BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

================

This page is dedicated To you, FATIMA IBRAHIM(MUNEERAT) and SAWWAMA QAWWAMA (doughter) Allah yabarni tare daku har abadan."

.

================

Page 86

*
Jin kiran gaggawa daga asibiti yasa hankalin marshall masifar tashi, tun d’azu kawai yana meeting ne amma kuma hankalinsa na hospital, yarasa dalilin dayasa tunda yatashi gabansa ke fad’uwa hakanne yasa dakyar sanda ummii tasaka baki kafin ya halarcii meeting d’in.”
Ana cikin yii ko excuse bai d’aukaba ya fice, soldier’s suna kallonsa sukayi saurin bud’e masa k’ofa, dasaurinsa yashige, drivern yafara driving har suka iso hospital d’in, dasaurii ya fito ya nufii ciki suma suka mara masa baya, sanda yazo bakin k’ kofar shiga d’akinda aka kwantarda hanna ne sukaja suka tsaya, shi kuma yak’arasa, ganin ummii akan gadon marassa lpy dasaurii yak’arsa yana tambayarta mai yafaru?”
Ummii wani abune yasameki?” maimakon naga hanna naganki kota samu lpy ne?”
Muryan affan ne dake bayansa yakatseshi, yace yaya wallhy tund’azu nafad’a musu su sanarda ni abunda yake faruwa amma kuka kawai sukeyi bbu wanda yakulani.”
Dasaurii yakuya wajan Umma yana cewa Umma wani abunne yasamu hanna Umma dan Allah kifad’amun, jijinsa rawa kawai yakeyi.”
Kawarda kai gefe Umma tayi bata iya bashi amsa ba, gabaki d’aya tausayinsa ne yayi mugun kamata, kuka kawai takeyi, yajuya zuwaga hameeda dake k’asa numfashinta yana kok’arin d’aukewa, ai kafin yak’arso yasamu damar tambayar ta numfashinta yad’auke cakk, nan ta sulale k’asa sumammiyya.”
Muryar ummii ne ta daki dodon kunnuwansa,
Tana cewa Abdallah hanna ta6ata wallhy bamusan yanda takeba.”
Zuciyarsa ne tayi wani irin bugawa take wani abuu ya tunkaroshi da k’arfii ak’ok’on Zuciyarsa, abun tasowa yakeyi har wuyansa, tashi d’aya yayi wani tarii gudan jini ne yafad’o wanda duka d’akin sanda ya suka jijjiga, dasaurii affan yayi kansa yana kiran sunansa amma, d’aga masa hannu kawai yayi yatsaya cakk, yayinda shi kuma yaja da baya, yajingunu da bango, yazauna ya sunkuyarda kansa, d’akin yad’auki 10 minute ahaka bbu wanda ya’iiya magana, ga hameeda asume marshall kuwa ban isa ince yana sume ko yanada rai kokuma baudashi ba.” ga ummii itama hankalinta yayi masifar tashi naganin aman da marshall yayi.”
Umma kuwa tadawo mutum mutumii.”
Haka ummii tasauko tanufii marshall Tana kuka tana masa magana amma ko kiftawa idanuwansa bayayi, haka tayita jijjigashi ko motsi bai yiba.”
Zama tayi kawai agabansa, tana kuka, ganin abunda ke faruwa, yasa affan ficewa yasanarda mai martaba, ba’ad’auki lokaci ba ya’iso, hospital d’in,

Yana zuwa ganin abunda ke faruwa, yasa hankalinsa mugun tashi, nan aka kira doctor’s aka tafida hameeda, yayinda shikuma marshall mahaifinsa yayi kansa yana masa magana, amma ko motsi baiba.”
Ganin haka yasa mai martaba dakyar ya lallashi ummii aka tafii da ita gida, Umma kuma tana wajan hameeda.”
Awah ukuu curr marshall yad’auka awannan hali.”
Wata ajiyar zuciya mai k’aran gaske ya sauke, itane tajawo hankalin mahaifinsa, k’arasowa kusada shi yayi yana kiran sunansa, d’agowa marshall yayi da jajjayen idanuwanshi, yatsare mahaifin nasa da kallo kamar wanda yau yata6a kallonsa.”
Nisawa mai martaba yayi yace, yareema tashi mutafii gida, girgiza kai yayi yace A’a abba bazan tafii ba, zata dawo, zan jirata.” girgiza masa kai mai martaba yayi yace Zamu nemota kataso mutumii, zaiyi magana mai martaba yayi saurin katseshi yace, kada muyi haka dakai, yareeema ka tashi mutafii, har indai nine nahaifeka kabii umarnina, miqewa yayi yana Shirin fad’uwa mahaifinsa yayi saurin riqoshi, haka yafita dashi daga cikin asibitin yariqe hannunsa kamar k’aramun yaro, shikuma yana ta kalle kalle, haka mai martaba ya sashi amota suka nufii, gida.”

