BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Gyara zama minister yayi ya fuskancii iyalansa sannan yace,”
Kugafarcenii tabbas nasan abun da zan fad’a bazai muku dad’ii ba, amma kuma yakamata infad’a muku. “
Shekara d’aya da watanni d suka shud’e,”
Ina office, “
Sectery yakirani kam cewa inada visitor’s ban d’auki lokacii ba kasancewa yasanar danii way’anda keson ganina band’auki lokacii ba nace su shigo duk da cewa abun yabani mamaki.”
Senator ne shida shugaban y’an kasuwa sukazo nemana, “
Cikin mutumcii da karramawa muka gaisa tareda y’an barkwancii da baza’a rasaba,”
Nan suka zauna Senator ke sanar danii munada muhimminyar maganane, “
Tom alokacin ban fahimcii komai ba,”
Kawai dai nad’auka kan wani siyasa ne. “
Munyanke shawara akan zqmu had’u da su a guest house na Senator.”
Anan muka had’u alokacin naga ashe munada yawa wanda za’ayi meeting d’in. “
Ganinsu ahaka ya tabbatar mun cewa ba abin alkhairy bane,”
Koda nazauna suka fad’amun buktar su, da farko nak’ii amincewa,”
Kan cewa zan aikata abunda suka bik’ata, “
Amma Daga baya idanuwana suka rufe kiriff da ganin kud’ii na aikata sa6on Allah.”
Tun kafin yafad’ii lqifinda ya aikata, karima tafara hawaye dan ta tabbata ba abuu ma dad’inn jii bane mahaifinta ya aikata. “
Hajiya suwaiba da duk itama zuciyarta ta karye tace,”
Abban mufeedat wani irin abubuwane haka ka aikata? “
Nisawa yayi yace munshigo da gur6ataccen maganii wanda ak’allah mutane samada d’arii biyu suka mutu ta dalilin shan wannan maganii.”
Dagowa yayi ya kalli iyalansa wanda duk hankalinsu atashe yake dan kukama sukeyi yace.” Wallhy da hannuna danni da kaina nasa hannu atakardar muka shigo da maganganuwan. “
Idan baku manta ba shekara d’aya data wuce anyi ta mutuwa wanda aka alaqanta hakan da annoba,”
Mutane darii biyu sun rasa rqyukansu, samada darii biyu sun nakashe. “
Kuka Hajiya suwaiba takeyi tana dukan k’irjinsa tana cewa Abban mufeedat meyasa?”
Meyasa bakayi tunanin bayin Allah ba awannan lokacii?”
Adah nad’auka cewa mujina adalin shugabane ashe bansan cewa ina zaune da wanda baya tausayin talakawansa bane. “
Rungumeta yayi yana rarrshinta Kuka kawai takeyi banda karima da itama har shid’ewa takeyi dan Kuka.”
Share hawaye yayi yace suwaiba san zuciya ne yasa, “
Wata k’asace suka karyar mana da farshin maganin Kan sunyishi ba ka’iida ba,”
Amma kuma abun mamakin Anan shine sukuma y’an kasar da suka sayar mana, suma sun sayar ak’asarsu amma kuma hakan bata faruu ba. “
Maganii baya musu amfanii amma bai kashee wani kokuma naksar da wani ba.”

