BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai tsaye (mass general hospital bostoon International) aka nufa da shi.
Manya man yan likitoci ne suka shiga theatre dashi. kokari su keyi na ganin sun ciro harsashan dake cikin jikin sa.
Ummii ne zaune a falo ita da wata ‘yar aikin ta tana matsa Mata kafa. ji tayi ga baki d’aya ba ta cikin nutsuwar ta.
Hakan yasa ta umarci d’aya ‘yar aikin da take yan ka mata friut data kunna Mata TV.
Hankalin ta baya Kan tv d’in Amma labaran da taji a nayi ne yayi saurin jawo hankalinta wajan.
Idan ba kunnuwan ta karya suka Mata ba, taji a na cewa an harbi MG Abdullahi Abdul-Aziz lamido. Wanda a halin yanxu ba’a san yana raye koh yana maceh ba.
Hawaye ne ya fara bin fustan ta bbu abin da take nana tawa Sai inna lillahi wa’innah ilaihi raji’un.! Wanda hakan ne yaja hankalin yan aikin ta suma ju yawa su kayi Dan kallon abin da ya razana ta. ihu d’aya daga cikin su Wanda ya jawo hankalin sojojin dake bakin gate da cikin harabar gidan shigowa.
A razene suka yiyo cikin gidan, dan ganin abun da yake faruwa. Kan Wanda tasa hanu akayi tana kwalla ihu su kayi suna tambayar ta abunda ya faru dan basu lura da ummi data dade da zama mutum mutumi ba a kwance. Wanda bata gane komai a lokacin. TV ta nuna musu da ga baki daya hankalin su ya Kai kololuwa wajan tashi.
Ihu da sambatun sojojin ne ya dawo da Ummii han kalin ta tashi cikin tashin hankali ta musu umarni da su kaita a sibitin. Dan kuka yaki zuwa Mata gani ta keyi kaman karya ne.
Fita suka yi Dan rakata asibitin motoci uku ne suka cika da sojojin Sai Wanda Ummii take a cikin d’aya. Kai tsaye asibitin suka nufa dan ganin abun da yake waka na….
To be continued
Ur’s
Z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim
_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )
Dedicated to ummi aysha (haske Writter )
Page 18
*
Wata irin faduwar gaba ne yake damunta ayau, kuma tarasa dalili.
Hakanne yasa ko waje batayi sha’awan fita ba.
kasan cewar ranar asabar ce, bbu lectures, zama tayi kawai tana tunanin dalilin wannan faduwar gaban tata
Can zancen mutanen na shekaran jiya yafado Mata.
Addu’a tasamu kanta da kara yimasa na Allah yakareshi.
Dakyar taya kice damuwaar aranta, domin kar hameeda ta fahimci wani Abu.
Cigaba sukayi da hidimominsu kamar bbu abinda yake damunta,
Amma Can cikin zuciyarta damuwa ce sosai.
Kusan karfe shadaya 11:00
Tashiga falon babansu dake yana gida bbu office.
Da Sallama Tashiga ya amsa Mata cikin farin ciki,
Nadauka yar tawa yau baza tazo taya abbanta hira bane, saboda akwai yar uwarta kusa da itah.
Murmushi tayi sannan takarasa shigowa ciki, tazauna akasa kusada kafar sa.
Dama wannan ka'ida ne duk ran asabar tana tareda mahaifinta tana tayashi hira "sannu da hutawa baba, yawwa sannu *hannatun* baba.
Murmushi tayi najin dadin sunan da baba ke kiranta dashi.
Tad'i suka fara yi "irin" na d'iya da mahaifinta, cikin farin ciki da annashuwa.
Aljazeerah! Yake kallo, Amma hankalinsu gabaki daya yanakan tad’insu, tunda ta shigo yamaida hankalinsa kanta, danjin ko akwai Wata damuwa atattare da ita.
Saurin daukan remote yayi "yana kara sauti, subhanallahi, Kai mutane babu Imani, wato duk wani mai gaskiya Sai sunga bayansa.
