BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

To be continued

Ur’s

 Z33iiyyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirrahmanirrahim

Writing by
© Zaynab Bawa
( z33iiyyb3rw3r )

Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

 *Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, ku koyarda yaranku alqur'anii, dominshi lallai mai karanta qul'anii, yace (fii zillillahi) yana cikin inuwar Allah, yauma da (zilla illa zillahu) yace ranarda bbu wata inuwa sai inuwar Allah, wato ranar qiyama, Allah kabamu ikon karanta alqur'anii, ameen ya Allah*

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, ku ringa tuba zuwaga Allah, wato karinga karanta astagfirullah wa’atubu ilaik, kana qaskantarda kanka zuwa gareshi, koda sau d’ari arana d’aya.”

================

Page 68

*
Sai kusan 3:00pm kafin MG yadawo gida, ganin dawowarsa yasa matar shahid yimusu sallama ta fita, k’arasawa yayi wajan hanna data turo baki kamar zai ta6o k’ofa, dariya yayi ya Girgiza, kai yace yar rigimata anfara kenan, k’arasawa yayi tajuyar dakai gefe, yana murmushi yatar6o fuskanta yace, beb yane turo baki tak’arayi, yace ko yunwa kikeji?”
Kamar zatayi kuka tace bakai bane, nine nayi meh?”
Katafii kace zaka dawo dawurii kuma kak’ii dawowa,”
Owhh srry dear kinsan nikaina bansan zansamu aikii hakaba, amma ai duk laipynki ne, laipyna kuma?”
Eh laipynki ne mana tunda naje Nigeria kikak’ii ki barnii harsanda na auroki tukunna, kinsan cewa 6 month kenan banzo k’asarnanba?” nazo nasamu matsala dayawwa, yanzu dole sainayi making dinsu up,”
Dan haka yanzu kinga ai ba laipyna bane.”
Sake fuska tayi tace tom muje kacii abincii, ke kincii ne?”
yatambayeta A’a banciiba inajirankane, ok tom muje kimin wanka sai incii abincii.”
Tabb mujedai kayi wanka, kafin ka yi sai inhad’a mana abincinn,”
Girgiza kai yayi yace wataran basaina roqa bama.”
Ta6e baki tayi tace ai watarana kace.”
Haka yashiga wanka tafito masa da kayanda zaisa, ta ahjiye akan bed, tafita tashirya musu abincii.”
Fitowa yayi da armless shirt dakuma 3quater, k’arasowa yayi dining d’in , yanacewa beb baki tausayina kikabanii wannan kayan, ana sanyii fahh.”
Tabace komaiba haryazo yazauna, zuba abincin tayi aplate d’aya kuma d’an kad’an, kallonta yayi yace ya kika zuba kad’an?”
Ni bazanciba tabashi amsa atakaice, bazakiciba kuma?”
Eh tace,”
Meyasa to?”
Nifa banta6a cin irin wannan abincinba.”
Kallon abincin yayi sai alokacin yatuno cewa itafa bata saba cin wannan abincin ba,”
Tashi taga yayi, tace kazauna kacii mana, A’a yabata amsa atakaice tace to meyasa, bazan iyacinn wani abuu sweetyna bataciiba, je kid’auko mayafinki mufita na nema miki abincii, toh tace sannan takoma, shikuma yashiga yad’auko fanko na jallabiya sabuwa yabud’e yasaka, itama tafito suka fice,”
Had’eda sojojinsa, wanda bai ebii dayawaba kawai ya ebii wanda zasu rakashine, dan bbu halii yatafii shikad’ai.”
Ahanya sai zuba masa labarii takeyii yayi shiru, daga alamu akwai abunda yake tunani.”
Har suka iso bakn wani k’aton mall wanda zaiyi mata shopping na mak’ulashe.”
Har hanna tabd’e k’ofa zata fita yariqo hannunta yace, kijiranii mana sarkin y’an saurrr,,,,,, aibaki k’arsaba yajii k’aran harbii wanda da’alamu harbin wajensu ake hara.”
Lokacii d’aya kuma aka bud’ewa motocin wuta sosai, tako ina harbii akeyi har yakaiga anharbii, daywa daga cikin sojojinsa.”
Shikuma hanna kawai yake tunani yariqe kanta yakwantar k’asa, itakuwa hanna 6arii kawai jikinta yakeyii, sai kuka takeyi tabi tad’agawa MG hankali, yarasa yanda zaiyii, yanaso yafita amma ta duk’unk’uneshi.”
Dakyar yasamu yab’anbare yace ta rufe idanuwanta, ta kuma toahe kunnanta kada ta bud’e saitajiishii, d’aga masa kai tayi, yace yaewa rufe, dank’e idanuwan ta tayi sjlhikuma yabud’e tad’ayan gefen zai fita, dan dama duk soldier’s dinsa sunfita saurashi kad’ai, jin karara bud’e kofa yasata bud’e idanuwa tace, inazakaje?”
Plz karka futa zasu kasheka,murmushi yayi kawai yace, ilove u yasakai yafice, yarufo mata k’ofar, garam, itakuwa dake motar bullet proof ne yasata k’in kwanta, sai juye juye takeyii, neman MG kawai takeyi, can ta hango lokacinda c.Ahmad ya cillo masa bindiga, MG yamatuk’ar harzuqa ganin yanda wasu dage cikin sojojinsa akwance, ga mutanen garii yanda abun yarutsa dasuu, ta wajan da mutanen suke kawai MG yanufa, harbi kawai yakeyii, duk wanda yaharba baya harbinsa awajenda zai tashii, kisa kawai yakeyi nana danan hankalin hanna yatashi ganin yanda MG ke kisa ko alamun imanii bbu, wata irin tsanarsace ta d’arsu aranta, Kukan yak’ii zuwa mata gabaki d’aya, aikuwa sai numfashinta yafara sama-sama, acikin motar ta sulale ta sumee ko numfashii bbu.”
Su kuwa MG yad’auki 30minute kafin yagama clearing komai, mutum d’qya suka barii araye, a”inda zasu bincikeshi dansusan wajen zamansu,”
Alokacin aka fara d’bar wanda suka samu raunuka, suka yi asibiti dashi, acikin sojoji, bbu wanda yarsu. Saidai munanan raunuka, su kuwa sauran mutane yaro d’ya dakuma wani mutum sunmutu,
Yana bud’e kofa yaga hanna ahaka, dasaurii yasa hannu ya d’aukota, bayadda beyiba amma hanna ko motsii, ambulance yanufa yasata duk hanklinsa atashe, ko numfashi batayi yad’aurata akan bed d’in nan likitocii suka shiga vata taimako kafin a”isa asibiti.”
Hannunsa yaduba ynada yabacii da jini, tsorone yakamashi, badai anharbeta nan danan MG yafara surutai kamar wanda yazauce, yanayii yana, hucii, idanuwansa sunkad’a sunyii jajirr, kamar jinii ganin dagske jinin daga jikinta yake,
Sun d’auki 20 kafin suka is hospital, dama tuntunii ansan da zuwansu, ana isa suka karbi hanna suka shiga bata taimakoo.”

