BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Page 28

*

Futa tayii ahankali kamar wata marar gaskiya.”

Hange ” hange” tafara can ” sai ta hango motarsu awajen can dan nesa Da gidan.”

Nufarsu tayi Da gwarin guiwa, amma duk da haka gabanta yanata faduwa dar-dar. 

Tana isah” bakin motar ta bubbuga glass din, ahankali suka zuge, kara hade rai tayi sannan tadauko ledar Da mika musu, ba musu dayan ya karba wanda yawanci shi yakeyin driving din car din. “

Kara turnuke fuska tayi, sannan tace kudaina zama Da yunwa, ta dalilina gwanna idan zaku ringa futa kuna neman abinci ku futa.”

Tana fadin haka tajuya. “

Binta sukayi Da kallon mamaki,

Juyawa yayi ya kalli dayan sannan yace, captain bala yarinyar nan nada abin mamaki.”

Yadda kasan oga data murtuke fuskar ta shima haka yake, an hadu an dace sukace hadeda kyalkyalewa da dariya, bude ledan sukayi, gaskiya yarinyar nada kirki, wato hartaji tausayinmu. “

Dama yunwa sukeji, take suka fara cin abinci." 

Karfe biyu suka fito dan wucewa kano, sosai sukayi kewar maman nana mace mai kirki. “

Sun dau hanya, sun kai wudil najeeb yakirata, tayi mamaki nasanin cewa yasan dasudau hanya amma ko saudaya bai kirata ba.”

 Sauke ajiyan zuciya, tayi sannan tayi picking call din,  hira sukayi sosai, har ta manta Da yaya jalal a motar. "

Haka kawai yaya jalal ya tsinci kansa Da bakin cikin wayar da takeyi, shi yasan ya dade yanason *hanna*  amma kuma yarasa dalilin dayasa har yanzu yakasa furtawa." 

Saida suka shiga garin kano sannan sukayi sallama da najeeb, alokacin ran yaya jalal yakai kololuwa wajen baci, yayi kucin kicin ya hade rai,

================

Wannan mutuminne wanda haryanzu bawai nasan waye bane, yadaga waya yana kira da alamun wani yake nema.”

Can aka dauki wayar, cikin firgici yafara magana, chief sanda nace ma a airport mutada bomb yamutu ahuta kukaki, gashi abinda nakeji yafara, faruwa. “

Yanzu Haka dan gidan minister yananan a asibiti yafara daukar fansa.”

D’azu yakirani yake shaidamin, cikin wayanne naji ankatseshi, ya’akayi har yasan mune muka aikata??” shima ya fada cikin tsoro, Yanzu abinyi shine, duk kai musu waya muhadu musan abinyi, tun kafin kwabar mu tayi ruwa, nan Da zuwa week duk muhadu a abuja. “

Cikin kid’ima ya amsa Da yes kawai, yana gama wayar ya cire hula duk ac dake falon amma gumi na tsatsafo masa.”

Haka kira yayita shigowa wayarsa kowa cikin tashin hankali yake tambaya danjin, cikekken labari. "

Ahaka dai suka tsaida magana akan zuwa next week zasu samu yin meeting dan samun solution.”

Akarshe ne yakira wani awaya, bayan ya dauka ne yafara ce masa, “

Inason ka samomin tak'aitaccen _history_ MG Abudullahi abdulaziz lamido ne." 

Duk wani wanda yasha feshi, Inason sani koda jaririyar da aka haifa a family din akawo min sunanta Da kuma pic din su, zuwa nan da 3days banji mai akace ba yasauke wayar akunnensa. “

 ===============

Sai yamma likis suka shiga garin kano, kowannensu agajiye yake, gashi kokadan yaya jalal baya gudu amota.”

Kuma k’arin abinma, bacin ran dayake ciki yasashi k’ara saibi. “

Suna isa cikin gidan ko gaisawa da umma basuyi ba suka wuce part din ‘yan mata yanda dakin anty samha da hameeda yake.”

Suna shiga agajiye suka zube kan gado, sis wai meya batawa ya jalal raine a mota?? "

Ki kalla fa ko magana yakiyi.”

Damuka iso ma ko kallon mu baiyiba yafice yabar motan. “
Ohonsa nikam, tana fadin Haka tashige ta dauro alwala, bayan tafito hanna ma tashiga tayi wanka, bata damu Da yamma Da tayiba, ta d’ane gado sai baccin gajiya, dama rabonta da irin Wannan tafiyar tun tana yarinya.”