TV take kallo haikam.
wanda tagama tabbatar wa wannan da yanxu ake fadin an harbeshi, A Aljazeerah”
Shine Wanda ranar sukaji Ana zancen kasheshi,
Batasan lokacin da hawaye yafara bin fustan taba, tsan tsan tausayin sane ya cika Mata ruhi,
Lallai wa ‘yan nan mutane sun ciki azzalumai marassa imani.
Juyawa baba yayi gunta dan yimata magana,
Tsintar ta yayi hawaye daya nabin daya.
Juyawa yayi yaga yanda take kallo.
TV takurawa idoh, sanin zancen da’ akeyi a tv din yasa yayi tsammanin tausayi,
Yabata.
Dan yasan itah! Mutum ce” mai tausayi.
Lallashinta yashiga yi” sannan yace taje daki ta kwanta ,
Tashi tayi ta fita, yabita da kallon tausayi,
Shiga d'aki tayi, takwanta rub da ciki akan gado, Sai zullumin wayannan mutane takeyi aranta.
Hameedah ce" tashigo daka Mata duka tayi, ke Ina kika shiga inata nemanki, saida ta'iso kusa talura da halin da 'yar uwar tata tashiga.
Zaunawa tayi kusa da ita!! Taci gaba da Lallashinta, dan ganinta awannan yanayin tasan ambata Mata rai ne.
================
Koda zuwan su Ummii basusha wahalan shigaba.
Dan akwai abinda sojoinsa suke d’ aurawa adam tsen hannunsu.
Ganin haka yasa bbu bata lokaci suka cika cikin asibitin.
Cikin dakin Theatre kuwa,,
Angano dayan harsashin rigar bullet proof dake jikinsa ta tare,
Inda dayan na gefen cikin sa ” harsashin bulawa yayi ya fice.
Amma dayake ba Kowani irin harsashi bane, anyi shine na musamman mai hade da guba yasa yaratsa jikinsa sosai.
Gubar mai karfi ce.
Koda kirjinsa da yake da riga Amma sanda wajan yayi shatin baki.
Sun dauki akalla awah hudu akansa.
Kafin sukayi iya kokarin na ganin sun kashe karfin Gubar.
Saida suka kammala komai. lokacin awansu hudu da rabi da shiga theatre.
Inda haryanzu maganin bai fara aiki ba, Sai yayi 1hour ajikinsa kafin yafara kashe Gubar.
Lokaci daya suka gama aka futo dashi, ko numfashi bayayi.
Aka kaishi zuwa wani d`aki mai tsaron gaske.
C I D camera ne takowani sako na dakin.
Nan aka ajiyeshi.
Dan zuwa nan da 2hours numfashinsa zai iya dawowa.
Yanxu roban numfashi ne amaqale a hancinsa.
Wajen dakin kuwa sojojine masu tsaransa birjik, tundaga gate din asibitin.
Ummii kuma na kofar dakin da yake, addu'a kawai takeyi, kokadan tunaninta bai kawo ta "khira mahaifin sa ba.
================
Mai mar taba ne zaune a faadaa.
Wayar sa da ke hannun wani bafade ne, tadauki ruri.
Kallon sa sarki yayi alamun ya amsa, amsa kiran yayi tareda karawa mai martaba akunne.
Sallama akayi ya amsa.
Meh????? Yaushe???? A’inah?? Shine abinda sarki yace, inna lillahi wa’inna ilaihi ra’ji’un kawai yake nana tawa, wanda hakan yaja hankalin fadan.
Rike kansa yayi dayake wani irin sara masa.
Lokaci daya kuma yafara ganin duhu.
To be continued
Ur’s
z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim
_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )
Wannan shafin nakine nafii nagode da yadda kike nunawa liittafina soyayya
Kodan ke Sai na kara yawan pages ????