PLZ KUTAYANII DA ADDU’A WALLHY INACIKIN DAMUWA SOSAI ,???????????????????? INA CIKIN MATUK’AR DAMUWA , DOLE INA BUK’ATAR ADDU’A DINKU , KUYIWA GIRMAN ALLAH KUJII TAUSAYINA KUMIN ADDU’A .” KARKU GA TYPING YAYI KAD’AN AYANAYIN DA NAKE CIKIMA DA BAZAN IYABA, BUK’ATAR ADDU’A DIN KU DA NAKEYI NE YASA , NAYI , DAN AllahT KADA KU MANTA DANI .”
KU D’AGA HANNU KU ROQAMIN ALLAH YABIYAMUN BUKATUNA.

Kuyi hak’uri ko zakuga mistake, wallhy dada rana nayi typing da yayi yawa amma yanzukan sai neman gyaran ubangiji.”

To be continued

Ur’s

 Z33iiyyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

بسم الله الرحمن الرحيم

Writing by
©zaynab bawa
(Z33iiyyb3rw3r)

Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels

Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S

Manzon tsirada amincin Allah su tabbata agareshi Yana cewa Allah ya jikan wanda ya yi sallar nafila raka'a hudu kamin la'asar.

Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi yace, Wanda da yi Sallar nafila a cikin duhu inda bawanda zai ganshi to Allah zai' linka masa sau ashirin da biyar na sallar da zai yi wani ya ganshi.

Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata agareshi ya ce, Wanda yayi sallar walha (Sallar hantsi/Luha) rakaa hudu kuma yayi rakaa hudu kamin sallar laasar, Allah zai gina masa gida a cikin aljanna.

.

Page 87

*
Fad’in irin tashin hankalin da marshall yashiga wannan ma tsayawa, bata lokaci ne, gabaki d’aya yazama wani iri, bud’e idanuwansa ma wahala suke bashi, balle aje ga cin abincii ko wani abun.” nauyii idanuwansa ke masa, alokacinne yak’ulla mugun alaqa da ciwon kai, wanda akullum kansa ke barazanar tsagewa gida biyu,
Baida sukunii, baida wani sauran kwanciyar hankali, kullum cikin zullumi da tunanin yanda hanna tashiga yake, tunaninsa ko awana irin hali take, baisani ba.” a kullum har wani hucii ne mai d’umi yake fita daga jikinsa, idanuwansa kuwa idanya bud’e yanda kasan garwashi, har shakkarr bud’esu yakanyi, dan har indai mutum yana kusadashi sayyya razana, sa’ii-sa’ii yakanyi aman jini, amma bai bari kowa ya lura ba, koda sallah ma ad’aki yakeyi, ummiii tayi kukan harta gajii,