Bayan hameeda ta idarda sallah ne itama tabita gadon, nan danan bacci mai nauyi yayi awon gaba dasu. "

To be continued

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim

_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )

this Page is humbly dedicated To u maman manal yhur such a nice an wonderful person luv u so much nima inasonki kamar yadda kike sona muna mugun tare????

Page 29

  • Basu suka tashi daga bacci ba, sai kusan bayan magrib. ” Umma batsan da dawowarsu ba dan tajira har tagaji kuma takira waynsu hanna ba’a picking yaya jalal dama ransa abace yake shiyasa yana isa yakashe wayansa, saleem kuma bayansa yabi suka shige daki.” Kusan eight 8:00 wata irin yunwa tatashi hanna. ” gani tayi hameeda tawani baje sai baccin take sharar bacci.” Dak’ar k’arewa tayi ta sake mata marii, a back dinta sanda ta tashi zaune bbu shiri. ” Ke da’allah yunwa nakeji.” shine dan rashin mutunci sai ki dake ni banza kawai, tafada hadeda komawa baccin ta. ” Please sis wake up am terribly hungry , bakisan kofa ba kenan, tafada atakaice.” But i said am srry hanna tace had’eda langa6ar Da kanta, banza marar mutunci tafad’a had’eda mikewa tayi hanyan futa, ai hanna dataga ba sarki sai Allah kuma tafiya zatayi ta barta. ” a arba’in taduro akan gadon tabi bayanta.” Afalo suka sami Umma tayi tagumi, ai Da gudu hanna tawuce hameeda tafad’a jikinta. ” A razane Umma ta juya jin mutun ajikinta, ai tana ganin hanna cikin murna ta kankameta ajikinta, sai can ta sake ta.” Ba kunya hanna ta gyara zamanta dere-dere akan cinyan Umma, kod’od’uwa Da ita sai wani zuba mata shagwaba take zubawa kamar ‘yar goye. ” Tsakin da hameeda taja ne yasa hankalinsu yakai kanta datake tsaye.” Ware mata hannu ummah tayi, sannan tasaki murmushi ta shige jikin Umma. “
    Umma Haka Allah yayita dasan yaranta da kuma jansu ajiki.” Ture ture suka fara kamar wasu yan biyu,, dariya kawai Umma keyi musu, dan yanda takejin hameeda Haka takejin hanna kokadan bata tabajin banbanci akansu ba, hasalima dukansu da ita suke kama. ” Yaran ummah biyar ne Allah ya azirtasu dasu, babban danta ya auwal shike auran anty hindatu yar mama, sai me bi masa yaya jalal, daga nan sai anty samha wanda za’ayi aure tagana degree dinta a buk.” sai salman wanda hameeda ke bi masa, yagama degree dinshi agana yana service, kunsan yanayin karatun mu bad’aya dana muba dan anty samha tarigashi shiga da shekara daya amma tare suka gama, sai hameeda itace auta.” Hanna ce tarik’e cikinta cikin muryar shagwaba tace Umma yunwa, tashi tayi taja hannun su zuwa dining, sanda sukaci suka koshi sannan suka fara tamvayar wajen anty samha. ” shaida musu tayi tana d’akinta aguje sukatashi sukayi dakinta, tana waya da mijin da zata aura saiji tayi kawai anzube akanta had’eda saka ihu.” Itama cikin razana ta saki nata ihun wanda sanda yasa abubakar dake zaune a kusa da MG yana waya saurin kawarda wayar a kunnensa, afili kuma ya furta su hameeda an isoh kenan. ” Gaban MG ne yafadi, yanason masa tambaya amma bayaso ad’ago shi, kawai saiya share.” Amma ransa fall yake da farinciki, ya tabbata hannan sa ta isoh lafiya. ” Juyowa tayi aikuwa tana kallonsu wani sabon ihun ta dad’a sakewa sanna ta rungumesu, Umma tana daga falo amma tanajin ihunsu.” Yan iska yaushe kuka isoh?? ” Tun da yamma” shine kuka shige daki? ” kunsan tun yaushe nake jira kuzo kufutar da ashoben kanne yan iska kukaki zuwa.” Hanna Da hameeda ne suka kalli juna harsuna hada baki wajen cewa k’anne?? ” Hanna ce ta tabe baki yanzu ke anty samha ku kunya bakijiba wajan cewa wai mu muyi ankon k’anne, hameeda ce ta amshe zancen haba anty yanzu dame kika fimu?” har mun daraki atsayi fa gaskiya aduba wannan zancen.” Daura kafa daya kan daya sukayi sai wani jujjuyata sukeyi, irinna mararsa mutuncinnan. ” Ita kuma anty samha tunda suka fara magana tasake baki kawai tana kallonsu, Ita kanta tasan gaskiya ne inba fuska aka duba ba ba’ace ta girmesu ba.” Idan ta jiki ne ma sai ace sun girmeta. “
    Cikin rasa abin cewa tace ku6ude, wadrope dina zaku kalli kalli kala biyar biyu na k’anne, uku na kawaye, green da yellow dinne na kannen saiku ebi na kawayan.” Hanna ce tatashi ta bude sif din, na kawaye tafara cirowa sanda taciro set uku, sannan tajuyo, taga yanda anty tazuba mata idoh, meye????‍♀?? ” Hanna hameeda amira tafad’a atakaice.” Hameeda ne tataso, Itama, ” na kannen ta eba set biyu.”
    Kwasan kayan sukayi dasu fice, anty tatsaresu, me kuma dakuyi dana k’annen, owh anty dan munce baza musa abiki ba doesn’t mean ba maso, ” A’a kawai abikinne baza musaba.” suna fadin haka suka fice suka barta totally speechless Abubakar kuwa dariya yakeyi kamar dan itah aka aikoshi yi duniya.” tun lokacin bawai yakashe wayan bane, saima samusu Ita da yayi a handsfree koh MG dako murmushi bawai yacika yi bane amma yau sanda yayi har hak’waransa yafito. ” Jin muryar ta da yayi yasashi awani irin nishadi, soyayyarta ne ke ratsa duk wani gabbai najikinsa,” wanda har wani kasala yasaukar masa dashi, ” sai wani shimfid’aden murmushi wanda ke kwance a fuskarsa dayasa, kuma tunshi suka zauna a lobe wato dimfull, wanda wasu ke kira da beauty point.” Damashi ko motsa bakin sa yayi, toh side da side na cheeks dinsa sai sun lotsa, ” Su Hanna nashiga daki duk suka zube kayan ak’asa, Hanna ce tacire doguwar rigar dake jikinta, da niyyar shiga wanka, yarage daga itah sai bra da short din wando wanda yawuce guiwa amma baikarasa kasaba.” Hameeda ce tashigo, daga falo taje dauko ruwan sanyi,, saurin daukan rigarata tayi da niyyar kare jiknta. ” Wata muguwar harara da hameeda ta watsa mata da’allah banza, with dis yhur platty tommy mai mutum zai kalla?” eh din najidai futa da’allah. ” K’arasa shigowa tayi saikiyi kuma.” Tsaki taja ta shige toilet. “