Alokacinne nashiga buncike, “
Abinciken da nayi ya nunamin cewa amfanii sukayi da jinin al’ummar suakcii za6e.”
Sannan Abinciken nagano cewa mu biyu aka rufe bamusanda wannan al’amarii ba. “
Ganin mutuwar tayi yawa yasa shugaban sojjoji na k’asa da k’asa wannan yaron wanda akeyin bikinsa,”
Yashiga buncike ton duk yagano cewa dasa hannu aciki kuma yasamu evidence, “
Wanda alokacii d’aya zaigamo masu hanuu,”.
Hakan yazao kunnemu ne daga wajen shugaban sojjoji na k’asar Nan.”
Dan duk wani abunda zqmu yin da hannunsa aciki. “
Sannan kuma yashaida mana cewa yagano da hannun shugaban kasuwa da custome aciki,”
Kuma yatabbata zai iya gano wa cewa da hannunmu aciki. “
Bamusan maiya faruba yayi tafiya na y’an month,”
Acan dubai muka shurya kasheshi Allah baiyiba. “
And yaban yadawo na wasu month muke tunanin sake Kai masa harii.”
Amma nafuto na fad’a musu cewa bazan iyaba, “
Dan yanzu nikaina nafii buk’atar hukuncii fiyeda komai.”
Nafii buk’atar ayiwa way’anda na zalumta sakayya, “
Ina tsoron gamuwata da Allah.” tashi yayi yabud’e wasu jakka Sannan yad’auko duk takardunda yake ciki ya miqa musu, “
Da kunnena najii suna cewa wai zasu kasheni gwamma sikasheni Tun yansu,”
Su d’auke duk wani zunubinda nake dashi akansu. “
Fargabata d’aya kada suce zasu ta6amun iyalina kuma nasan zasuyi k’akarin aikata hakan,”
Ki dauki y’ay’ankii kuje kada ku zauna.”
Inada wani gida acan gandun albasa, bansaya da sunana ba ku je can bbu mai sanin cewa kuna raye, “
Kungq mufeedat bata k’asa idanna ce,” Kuje wajanta za’agane cewa kunfita daga k’asar dan kunsan ba kananun mutane bane. “
Nabiyu gashi duk wata dukiyar dana mallaka tana cikin nan da takarduna da information na bankuna,”
Kada wani acikinku yasake amfanii da atm d’insa ga tsaban kudii acikin wancan jakar kuyita amfanii dashi, harsai randa kukajii cewa ankamasu Sannan kufito Kuyi rayuwarku Kamar kowa. “
Kuka hajiya suwaiba takeyi sosai tace wallhy abban mufeedat bazan iya tafiya nabarka ba,”
Bazan iyaba idanma mutuwane nafii buk’atar namutu kusada mijina. “
Girgiza matakai yakeyi yana a’a hajiya kitafii da yara kinga kinada k’ananun yara,”
D’gowa tayi ta kalli karima tace karima Ki riqe k’annanki da kyau dan Allah Ki musu tarbiya mai kyau, “
Idan Allah yasa kwanan mu yak’are nida mahaifinki kuyita manq addu’a.” bayadda mahaifin karima baiyiba akan hajiya sawaiba tabisu ba amma takii, “
Jakar kud’in yad’auka kirar dana ta kardiun ya nafii bayan gidansa yasa abayan wata mota vibe.”
Hajiya suwaiba kuma ta shiryawa d’iyanta kayansu a trolyn dukansu.”
Itama takai musu motan, “
Ahaka tatashi abida dake bacci wanda bazata wuce 17 ba sai dan sa’ad dan 14. Da kuma y’an biyu hassana da usaina,”
Sai autansu kabir 7yr’s, “
Karima tana Kuka Kamar ranta zaifita iyayenta suka turata amota,”
Duk sauran basusan maiyake faruwa ba, amma suma Kuka kawai sukeyii iyayen sukabii d’aya bayan d’aya suna rungumewa suna yiwa y’ay’ansu addu’ar nasara. “
Sauran yaranma duk Kuka sukeyii banda kabir dayake bacci.”
Minister ne ya leqa ta window yabata wani photo yace, ba lallai abinda nashirya yatafii dai-dai ba, “
Amma duk lokacin da Kuka shiga matsala kinemi tajikin pic d’innan inada tabbacin zata taimakeku.”
Kada Ki tada motar harsai kinga kirana yashiga wayarki. “

Ahaka suna kallo babanta yawuce yatafii ta baban gate nan y’an sandan da suke tsaronsa suka takemasa baya.”
yana futa kuwa yaga abinda yake zato mutane ne acikin mota har uku agaban gidan. “
D’aya ya dagwa yawa yakira sauran akan suzo ko za’asamu matsala ga Minister nan tanan k’ofar.”
Aikuwa duka suka tattaro zuwa nan alokacin Minister yadanna wayarsa dake aljihu yakira diyarsa, “
Tana kallon kiran mahaifinsa ta tada motar ahankali tafice tabar anguwar.”

Shikuma sanda yatabbatr tabar anguwar ya juya yakoma, “
Gabaki d’aya kansu yad’aure ganin yakoma.”
Yana shiga gida yakira senator, “
Senator na d’auka yace dama nasan zaga sauko ma.”
Dariya Minister yayi yace kakarancenii abaibai, “
Kasa tsaro ak’ofar gidana kana tinani zan gudu ko,
To Allah yafiaka, yana fad’in haka ya katse kiran.”

=============== wannan rana takasance ranar da mutane dayawa bazasu manceta ba, wasu takasance musu ranar farinciki wasu kuma takasance na bak’in ciki.”
Ranar intisar kwana tayi bata runtsa ba tsabar bak’in ciki da kishi. “
MG kuwa shima hakane takasance anasa wajan amma shi saba’anin haka,”
Tsantsar farinciki da nishad’ii yake ciki kokad’an baisamu bacci ba sai 3:30 yana nafil fili na yiwa Allah godiya, nacika masa burinsa.”
Sai 3:30 yasamu ya kwanta bacci yayi wanda rabonsa da bacci mai da d’in haka shekara goma tunda yad’aura idonsa akan hanna ko kuma ince bai taba bacci mai nishad’in haka ba. “
Sanda yamakara asallah, sai 6:00am kafinnan yafarka yayi sallah duk da haka bawqi baccin ya isheshi bane yana idarda sallah ya kwanta bacci.”
Dan jinsa yakeyi fayau Kamar wanda aka d’auke masa nauyii. “
Itakuwa hanna anata wajen bazaka iya bambamce farinciki take cikiba ko saba’anin haka, amma dai tana cikin kewar mahaifanta na gaske,”
Dakyar bacci yad’auketa.”
Wajan minister kuwa da hajiya sadiya kwana sukayi nafil fili, sunata zuba ido suga abinda zai biyo baya amma shiru har garii ya waye bbu wanda ya runtsa.”
Sai karima da sun isa gidan tasa, yan kannenta dasuke bacci agaba kuka kawai takeyi, “
Ahaka takwana bata ko runtsa ba,”
Ahaka abida ma ta kwana tana kallon yayarta, batasan mai yakeyi damunta ba, “
Tatambayeta iya tambaya amma bbu amsa haka tazauna tazuba mata ido.”
Kawai suka kwana bbu bacci. “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button