BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yaukam abar hanna tasha ruwa danta amince da auren MG z33yyb3rw3r ma tasha ruwa

Saura kuma naji nace Page yayi kad’an sai nayi suburbud’a????

To be continued

Ur’s
Z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim

_
Writting by

© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )

Page 46

*
Ihuu badaga mutanen wajanba har wanda suke kallo a insta, sanda sukasa Ihuu.”
Hakanne yayi sanadiyar daskarewar najeeb dake zaune ad’akinsa yana riqeda waya ahanunnunsa, “
Tun farkon fara abun yake kallo awayansa,”
Zafii yakejii sosai na amincewar hanna dan hakan yana nufin rabuwa da ita dan dolensa yayi hakuri, “
Dan yanda yaga MG daga yanayin kyansa da tsarinsama bazai iya ja dashi ba,”
Balle aje ga matsayinsa, “
Kuka kawai ya fashe dashi na bak’in Cikin rabuwa da hanna.” hakane ta faru da yaya jalal dan shima Hameeda ta kira shi duk wani abinda yafaru yana watching, “
Tun baiso hanna ta amince har yadawo yanajin tausqyin MG kuma har Cikin ransa yakeso hanna ta amince da auran MG ko bbu komai yasan cewa MG namata sonda shi baya mata kuma zairiketa tsakani da Allah, zaiso duk wani farin Cikin ta, zai faranta mata fiyeda yanda shi zaimata kuma shi arayuwarsa yanason ganin farincikin ta wanda yanada yakinin zata samu hakan, “
Shiyasa har Cikin ransa yaji dad’in amincewar da tayi duk da cewa yanajin kishi acikin ransa.”
Saleem kuwa yana Cikin kallo shida abokanansa farko dayace musu yarsace k’in yarda sukayi, “
Shine yace musu su d’aura bet su halarci wajen hakan yasa, suka nufii wajen a motar baban abokinsu daya d’auko musu dan tafiya yawo.”
Ita kuwa anty samha itada Abubakar da suke kallo farinciki kamar zai Kashe su, “
Anty samha ce tace wannan yarinyar taurin kai kamar ‘yar aljanu,”
Abubakar ne ya d’aga kafad’a sannan yace amma kinsan ni banga laifinta ba, harara anty samha ta galla masa sannan tace tana wahalarda bawan Allah amma a hakan burgeka tayi? “
Kuma abokinka ma,” riqo hannunta yayi sannan yace honey bazaki fahimci halin matane ba,”
Duk wanda yaga ta aureshi Ahaka zaice kud’insa ko mulkinsa ta ganii, “
Amma yin hakan zaisa daniya ta fahimci k’anwar taki ta dabance wani kyqlkyalin duniya duk baida metaa ba.”
Kwanciya tayi ajikinsa sannan tace ammadai duk da hakan nidai najii dad’ii ina farinciki, “
Cikin tsolaya yace anya kinkai ni kuwa nifa abokinane kuma cousine d’ina zaiyi aure na tabbata za’ayi bikinda duk fad’in kasarnan ba’a ta6a irinsa,”
Ahaka suma sukayi ta murnar farinciki. “
Ita kuwa adda hindu,”
Tsabar murna lokacin nak’uda ta tashi dama yaya auwal nakusa kawai suka wuce asibiti. “
Ina akabar iyalan gidan sarki kowa na gidan farin ciki idan kacire mutum biyu kilishi da intisar.”
Dan bakin ciki kamar zai kashesu intisar sa kilishi tayi agaba tanata rausa Ihuu, “
Ita ai dole sai kilishi tasan yanda tayi ta wargaza wannan aure,”
Kinji na fad’a miki abinda malam yace” yace wannan aure saiya yiwu, “
Amma mubari ayi auren ba za’a rasa abinyi ba kuma kinsan maganar malam daiko har inde yace zaiyyi abu to tabbas zaiyi ki kwatar da hankalinki.”
Cikin kuka intisar tace tayaya kikesoo na kwatar da hankalina umma kinsan irin sonda nake masa kuma kinacewa na kwantar da hankalii nayi shiru ya aurii wata ba niba wannan ma ba mai yiwuwa bane, “
Kiduba kiga yanda yazuba gwuiwo winsa ak’asa yana roqarta ta aure shi umma wannan wani irin so yake mata?”
Yabarni insonsa kamar zanyi hauka amma ko kallo ban isheshi ba. “
Kiduba wannan yarinya umma itafa bakyawun arziki ba,”
Kiduba na tabbata da za’a ajiyewa maza dari ita sai 99 sun d’aukeni basu kalleta ba kidubata fa tana fad’in haka takara fashewa da kuka, “
Ita kuwa kilishi sai rarrshinta takeyi dan tafi sonta fiyeda yaranta data haifa acikinta.”