================

Tashi yayi ya shige shaashinsa.” idanda sabo abubakar yasaba, shi bayayun sallama saidai kawai kanemeshi karasa. “girgiza kai abubakar yayi sannan shima yatashi yatafi.”

Yana shiga dakinsa wani godon alfarmane aciki, wanda daka kalla ansan gadone wanda jinin sarauta ne kawai masu irinsa wanda ake kira da royal bed . “

Farin bed shit ne kall a kan gadon a shifideh, kamar yanda paint nadakin yake fari,
Dakin yakai akarsa gado uku aciki kawai dan girma da kyau.”

Dakin a gyare yake tsaf-tsaf bazakace akwai mai rayuwa adakin ba tsabar yanda dakin yake so cleanness. ” wani sanyi mai dadda dan kamshi ne ketashi wanda yahadu da kamshin room freshner dana turarukan dayake amfanida su yabada kamshin sanyi.”

Wata kofar glass yanufa ammata design mai dan karan kyau, wasu numbers yadanna kofar tabude. “

Ashe wani dakinne aciki, shima komai nadakin farii fat pics din Hanna ne akowani lungu da sako nadakin.” tun tana karama har lokacin da tadan tasa har izuwa girmanta nayanzu. “

Kurawa pics din idanuwa, sannan yakarasa ya6ude wata drawer yadauko wani diary mai kyau harda bironsa a manne Ajiki.”

Wasu yan rubuce rubuce sannan yamayar ya aji’yeh, ya tashi zai tafi yabige drawern wani file ne yafado, takardun ciki suka watse, kurawa takardun idoh yayi.”