Page 19
*
Duk wani tashin hankali, mai martaba yashigeshi. Jin cewa d`ansa mafi soyuya yananan, rayuwa akwai ko babu.
Ganin mai martaba, cikin wannan yanayi yasa akatashi fada Alokacin.
Dakyar mai martaba, Ya tashi ya shige, sha shinsa.
Kunsan yanda zance baya 6uya, barin ma amasarauta, mai girman gaske irin ta kana.
Har yakai kunnan kilishi, alokacin da'akazo Mata da zancen suna tare da intisar da yayanta guda biyu.
Affan Wanda bazaifi kimanin shekara ashirin da biyar ba. Da halima Wanda tayi aure yaranta biyu. Kanwar Affan ce"
Bakaramin tashin hankali suka shiga ba, jin mahaifinsu na wani irin yanayi, wanda gab yake da tashin ciwansa.
Nufan shashinsa sukayi, cikin matsanancin damuwa, basu jira anmusu isoh ba,
"Shiga kawai sukayi"
Nan suka ganshi ya kifa kansa,
Affan ne yanufeshi cikin sauri, yarikoshi,
Abbah meye yafaru???????
Dagowa yayi ya kalleshi,
Muhammadu je kayi mana tanadar mana jirgi zuwa dubai,
Tafiyan Karya wuce nan da awah biyu”
Abba me zamu jeyi dubai??????
Yareemah!!!!! Yareemah!!!!!!! Kawai yake fadi cikin sarkewar harshe.
Abbah"" mai yafaru da yaya yareeman??????
An harbeshi!!!!!
Fadin irin tashin hankalin da suka shiga ma bata bakine.
Dan affan kuka yaringa yi kamar Wata mace.
Intisar da halima kuwa kuka sukeyi kamar Wanda akace yamutu.
Kilishi" ne tayi kafin halin cewa, aibe kamata mutafi mu kadai ba,
Mukira sauran yan uwansa sannan muwuce.
Hakan kuwa akayi cikin Kan kanin lokaci akasanar da sauran 'yan uwansa. cikin awawin da basu wuce hadu ba duka suka hallara. Fadin irin tashin hankalin da suka shiga ma bata hannu wajan typing ne????????,
Sosai suka shiga tashin hankali.
Sai wajan bakwai na dare, kafin jirginsu ya daga. ✈.
================
Anyi iyah bin cike , Dan gwano wayanda suke da hannu awannan aika aikan ankasa, Dan kokadan bbu Wata shaida da zata nuna hakan.
Wannan aikin dole dasa hannun wasu manyan acikinsa, dama daniel yana raye ne to da akwai hanyoyin da zasubi Dan gano wayannan masu laifi.
Amma tun harbin da captain Ahmed ya yi masa, daniel ko shurawa baiyiba ya mutu
Amma a nanan an kara karfafa tsaro da bincike.
Bayan kaman awah biyu da kaishi dakin hutu, wani likita yashiga dan dubashi,
Alokacin kuwa hankalin Ummii yakai kololuwa wajan tashi, dan Har yanzu bawani gamsheshen labari gameda halin da d`anna ta yake ciki.
Likitanne yaje shiga tayi saurin tsareshi, tana tambayarsa yasanar da ita!!! Halin da d`anta yake ciki , Idan ma yamutu ne kawai yasanar da itah"
Mam" d`anki bai mutu ba yana nan araye mana iya bakin kokarinmu na ganin mun ceci rayuwarsa.
Daga Fadin Haka yajuya.
“Yashige dakin”
Turus yaja yatsaya Ganin sa a zaune, kamar ba shine wanda dasu ko numfashi bayayi ba, kallon gefe da gefen dakin yafara yi Dan atuna ninshi ba mutum bane.
“A iya saninsa wannan gubar yakan dauki tsawon lokaci kafin yasake mutum, harya fara gane mutane.
Fita yayi cikin sauri dan kirawo sauran `yan uwansa likitoci, Ganin yanda yafita a gigice yasa hankalin Ummii dasauran sojojin kara tashi.