To be contineud

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirrahmanirrahim

Writing by
© Zaynab Bawa
( z33iiyyb3rw3r )

Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

Manzon Allah tsira da amincin Allah Su tabbata agareshi yace, har indai kakaranta wannan addu’ar da safe.” Allah humma innii as'alukal jannah, wama yuk'arribunii ilaiha min qaulin wa amal, wa a'uzubika minal narr, wama yuk'arribunii ilaiha min qaulin wa amal."
Bazakq gushe kana karanta wannan addu’ar ba, face Aljannah tayi addu’a tace, ya Allah ina roko ka kawo wannan Bawa naka cikina, wuta sai tayi addu’a tace Allah ka kare wannan Bawa naka daga shiga cikina.”

*Akwai wani lokacii da wani mutum yazo wajan Manzon Allah yace ya rasulillahi, inaso kabanii shawara, sai Manzon Allah yace masa *(la tagdabb)* *kada kayii fushii, sai wannan mutumi yak’ara cewa ya habibullah inaso kabanii shawara, thumma k’ala rasulillahi *(lah tagdabb)* kada kayii fushii, sanda sukayi haka har sau uku da Manzon Allah.”
Manzon Allah (SWA) yace ku nemi tsarii daga fushii tahanyar karanata a”zuubillahi minal shaid’anurra jimm.”
Allah karabamu da yinn fushii dakuma yanke hukuncii cikin fushii.” Ameen ya Allah.”