To be continued

Ur’s
z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim

_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )

Page 30

*

Tsugunnawa yayi hankali ya tarataro takardun yana me kare musu kallo. “
Afili, ya furta subhanallah wat boders me Haka dahar namanta da takardunnan.”

Neman bakin gado yayi ya zauna, tabbas na gabatar da takardunnan."

Kiran captain Ahmad yayi,” inason ganinka yanzu, ya ajiye wayan ba’a dad’e ba kuma sai yajin ring alaman anshigo falonsa. “

 Tashi yayi ya nufi hanyar fita hadeda takardun a hannunsa, yana Futa kofan takoma tarufe, bakace dakine awajen ba saidai kayi zaton _locker_ ne haka

Sanda yafuta adayan dakin, sannan yanufi falo.”

A tsaye ya samu captain Ahmad, yana kallonsa yayi saurin k’amewa, wata harara MG yabishi da itah. “

Da’allah malam sauke mun hannunka, cikin gidana muke ba barrack ba.” sauke hannunsa yayi hadeda dan sosa kansa. “

Zama yayi ya nuna masa waje shima ya zauna."  

Mik’a masa takardun yayi sannan yace” shad’af na manta dasu, karba yayi ya bude, cigaba yayi da cewa ” yaushe kaga yakamata mugabatar da su??”
Dan idan mata ki ne ma yskamata adauka tun da dad’ewa. “

Kallonsa yayi sannan yafara magana acikin lafazin da zaifahimceshi.”

Yalla bai da mu d'an dakatar da wannan zancen tukunna kallonsa yayi da alamun tambaya? " dalili?" yafada atakaice. "

Dan zakudowa yayi akan kujeran, alamun yanaso zancensa yashiga.”

Yallabai kaga nan bada dade waba kaza kama ango, harara MG yasakemasa wanda bbu shiri yashiga taitayinsa. “

Shiru yayi nadan wani lokaci.” cikin hasala MG yace kaifa nake sauraro”

Yallabai be kamata ace angabatar da wannan shaidu, batareda, kayi aureba tukunna. “

Kasan lokaci k’alilan yarage faruwar hakan.”

Wayanna mutane ba k’ananan criminals bane dasu iya hurting dinta. “

Dasuyi iya investigation dan su ganota.” maiyasa kace Haka?? ” meyasa ni bazasu yi hurting dinaba sai itah??”

Wani dan murmushi captain Ahmad yayi, naganin shawararsa tafara shiga.”

Yallabai i know yanzuma may be they have tried several tyms to hurt u but Allah baibasu ikoh ba. “

Dannasan bbu yanda za’ayi susan wyannan evidence na hannunka wanda zai iya destroying life dinsu kuma su zauna shiru,” u knw dat it can’t be. “

Atunanin yanzu haka suna neman abinda kafiso wanda zasuyi treating dinka akansa.”

Bincike bbu yanda bazai iya ba, karkasha mamakin su nemota kuma su sameta. “

Alokacin bbu wani sucurity da zasu iya kareta, amma idan tana karkashin she will be more safe than ace tana gidansu” .

Yallabai idan tana karkashinka akwai * sucurities masu bada duk family dinnan kariya, kuma hankalinka zai fi kwanciya da fargabar mai zasu iya aikatawa. “

Ni yanzu aganina is good n better anyi abu cikin gaggawa, ayanzu may be they planning or up To something terrible wanda faruwar sa bazaiyi da’di ba.”

Captain bala da kalan kakin tawagar mu suke amfani baka ganin, wasu zasu iya binkice mai suke bi?? "

Shiru MG yayi yana tunani dan duk maganar captain Ahmad gaskiya ne.”

Atake hankalinsa yatsahi gani yake kaman yanzuma nemanta sukeyi, atake idanunwasa suka kada sukayi red. “

Sosai captain Ahmad yashiga rudani, yafara cewa sir am srry i dnt meant To hurt u.”
No u didn’t yafashi amsa atakaice.”

Nagode da shawarka kiramun sajen ma’arof, tashi yayi cikin 2 minute sai gashi sundawo tare. “

Idanuwansa a lumshe dan yasan da shigowarsu.”
Kaje kasamu wani Acikin soldier’s d’ina, kutafi wajen captain bala, kace masa nina ce kuyi aiki tare, captain Ahmad zaimuku bayani, sannan kullum yaksance da gun ajiknku, yana fadin haka ya tashi yashige daki. “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button