BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru mai martaba yayi duk jikinsa, yayi sanyii, yadubi Marshall yace tashi kaje, zankira Ahmad d’in zanji tabakinsa zansame ka.”

Tashi yayi yamiqe yafice murna aransa fall, yayi nasara danya fahimci jikin abba yayi sanyii.”

Abba ne yashigo afalo yasamu umma, badai yadda take walwala ada ba, zama yayi kusada ita yace khadija, juyowa tayi takalleshi, yace inaso muyi magana, amma kuma yakamata ki fahimceni, yakamata ki fahimci mezan fad’a miki, dan kada kiyi mana gurguwar fahimta, kisani komai mukaddarine daga Allah, nan yafara zayyano mata bayani, kallonsa kawai umma takeyi, ji takeyi, kamar tashaqe shi kokuma tarufeshi da duka, juyarda kai tayi gefe, har yagama bayanansa ya wuce, tabishi da kallon banza kawai dan wani haushi yabata.”

Tashi tayi tanufii d’akin hameeda, tana zuwa taganta kwance akan gado, duka ta d’aka mata, wanda yasa hameeda zabura tatashi, tana shirin kurma ihu.”
Umma tace da Allah rufamin baki, nasan abbanku zuwa jmawa zaizo miki da maganar wai zasu aura miki mijin er uwarki, idan kika kuskura kika amince nidake, zaro ido hameeda tayi, sannan tace umma er uwata kuma wacce?” mijin hanna zasu aure miki, wallhy idan kika amince saina kasheki, kuka hameeda tafashe dashi, tace haba umma yaya za’ayi na’amince, kamar uwa d’aya uba d’aya fa muke, kima amince dan wallhy zan iya kasheki, kokuma in tsine miki, kuka takeyi tana cewa wallhy bazan amince ba umma.”
Rufo mata k’ofar tayi da karfii, itakuma takoma takwanta tacigaba da kuka.” jitakeyi kamar amafarki wai mijin hanna,

K’arfe takwas dai-dai mai gadi yashigo afalo yasamu umma yagaidata, sannan yace, hajiya wani yana sallama da hajiya hameeda, ak’ofar gida, umma ne tace jeka kace tana zuwa, leqa d’akin hameeda tayi taganta tanata kuka kamar ranta zai fice, bak’in cikinta d’aya wai arasa wanda za’ace ta aura sai mijin er uwarta.”

Kitashi kije ana sallama dake awaje, mamakine yakama hameeda ganin, Ko ance ana sallama da ita umma sai tace ace batanan.”
Yau itada kanta take cemata tajeta ana kiran ta, harta juya zata fita sai tace, yauwa sannan ki gyara fuskarki, ki tareshi da tad’i, har babanku yazo yasameki.”
D’aga kanta kawai hameeda tayi, sannan tatashi tashafa powder, da turare tasaka hijabinta tafito fargabanta d’aya Ko waye yazo wajanta, itadai data aurii mijin hanna gwamma koma waye ta aura, afalo tahad’u ta umma, har tawuceta tajii umma nacewa, kuma kada kiga nace kifita kije kiyi rawar kai, ki kulada mtumcinki, kisan cewa Allah yana ganin ki, d’aga kanta kawai tayi tafice.”

Ajikin mota tasameshi yana jingineda mota, tun kafin tak’arasa tagane wanene.”
Tana isa tagaida shi, ya amsa, bai boye mata komai ba yafad’a mata yanda sukayi da Marshall, Jijjiga kai tayi tace wallhy hakan yafii, bansan wani irin abuu sukeson aikatawa ba.”
Kallon fuskarta yayi yace, kin amince dani kenan, kai kawai tad’aga masa, nan ya bata labarin sa, har tad’an saki jiki dashi suna hira.”
Motan abbane tadanno kai, tun daga nesa yahangeta tana hira, bai kulata ba yayi saurin parking Motan ya fito ya shigewa gida.”
Anan falon yasamu ummii, zama yayi cikin sanyin jiki yace wai baki fad’awa hameeda wannan maganar bane naganta atsaye tana hira, umma ne tace, banfad’a mata ba, tunda naga tanada wanda takeso, kulllum yana zuwa hira nayau d’aya ace anmata miji, dawuya ace na fad’a mata wannan zance lokaci d’aya sai dai idan kai zaka fad’a mata idanta shigo.”

Ganin lokaci yaja g Ahmad yace, barin tafii time yanaja sai gobe zanzo, kai tad’aga masa, sannan yace kuma kada kisake yin kuka anshawo kan matsalar dan fuskarki tanuna kinyi kuka, bazan sake ba tace sukayi exchange na number, sannan sukayi sallama.”

Afalo tasamu abba gabanta yayi mugun fad’uwa naganin sa, amma tadake tace sannu da dawowa abba, yawwa sannu yace, tana k’okarin wucewa, yace dawo nan zamuyi magana dake, dawowa tayi tazauna yadubeta yace, waye wannan wanda naganshi tareda ke yanzu, sunna kai tayi kamar maijin kunya tace, abba k’anin mijin hanna ne, shima sojane yanzu yakai matakin general, gaban abbane yafad’i, ya k’ara maimaita k’anin mijinta kuma, tace eh, yace Yau yafara zuwa kenan, girgiza kai tayi tace, A’a abba tun bikin hanna muka had’u baku ta6a had’uwa bane.”
Yadad’e ma yana cewa zai turo banbashi dama bane.”
Abba bai iya cewa komai ba yace tashi kitafii, tashi tayi tamiqe, dad’ii yacikata ganin yanda jikin abba yayi sanyii.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button