Ba'a dade ba yadawo da wasu likitocin guda uku abayansa.
Ganin su cikin sauri sun shige dakin yasa Ummii fashewa da wani matsanancin kuka, basu dade da shiga ba _afeeya_ tashigo Wanda ita kebin MG da yaronta zasuje excotion egypt ne tabishi, Sai kuma wannan abun yafaru shiyasa tabar yaron acan tayiyo nan asibitin, cikin tashin hankali.
Farkon isanta sun hanata shiga ne, sanda takira ummi taturo captain Ahmed yashiga da ita!!! Ganin Ummii na kuka ne yasa itama tazauna ta fashe da nata kukan, bame lallashin wani.
Sai wajan 6 :00am mai martaba suka shiga asibitin, lokacin da suka isoh sun wuce gidansu dake nan Dubai "wato gidan Ummii sanda suka biya bashin sallolin da ake binsu, sannan suka nufee hospital din.
Ummii na ganin isowar mai martaba tatashi dasauri taje ta rungumeshi, sannan tafashe ta matsanan cin kuka, tana cewa sun kashe manashi, abinda take nana tawa kenan, bubbuga babanta mai martaba yahau yi, Dan Shima Idan yace zaiyi magana toh tabbas zai’iya yin kukan.
Allah kadai yasan yadda yakeji, sanin dansa dayafiso yana cikin wani hali,
Wani irin bakin ciki ne yatokare zuciyan kilishi jitakeyi kaman ta shakesu.
To be continued
Ur’s
z33yyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim
_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )
Dedicated to
Page 20
*
Isowar mai martaba ne yaje yasamu likitocin, danjin kwakkwaran bayani, aikuma sun samu labari mai dad`i dan an tabbatar musu da cewa Har ya farka, inda mai martaba ya nuna rashin gamsuwa da maganarsu, TV suka jona, nadakin dayake, aka nuno musu tundaga kaishi dakin harzuwa farkawarsa.
Ba’afi awah daya da kwantar dashi, yafarka, harzuwa shigan likitannan, Ya fita yadawo da wasu likitocin suka zo dakyar suka samu, suka masa allurar bacci. Kasancewar maganin bai ratsa jikinsa ba. Kuma alluran da "aka masa jininsa nada karfi yasa basu dad
e suna” aiki ajikinsa ba ya farka.
Gashi kuma, gubar haryanzu bata gama sake jikinsa ba, Kodaa lokacin daya farka bawai yagama sanin “a’inah yake ba.
Wannan labarin ne yasa hankalin danginsa ya kwanta.
Gida suka wuce, Dan mai martaba ya fahimci Ummii tun jiya bbu komai acikin ta.
Dakyar ya lalabata suka bar aaibitin suka nufi gida, affan kadai suka bari acan, duk da intyy taso zama Amma, kilishi dake ranta abace yake tayi kirmushi shi tahanata.
Suna isah gida mai martaba yaja hannun Ummii, Har kofar bandaki yaraka ta yace tashiga tayi wanka, ba gardama ta shiga, dan itama jikinta baya Mata dad`i ahaka.
Bata d`auki tsawon lokaci ba ta futo.
Nan ta samu Har ya had`a Mata tea mai katuro, zama tayi agefen gado, Mika Mata kafin tea d`in yayi nan ma bbu musu ta karba, tafasha sanda takai rabi kafin yadaga Kai, karasa mana yafada Mata, dagowa tayi ta kalleshi, tayi narai narai da idoh, hawaye yacika idon tapp, girgiza Mata Kai yayi, "ya kar6i kofin ya kara Mata abakinta, ba musu takarasa shanye sauran.
Ajiye kofin yayi, sannan yajuyo da ita suna fuskantar juna, magana yafara Mata cikin harshen da tafi ji" Amina kisan cewa wannan abun da yafaru da yaron nan bawai, rashin tsaro kokuma kulawa bane, yasa faruwar hakan.