Ganin bbu Wata mafita yasa umma takira mama akan tanason ganinta idan zata samu dama suzo suda baba, dafarko mama tayi tunanin su hassana da hussaina,
Hakan tafad’awa umman, amma umma tace mata tabarsu ma ammah tazo, ganin zancen mai k’arfii ne yasa tasanarda baba, kiran k’aninsa yayi awaya, abba yacewa baba gaskiya yanadakyau zuwannasu, haka suka shirya washe garii suka d’auki hanyar kano, sha d’aya tamusu acikin garin kano, gidan Abba suka wuce kai tsaye, ganin Wata irin ramar da umma tayi mama ta matuk’ar tsorata, dasaurii tak’arasa kusada ita, riqo hannunta mama tayi cikin kid’ima tafara magana, yaya menene yasameki haka?” yaya dama bakida lpy ne baki fad’amunba?, girgiza mata kai umma tayi kawai hawaye nabin fuskarta, da sallama abba yashigo falon, ganin umma na hawaye yasa yace ashsha assha, yanzu daga zuwansu kintaryesu da kuka, hava da Allah wai kekam bakyada hakurii ne, kuma bakida juriya, hava, idon mama har yacika da hawaye tashi d’aya yafara zubo mata takalli abba tace dan Allah kafad’amun ko wani abun ne ke damunta, rintsawa abba yayi kafin yace, kuzauna ku huta kafin namuku bayani, girgiza kai mama tayi tace, nidai bazan iya wani hutawa ba, bayan Ina kallon y’ar uwata cikin wani hali, juyawa abba yayi batareda yak’ara cewa komai ba, yanufii babban palour wajan baba.”
Duk yanda mama taso tambayar umma abunda ke faruwa takasa sanarda ita, abba baifii 10minute da tafiya ba ya leqo yace, sutaso su tafii, tunda suka d’auki hanya bbu wanda ya iya magana, ganin sun nufi fadah yasa gaban mama da baba yayi mugun fad’uwa tunainsu d’aya badai wani abun bane yasamu hanna sunfii ma karkata da ko batada lpy ne, har suka isa fada, bbu wanda yatofa ko da kalma d’ayane, dama ansan da zuwansu, dan haka falon mai martaba, aka sauk’esu marshall na kwance tun shigarsu afalo, amma bai iya d’aga kansa ya kallesu ba balle susaran zai gaidasu abun bak’aramun mamaki yabawa baba da mama ba, banda umma da abba dan dama sunsan irin halinda yake ciki, tunda hanna ta6ata bai k’ara furta ko kalma d’aya ba, ummii da mai martaba ne sukayi sallama suka shigo falon daga d’akinsa, waje mai martaba yasamu yazauna, sannan yabawa su abba hannu suka gogaisa da addu’a yabud’e taron sannan yafara magana.”
Kusani cewa Duk wani abunda yafaru muqadda rine daga Allah, kuma Allah subhanahu Wata ala yace, la yukalliful lahuu nafsan illa wus’aha, yace Allah baid’aura rai abunda bazata iya ba.” sannan Kusani kowani d’an adam da irin hanyardaa Allah ke jarabtarsa, sai dai muyi addu’a Allah yabamu damar cinye tamu jarabawar data fad’o mana, sannan d’aukan qaddara yana d’aya daga cikin cikon imani, musani Allah baid’aura mana abuu har sai dan yagwada imaninmu
Yaga yaya jamuyi dan yajarabcemu, tundaga wannan lokacii ummii tafara hawaye tana goge hawayen idanuwanta, nan mama tak’ara karyewa sosai tace,” ku gayamun maiya samu hanna mu musulmaine tabbas zamu kar6i kaddar mu hannu bibbbiyu, zamu riqe wannan jarabawa, dakyau mumata kyakyawan duba yanda idan skamakon mu yatashi futowa zamu samu sakamako mai kyau.” ita kanta duniyar nawa take?” kan ummii nak’asa takasa d’agowa takallesu tace hanna ta 6ata wallhy hanna ta6ata, gaban mama ne yafad’i rass, wani irin jirii ne yafara ebanta, amma kuma duk dauriyarta ta tattaro, da mamakin mutanen wajan gabaki d’aya, murunushine kwance afuskarta, sannan cikin dakiya tace, kada ku damu da sanin Allah in sha Allah zai bayyanata, addu’arda zamu mata Allah yasa tana wajan kyakyawan hannu.”
Shima baban dukda cewa abun yadakeshi addu’ar kawai yayi, share hawayen idonta umma tayi sannan tace, Aisha abun damuwar d’aya shine hanna bata cikin hankakinta lokacin da ta 6ata, hanna tahad’u da ta6ewar hankali, abunda yasa bangaya miki ba, bawanda yad’auka, zata dad’e cikin wannan jinyar, dan Allah kiyi hakuri, girgiza kai mama tayi tace hava yaya wani irin hak’urii kike bani?” bayan kuma mahaifanta ne, nasan kulawarda zaku bata, ko da inanan bazan bata hakanba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button