================

Page 69

*
Likitocii Basu dad’e akanta ba suka fito, suna fitowa wajen MG suka nufa. Babban liktanne yace, Major ka kwantar da hankalinka, she’s out off risk now, but tana buk’atar rest, for about 2hour’s danta razana.”
Haryanzu hankalinshi ba akwance yakeba.”
Tunaninsa jinin dayaganii ajikinta nameye. riqe hannun doctor yayi yace jininda take zubarwafa?” badai harbinta akayi ba?.”
Girgiza kai liktan yayi yace, tsoratan datayii ne yasa, mensturation d’inta yazo, a wannan lokacin, dake date d’in yakusa yasa jinin ya matso kusa, kuma dalilin tsorata datayii yasashi tsinkewa, amma bayan haka bbu komai, sai alokacin MG yafitar d numfashi yana furta Alhmdllhy kawai dan bbu abinda zai iya cewa.”
D’akinda take yawuce, yana bud’e k’ofar da sassafar yak’arasa bakin gadon, yariqe hannunta, itakuma tana baccinta, numfashinta nasauka ahankalii.”
Fuskanta yayi fayau, bakinsa yakai kan goshinta ya sumbata, yak’ureta da ido kawai.”
Wayrshice tayi k’ara, dube – dube yafara danshi baiyi tunanin cewa wayarsa na aljihunsa ba.”
Jin k’arar ajikinsa yasa yakai hannunsa aljihu, yana ta6awa kuwa yajita cirowa yayi, nan ake gayamasa meeting nanda 3hour,”
Kallon hanna yayi duk saiyajii bbu dad’ii, kasan cewaar dole yatafii kan lokacin yacika, hakan yana nufiin bazata tashii agabansa ba kenan.”
Wani d’an siririn tsaki yaja wanda saida yafito fili duk saiyajii ransa ya6acii dan baiso ace yarabu da hanna kona secound d’aya balle tanacikin wannan halin.”
Yakusan 1hour ahaka Jin kiran sallan magrib ya tuno ko la’asar baiyiba.”
Tashii yayi ya shiga toilet,yad’auro alwala, dake da sabon carfet ashimfid’e sai yayi sallan la’asar akai sannan yagabatar da magrib.”
Dake soldirer’s d’insama asibitin daa akawosu kenan yasashi fita yadubasu kowanne, wasu harsun farfad’o, wasu kuma haryanzu bbu alamun farfad’owa.”yana komawa d’akin da hanna take shida wasu sojojin da aka turo masa daga baya, had’uwa sukayi da abid dake zuwa shida matarsa da d’ansu d’aya.”
Ganin matar abid yasa shi, tafiya amma dakyar dan hankalinsa yanakan hanna shida abid suka juya suka tafii, Su uku suka had’a motocinsu da sojojin Su zuwa wajan meeting d’in.”
Sun d’auki awowi dayawa wajan meeting d’in, awajanne ake shaida musu cewa yanda aka musu da cewa nan da 1month akeso sukawo
k’arshen wannan terrorism d’in, d’an Sun kashe sojojin dayawa da musu mulki, a wannan karan suka kawowa MG harii wanda k’asahen dayawa bazasu iya taasashiba, gwara, Su fataucesu tun kafin dawowarsu.”
Ahaka Ahaka aka tashii a meeting d’in.” Alokacin hanna tayi kusan 2hour’s datashi, ganin tafarfad’o bbu MG awajan wani bak’in ciki yakamata wato bazai iyajiranta tafarka ba kenan?”
Zai tafii damuwarsa.”
Suna barin wajan bbu yanda basuyi da MG ba ko gida yayi ya, gani yakeyi kamar yayi shekara baiga hanna ba yasan aduk yanda take yanzu tafarka.” da d’an saurinsa ya shiga cikin asibitin ko soldirer’s d’insama bai jiraba.”
Yana bud’e k’ofa, idanuuwan sune suka had’u waje d’aya wani irin haushinsa ne yakamata.”
Hawaye tajii yana k’okarin zuwa Mata tayi saurin kauda kanta.”
Dasaurii yak’arasa yayi hugging nata tight har wani d’an nishii tayi,ganin matar abid awajen kawai sai kunya takamata, saketa yayi yanaso ya hango kwayar idanuwanta amma firr taqii dantayi k’asa da kanta.”
Hannunta yake murzawa alokacin yana tambauarta tacii abincii tace, d’aga kai kawai tayii, dan idan zatqyi magana to kukane Zai biyo baya.”
Sai Lokacin MG yalura da matar abid dake wajan, cewa yayi au namanta abid yana jiranki yana waje.”
Dariya tayi tace yaushe zaka tuna, aina lura idankana tareda matarka baka ganin kowa.”
Shiryawa tayi, sannan tajuya zata yiwa hanna sallama narai-narai tayi da idanuwanta tace dan Allah karki tafii, mukwana anan.”
A’adai gashinan yadawo nasan cewa tun d’azu dakikak’ii magana shii kike jira.”