Wajen su hanna kuwa celebration aka farayi kai har wanda ba’asan da zamansu bama sun zo wayan dan kallon wayannan masoyan kuma ba’a bari ashiga, “
Sai can su saleem suka iso anan aka k’i barinsu su shiga waya ya d’aga yakira hanna a lokacin ya turo wayarta najikinsa dan idan zaifita saiyabi yad’auke wayarta,”
Juyawa yayi yacewa abokan sa lahhhh na manta ashe phn d’inta najikina.”
Kallon mk’aryacii suka fara masa hakanne yasashi kiran hameeda itma bata d’auka dawuri ba sai da yayi 2missed call kafin tadaga, ” Tana d’auka yace sis muna waje fa anki bari mushigo ai babu b’ata lokacii hameeda tazo ta shigo dashi hadda abokansa.”
Tun daga nesa hanna wanda suke tsaye da labba tafara galla masa harara yana zuwa kusa tace ban wayana, “
Sosa kai yafarayi tace idanka k’ara d’aukamin waya Allah nidakai shi kuma sai ido yake mata akan ta bari abokansa amma takii,”
Sanda ta sulleshi tass sannan tabarshi, “
Amma duk da haka sai wani shan kanshi yake yiwa abokanansa shi ala dole, yarsa zata aurii mai mulki.”
Sai gab da magrib sannan sukabar wajan amma har tym d’in hanna bata bari sun Had’a ido da Yareema ba duk yanda yaso ya kebe yayi magana da ita abun ya faskara dan wata irin kunyarsa da kwarjininsane yarufeta.”
Sai dab magrib sukabar wajan gida suka nufa, “
Wanda Cikin wajan bbu wanda yasan meyake faruwa jira kawai sukeyi,”
Suna dawowa hameeda tafara zayyana Bayani nan tafara nuna musu, “
Mamane tace kadai anji jiki ace mutum taurin kai kamar maye,”
Umma ne tace kadai tunda ta amince zancen yawuce mana, “

Aranar su labba suka wuce,” washe gari kuma akatashi da shirye shiryen, kaiwa kayan tambaya. “

Plz kuyi hakuri da wannan.”

To be continued

Ur’s
z33yyb3rw3r

[9/24, 8:41 AM] ‪+234 810 367 2210‬: BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim

_
Writting by

© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )

Page 47

*
Tun sassafe aka fara shirin zuwa nemo aure, “
Alokacin aka kira baba aka sanar dashi zuwan,
Aikuwa yaje yasamu Abba ya fad’a masa.”
Abba ne yace amma yaya gani nayi kamar yayi wuri dasun bari nan da zuwa koda satii ne sai, “
Suzosu kaga yanzu bawani shiri mukayi ba.”
Babane yace nima abinda nagani kenan, amma idan mukace wani abu zasuga kamar basan abun mukayi ba. “
Kuma ni maganganunda yarinyar nan ta fad’a ranar auren samha sai ina kallo kamar akwai wani abuu ak’asa,”
Kaga kuwa yakamata mu amince musu ayi wannan zancen da wuri kamar yanda suka bukata.”
D’an gwauron numfashi Abba yaja sannan yace nima nayi tunanin hakan dan inaga akwai masu yiwa yarinyar nan ba dai-dai ba tunda dakanta tace aidama tasan bazasu barta ba, “
Acika mata burinta kamar yanda ta bukata abarta tazauna haka,”
Ai yaya kanajin wannan magana zakasan da wani abuu ak’asa, “
Kuma ta iya yiwuwa yanzu haka ita yarinyar tajii da kunnenta ne yasa ta fad’ar haka.”
Dan ni gaskiya yaya bazan 6oyeba gidankanna bakowa nayarda dashi ba kawai abun yafi yanzu mudage da addu’a sannan kuma musa ayita mana saukar qur’ani, “
Kasan mutum kai baka damu dashi ba amma kai yadamu da rayuwarka.”
Baba ne ya nisa sannan yace toh Allah yataimaka sai musan abinyi dan nasan zuwa jimawa zasu iso. “
Shiga Cikin gida sukayi,”
Suka samu mama da umma kud’in aikin da za’ayi na Cikin gida aka basu sannan su Abba suka wuce dan tanadarwa bak’i snacks da kuma drinks, “
Saleem ne ke fitowa daga dakiin su, Alokacin abokinsa yakirashi dan tun jiya sai samun kira yakeyi,”
Wa’yanda da ba frndz nasa bane, wanda then suna kallo mahaifinsa baida kud’in da zasuyi abota dashi yanzu haka sai kiransa sukeyi,”
Sunaso su jonehh. “
D’aukan wayan yayi cikin gadara.”
Daga can Cikin wayan nayi ance palz yadai naji wani labari wai dagaske ne? “
D’an gyarawa yayi yafara koro Bayani yanayi yana wani gadara,”
Aikuwa duk abinda yake fad’a a kunnen Ammah datake zaune abakin kofa,”
Rikicewa tayi wai metake jine waishin dagaske hanna aure zatayi?” kuma dan gidan sarkin kano zata aura?”
kamar yanda tajii Saleem yadad’a, “
Afili tace kai ina haka bamai yiwuwa bane.”
Shikuwa Saleem baimasan tanayi ba.”
Can garin kano kuwa MG harya gajii da amsa call, dan governor’s minister’s ambasador’s da president, “
Na k’asa she daban daban sai kiransa sukayi suna mai murna dan abu kamar wasa yabaza duniya sosai,”
Dayawa mutane ke sharing wannan video d’in. “
Aranar kuwa followe’r kamar zasu cinye, amira da hameeda.”
Kai har takaiga radio’s station, “
Tv chennel’s,”
Bana k’asarnan zallah ba har na k’asa she da yawa.”
Zance gabki d’aya ya karad’e duniya. “
Kowani tasha kika bud’e labaran kenan.” MG daya gajine da recieving call, kawai sai ya yanke call saidai massag gashi har yanzu yan wshing basu barshi ya d’an samu tym yakira hanna ba. “
K’anin mai martaba ne zaune a falon mai martaba,”
Magana yake yi, yana cewa, “
Yaya aduba wannan lamari gaskiya baida ce ace ya auri yar gidan talaka ba.”
Mahaifin yarinyar fa malamin makaranta ne,”
Kaduba matsayi da dukiya irinna yareema ga mulki, arasa wacce za’a aura masa sai yar gidan malamin makaranta yanzu yaya maiyaci yabawa iyalinsa har za’a gani ayi sha’awar aure? “
Ran mai martaba in yayi dubu yab’aci, dan irin maganganun da k’aninsa yake fad’i ya6ata masa rai,”
Amma dayake dattijo ne mai hakuri yasashi sharewa yabarshi yaci yacigaba da cewa ai wannan yakamata yayi tunda munada ‘ya’ya mata sai qhad’ashi da d’aya aciki, “
Mai martaba ne ya nisa sannan yace,”
Mai dukiya dakuma talaka duk Allah ne yayisu, “
Kuma inaso kasani koda yar bukka yareema yakawo yace yanaso toh ita zan aura masa.”
Balle mahaifin yarinyar yanada rufiin asirinsa duk abinda ake nema wajen aure to wannan yarinya da mahaifanta suna dashi addu’a yakamata muyi Allah yasanya alkhairii acikinsa. “
Duk da bahaka yasoba amma jikinsa yayi sanyi.” Ammah bata tsaya ko inaba sai gidan kawar ta aminiyarta,”
Hajiya lamii tana zuwa tafara mata birgima tana cewa wallhy malam yacuceni duk kud’in da nake she ace baimin aiki mai kyauba, “
Shege dan iska halama boka ne,” ????nikuwa nace kajimin amman nan dama ke atunaniki wajan malami kike zuwa toka kin yaudarii kankii. “
Dan wannan ba malamii bane.”
Hajiya lamii ne tayita rarrshinta sannan tace tayi hakuri su k’ara jarrava wani suganii,”
Cikin kuka Ammah tace mai nake dashi dazanje wajan wani kefa kina kallo na tattare duk kada rori na nasayar naba wannan macucin,”
Menake dashi dazan je wani waje,”
Cikin lallashi tace mata kiyi hakurii mutafii wani kauye abincika kinsan irinsu basusan zqfin kud’ii ba sai mu bincika.”
Cikin d’an gamsuwa da maganar ta Ammah tayi shiru sannan tace to yanzu yaya zanyi tace kodaiyaya kisan yanda kikayi kika nemo kud’ii koda bbu yawa, “
Gaki da yara ai Had’a musu wuta zakiyi sai sun nemo miki.”
Ahaka sukayi sallama Ammah tatafi bayan tagama kitsa mata makircii.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button