:00 najeeb yakirata suka sha soyayyarsu sanda tafara jin bacci kafin sukayi Sallama takwanta Dan hameedah ta dade da bacci,,,,,,,,,,,,,
Irin mafarkin jiya data karayi ne yatashe ta,,,,
Tarasa me wannan mutumi yake nema da take kallonsa gurfane agabanta,,,,,,,,

Datarasa mafita kawae ta dauro alwala tagiba dayin nafila Har bacci yadauketa,,,,,,,,,,
Har ta makara a sallar asubahi Sai wajen 6:30 ta tashi tayi sallah
Tunda ta farka ta tsinci kanta cikin wata irin matsanan ciyar faduwar gaba
Gabaki daya Tanaji kamar akwai wani abunda ke damunta amma tayi duk iya tunanin ta tarasa dalilin damuwar tata

================

Taro yayi iya Taro Dan duk wani manyan duniyar nan sun halacci wannan Taro
Amfara gudanar da taro komai na tafiya daidai Ina tawajan MG haryanzu faduwar gabansa tsananta takeyi

Duk wani tsaro daya kamata awajan antanadar
Inda layin da MG yake zaune layin manyan mutane ne wayar sace tadauki ruri ganin yanda wajan yake a cike yasa yatashi dan amsa wayar, mahaifinsa ne yake kira yasa bazai iya kindauka ba

Kokarin fita daga wajan dayake yake niyyar yi soldiers suka taso Dan bin bayansa daga musu hannu yayi alamun su koma,,,
Bamusu suka tsaya inda captain Ahmed yabi bayansa,,,,,,,

To be continued

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r)

Edited by KSA precious Hajjah ce

Dedicated to
Ummi Aysha (haske Writter) novel d’in ki na mijina sirrina yayi sosai Allah ya kara basira da zakin hannu

Page 17

*
Fita yayi cikin sauri dan amsa wayar da mahaifin sa ke kira.
Ga baki d’ayan sojojin suka bi bayan sa cikin sauri. d’aga musu hannu yayi alamun su koma. Bbu musu suka jah suka tsaya a inda suke.
Captain Ahmed ne ya bi bayan sa
Dan ya san hatsari ne barin shi yafi ta shi daya.

Amsa wayar ya yi sannan suka gai sa. tambayar sa ya keyi da cewa.
Yareemah…!!! Kana lafiya?” cikin murya mai cike da da muwa yace “lapya na klau abba, wani abin ne ya faru?”
A’a bbu babu komai ka kula da kan ka kaji ko?
Kuma na kira mahaifiyar ka tace mun bata san lokacin fitar kaba.
Ya kama ta Karin ga sanar da ita, ai addu’ar mahaifiyar ma yana da Amfani kaji ni?”

Yareemah yace “In sha Allah.”

“To Allah ya kare ka daga sharrin ko wani irin halitta.”
Ameen yace sannan ya kashe kiran.

Juya wa yayi zai tafi Sai ya ga daniel tsaye yana murmushi tare da sosa kyeya kaman Wanda yake neman wani alfarma.
Kallon sa yayi sannan ya kawar da Kai yana kokarin mai da wayar sa cikin aljihu.

"Sir MG please ina son magana da kai."

Kallon sa yayi tare da cewa “Ehem! ina jin ka.”

Yace “Sir Idan ba zaka damu ba mudan matsa tacan? ya nuna wani waje da bbu mutane ta cikin hotel d’in.

Kallon sa yayi batare da wani tunani a ransa ba ya nufi wajan.
Sanda suka isah MG ya d’an jin gina ya lumshe idanuwan sa ba tare da ya kalle shi ba yace “Kai nake sauraro.”

Duk wani abin da yake faruwa akan idon captain Ahmed ne.
Amma da yake Shima ba abin da ya kawo a ransa yasa ya tsaya nesa dasu sosai.
Ganin daniel na shirin ciro Abu daga cikin aljihun sa ne kuma ya nada tabbacin bindiga ne ya sashi fara shan jinin jikin sa.
Ga shi Kuma idon MG a rufe yake. Da sauri ya fara kara sawa wajan da suke a tsaye.

Amma dake da rata a tsaka nin su kafin yayi rabi harya karasa fitowa da bindigan. magana ya farayi cikin garaji Wanda hakan ne yayi sanadin bud’e idon MG amma kafin ya bud’e ido Sai sau kan harbi kawai yaji a gefen cikin sa.

Karar har binne ya jawo hankalin jami’an tsaron da ke wajan.
Bud’e idanuwan sa tarr yayi ya zuba su akan na daniel. Wanda ke wani irin dariyar mugun ta. A lokacin Idan kaga MG baza ayi tsammanin a kwai harbi a jikin sa ba. Sai dai Idan ka lura da yadda jinin kebin jikn sa.
Wani irin huci yake fita da shi Wanda duk d’auri yar mutum a wannan lokaci Idan ya gan shi sai ya razana. Dan idanuwan sa sun sauya kala sunyi jawur.

Wani irin shaqa ya kai wa daniel. Kan wani Dan lokaci idanun daniel ya fara zazza rowa. ganin yana shirin hallaka shine ya sa ya kara d’aga bindigan ya sake masa a gefen kirjin sa.
Ganin Haka yasa captain Ahmed cira bindigan sa Kan ya ‘iso ya sakewa daniel ita a goshi.

A lokacin jami’an tsaro suka isoh wajan a kayi saurin rirreke MG da jikin sa gaba ki d’aya ya 6aci da jini. captain Ahmed ne ya kara so ya tallafe shi.

Ga baki d’aya gun ya cika da sojoji. kai kace wani taron sojoji akayi. ga baki d’aya hankulan su a tashe yake Ganin shugaban su cikin wannan ya nayin.

Motar tai makon gaggawa ne tazo in da yan jaridu sun cika wajan makil. kowa koka rin d’aukan abun da ke faruwa ya keyi.
Nan da nan a kayi dashi babban asibiti dake cikin dubai. inda moto cin sojojin dake gaban su da Wanda ke bayan su sun Kai akalla mota sha biyu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button