"A'a Sai dan Haka Allah ya kaddara, karki manta kowani dan adam da tasa kaddarar.
Nisawa yayi sannan yaci gaba da cewa, ai mu abin alfaharinmu ne ace" yaranmu duk duniya Ana alfahari da shi.
Ba'irin taimakon da bayayi kingani kuwa ai addu'ar mutane ma kariya ce agareshi.
A yau akace dannan ya mutu, mu iyayansa zamu zama abin alfahari ga duniya, mun haifi da kuma munbashi ingattaciyar tarbiya, Wanda hakan yasa yatashi da tausayi da kuma taimakon al'ummah aransa.
Haka ya zauna adakin yayita kwantar Mata da hankali.
Ganin sun shiga daki, sun dad`e ne yasa ran kilishi mummunan 6aci, dakyar ta "iya yin break fast tawuce daki, bata bi takan kowa ba.
Koda sukazo komawa asibiti, cewa tayi kanta yana ciwo, sannu suka Mata cikin tausaya wa, sukace afeeyah tazauna kodata bukaci wani Abu, cemusu tayi suje kawai bbu matsala da saketa,
Sai hararan intisar takeyi takasan idoh, akan tazauna, kirmushishi tayi kaman bata ganta ba, dan jitakeyi kamar baza su “isa asibitin taganshi ba,
Haka suka futo, suka dugunzuma Zuwa asibitin.
Satinsu daya acan, MG yasamu lapya, Ya warware, Sai yar rama dayayi, yayi fari dama gashi bbu bambanci da larabawa, Sai yakara yin wani kyau sosai, Wanda yasa intisar kara yin kololuwa acikin soyayyarsa,
Duk wani Abu datasan zatayi yafaranta masa rai takanyishi, Amma ko kallan arziki bata samu daga gareshi.
Inda captain Ahmed ranshi baci yakeyi, irin yanda intisar ke shigewa ogan nasa, yasan akwai Wanda yakeso bayasan wannan kyautatawar da takeyi masa, bayason iyayen oganna shi su canja ra'ayi na jiran lokacin da suka eba masa,
Kuma hakanne tafaru, dan ransu mai martaba da Ummii yana faran tuwa da irin kaunar da take nuna ma dannasu, shikuwa captain Ahmed ya yatqbbata tanayi ne dan riya.
Gashi batada kunya kokadan bata dace da ogan saba, Dan ranan saida yaso marinta.
Kusan watansu daya "a" asibiti kuma acikin satin sukesa ran komawa Nigeria, dan umarnin mai martaba ne hakan, inda su sun dade da komawa.
Affan da intisar ne kawai suka saura da intisar taki yadda tabisu.
MG ne zaune adakinsa, shida captain Ahmed.
Daga idoh yayi ya kalli captain Ahmed, motsa lips dinshi yafarayi wanda sukaci pink harsunfara kaman red, lokacin dana eba yakusan cika kuma bana tunanin za'akara min wani lokacin, captain ahmad tattaro hankalinsa yayi gabaki daya dan yasan yana wuya furta kalmomi musu yawa abakin oganna shi, Har inde kuwa yafara magana mai tsayi to maganar nada mahimmanci.
" Iska ya furzar, tareda shafa sumar kansa ya lumshe idoh, ya cikaba da cewa, ka tabbatar ka kira captain bala ya tabbatar ba'asamu matsala ba.
================
Hanna ce suka fito a lectures, kowa ya gaji likis.
Amira ce ta fara magana ” inbanda jaraba irin na wannan malami ace monday za’afara exam Amma haryanzu yaki gama lectures, hmm ni wallahi nagaji nema, Ina gama exam kano zanbi yar uwata Sai Dan fara IT zandawo, bade tafiya zakiyi ki barni ba????? Amira ta amshe zancen, ahap Sai kuma kiyi, hameeda Wanda duk haushin su yacikata, itaba da karatu ba Sai shan wahaala, taama kasa tanka musu,