Tana fad’iin haka tajuya tafice, hanna Tana ganin tafita tajuyar dakai hawaye nabinn fuskarta, kwanciya tayi tajuya bayanta, yazo dabb da ita yana Mata magana amma tak’ii kulashii, duk yanda yaso tamasa magana amma tak’ii, ahaka har tayi bacci.”
Sai kusan 2:00.am kafin tatashi, nan ma firr tak’ii ta mishi magana, Koda yamatsa sai tasa masa kuka.”
Zuwa yayi da niyyar yariqeta ya rarrsheta, tace ni karka ta6anii, wallhy nadad’e banga marar imanii irinkaba.”
Har zaka iya kashe raii wallhy saidai, kamaidanii gidanmuu.”
Runtse ido yayi dan yasan haka zata faruu.”
Bayadda za’ace taga mijinta yayi kisa kuma ta aminta dashi awawannan lokacin, gashi yanada tabbacin ko kokuwa mai k’arfii hanna bataa ta6a kallo ba.”
Ahaka yak’arasa tana kuka amma ya manna ta ajikinsa.”
Ba yadda batayi takwace ba amma kuma abun ya faskara,”
Kwantarda kanta tayi tacii gaba da kuka, furzarda iska mai tsafii kawai yakeyi, dan baison kukanta, zafii yakejii acikin zuciyarsa, kokad’an baison 6acin ranta.”
MG ayanda yad’auki abun ba haka yayi zato ba.”
Dan har akayi sallah bai runtsa ba hanna rikicii kawai takeyii.”
Duk yanda yaso yayi calming d’inta abun yak’ii haka ad’akin yayi sallah, daga ita harshi tun breakfast najiyane a cikinsu.”
Sai a d’akin yatashi yayi sallah Zuwa safiya dole yanemii sallama wajan likita dan bazai iya da rikicin hanna a asibiti ba.”
Zuwa 9 aka sallamesu, amota ko kulashii batayiba shikuma duk wani motsin ta yanakan idanuwansa.” Suna isa yace ta shiga tayi wanka, bbu musu tashiga tayi dan itama kanta wani irii takejin jikinta.” tana fitowa awanka taahirya, saiga matan abid da Mata shahid sunshigo, abincii suka kawo Mata tacii sai ita, MG ganin tacii abincin hankalinsa yakwanta.”
Sai alokacin shima yasamu yashiga wanka, yad’ansa wani abu abaknsa.”
Labarin abunda yafaruu harya karad’e duniya, yanzu haka ma, Su ummii sai neman layinsa sukeyi.”
Saida yayi wanka sannan yakunna phn dinsa wayan ummii ne tafara shigowa, d’auka yayi daga yanda ummii Ke magana kasan hankalinta atashe yake.”
Kwantar Mata da hankalii yayi yace Mata bbu abunda yasameshi, dakyar ya lallasheta yad’an Kwantar Mata da hankali.”
Haka ma mai martaba kowa idan yakira saiya tambayi hanna dan bbu wanda yayi zaton tana wajan abun yafaruu, kowa yabarii akan tana gida, shikuwa ganin haka yasa baifad’a musu ba dan baiso hanakalinsu yatshii.”
Intisar data kirashi kuka takeyi tsakanii da Allah dakyar yasamu tayi shiru.”
Ajiyar zuciya kawai takeyi, yanzu yarinyar nabawa MG matuk’ar tausayii, dan yasan tana sonsa sosai, shikuwa kosaau d’aya bai ta6ajin sonta bayaga na y’an uwantakaba, duk lokacinda akace wani abuu yasameshi, takanfii kowa nuna tashinn hankalinta.”
Yana tausayin duk wani mai kok’arin shiga yanda hanna take, yasan ko takalmin hanna saiya fishii soyuwa a’iidanuwansa, Koda kullun hanna zata ringa yanka neman jikinsa shidai yanasonta, akullum yanajin zafii idan yaga 6acin ranta.”
Shikansa yasan wannan jarabawace ta ubangijii, ance zuciya nasan mai kyautata Mata, amma shi nashi zuciyar har indai akan hanna ne ko munana Mata takeyii yanasonta.”
Nisawa yayi ya lumshe ido, afili yafurta insonki hanna har iya k’arshen rayuwata.”
Tashii yayi yanifii falo dan sake ganinta, Koda bata d’ago ta kalleshi ba yakanjii dad’ii aransa, yakanjii sanyii.”
Juyawa yaje zaiyi wayanshi tad’auki k’ara,”
D’agowa hanna tayi tadubeshi sannan takawar dakai, tad’anja siririn tsaki, kallonta matar abid tayi tace wani wajanne Ke miki ciwo?”
Girgiza Mata Kai tayi kawai ta kwanta, ganin ta lumshe ido yatsaya daga nesa yana k’are Mata kallo.”
Wani dad”ii ne yaziyarcii xuciyarsa ganin yanda dangin hanna suka damu dashi tun d’azu suke kiransa dan sujii lafiyarsa, duk abinda yashafii hanna yana mutuntashi yana bashi kimarsa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button