BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ahankali tasa gefen gyalenta tamatso kwalla sannan tace mai martaba badai kanaso kagwadamin bani na haifeshiba shiyasa kaki amincewa da kudurina amma kasan yanda nake sansa araina koh yayan dana haifa bana sonsu haka
Kasan yadda nake jinsa araina kuwa tafada cikin muryar kuka inajin ciwo acewae shekara 35 amma haryanxu yagagara yin aure kuma munzuba masa idoh muna kallonsa
Nifa wannan yarinyar daya damu da ita atunanina aljanace ba mutum ba, mai martaba yakura mata ido kawae domin bayaso yatsaida ita saita dasa aya
Sannan taci gabada cewa tayaya xa’ace shekara tara kenan kullum zancensa mutum daya bamusanta bamutaba kallontaba
Mai martaba baza’aduba wannan zance ba idan da’abi shawarata atara malamai kawae suyita masa rokon Allah har adace wannan aljana tarabu dashi
Gyaran murya mai martaba yayi sannan yace bawae naki tatakiba amma yakamata mujira harsai shekatunda ya eba mana suncika kafin muyanke masa hukunci
Ainida ba se anjira ba dan wannan ba mutum bace ga yar uwarsa intisar aisai ahadasu
Kilishi Kilishi Kilishi mai martaba yakira sunanta tareda hadaerai sannan yace
Nafada miki alkawari na dauka zanbarshi yacika wannan lokacinda ya eba donhaka banasan sake jin tashin maganar nan
Toh tace amma bawae dan ranta yasoba sannan tatashi tawuce zuwa shashinta
Tana Fita fadawa sukafara kwasan gaisuwa amma ko kollonsu batayiba tawuce dayake Kilishi Allah yayita mace mai girman kai dakuma nuna isah
================
Zaman cikin gidanne yasoma gagararta domin sai habaice habaice kawae akeyi
Koda Mama taji abinda Su Amma sukeyi hakan baisa tatanka musu ba dan inda sabo tasaba kuma Allah yayita mace mai hakuri wanda gane fushinta abune mai wuya
Juyarda kanta tayi wajan inna kaltu sukacigaba da aikinsu domin yau itace mai girki domin bata taba bari mai aiki tayi ma mijinta abinci itata keyin kayanta
Hanna tashi tayi tayi da niyar shiga daki Hafsat da rabi’ah wanda suke yayu a wajanta ne suka tafa tareda shekewa da dariya Hafsat tace dama wasukam Ai saidai Zaman daki domin ba mashin shini suka kara tafawa yoh saima kunbata bakinkune kewar amma aixaman daki yanxu akaafarashi
Zuruf hanna tashige daki domin itama kanta abunyana damunta wani irin bakin jinine dani tafada tareda fashewa da matsanancin kuka
Amma yau tasamowa kanta amsar tambaya tada dade tana addabarta aranta, aljanine dagaske ya aureta tunda da kunnan ta taji bawani bane yajimata
Toh sukuma wayannnan masu bibiyarata suwaye shin ko suma aljanune??? ta tambayi kanta
Wannan tambayarne haryanxu takasa samun amsar ta kuma batasan wazata nema ya amsa mataba
Saidai takudirta aranta bawanda zaiji wannan zancen
Ai idan aljani yafi karfinta Toh itama akwae wanda zata kai karansu wajan sa
Tadauki alkawarin yin tsayiwar dare tahana idanta barci harsai Allah yamata sakayya da wayannan azzalumai masu BIBIYAR rayuwar ta.
Shin wae waye itah wannan hanna?????
Shikuma wannan wanda iyayansa suke tunanin aljana ta aureshi wayeshi????
To be continue
Ur’s
Z33iiyyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
Bismillahirahmanirrahim
Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)
Page 3
*
DUBAI
Wani tangameman gida nahango, wanda fadin girmansama tsayawa bata bakine, kyawunsa kuwa kokadan baya misaltuwa domin bansan dawani yare zanmuku bayanin da har zakugane kyau tsaruwar wannan gida ba, hatta tsaron gidan ma, sojojine masu tsaran gidan sunza gayeshi , tako wani sako da lungu gaba da baya,
Azatona tunda kasar larabawa ne nadauka sojajin larabawa zangani amma inah zancen yasha bam bam,
Sojojine kala kala wanda kowace kasa sanda suka bada gudumawa wajen kare lafiyar wannan bawa nasa, kowani soja yana sanyene da kakin kasarsu sojojine bila adadin wanda irga yawansuma bamai yiwuwa bane,
Mamaki da alja’abi suncikani waishin waye wannan dan adam dinda ake gadin rayuwarsa haka. ko sucurities dasuke gidan shugaban kasa basukai natsaron wannan bawan Allah yawaba,
MAJOR GENERAL (MG) Abudullahi kukeji daya tamkarda dubu, gwarzon namiji wanda kallonsa kadae ke razana makiyah, ba country dinsa ba kadai
hatta da sauran kasashen sunaji dashi shiyasa suke bada gudumawa wajen kare lafiyarsa, domin shi mai sadaukarwa al’ummah rai da lafiyarsa ne,
Zaune yake kankujerar tangameman falonsa kafanshi daya akan daya ya jingina da kujera karkada kafansa yakeyi ahankali cikin nutsuwah da solon birgewa,
Farineh tass kyakkyawan gaske wanda kana kollonsa dakaga kamanninsa da larabawa dogo neh sambal mai faffadan kirji, gwarzon namiji, subhanallah kyawun wannan bawan Allah, abin ba’acewa komai, saidaai hamdala. idanuwansa farare tass kwayar cikin kuwa bakikirin shape dinsu oval ne masu kyawun gaske, gashin kansa bakine sidik, with his cute pink lips, OMG he’s damn cute, i don’t even knw how to describe him, he’s so muah????
Rurinda wayarsa tadaukane yasashi bude idoh ahankali cikin nutsuwa daukan wayar yayi tareda karata akunnensa.
Amsa sallama yayi sannan yayi hade dayin murmushi subhanallah kyawunsa baisake bayyana ba saida both side na face dinsa suka lotsa (beauty point)
Abin al’jabin baizoba sanda yafara magana da hausa wadda hakan ba karamin abin mamaki bane
Amsawa yayi da toh abba ammafa akwae abinda nakeyi wadda haryanxu bankarasaba yana maganane cikin natsuwa abba ba halin tafowane cewarsa dadahali danazo cikin week dinnan saboda nima nayi kewarka ina bukatar ganinka to
Call u later baejira mai za’aceba kit yakashe wayan
Wata nauyayyar ajiyar zuciya yasauke kokadan bayason abinda zaisa yaje gida yanxu
Danbaxai iya jira lokaci yacika kafin ya cika kudurinsaba yafi masa sauki yajira lokacin kafin yashiga kasarsa tahaihuwa
Karar saukowar takalmintane yakatse masa tunanin dayakeyi
Wata farar matace wacce bazatafi shekaru hamsin da biyar ba kana kallonta ko tantama bbu dakasan itace mahaifiyar MG Abudullahi balarabiyace
Kyakkyawar gaske
Ko banfada ba kunsan yanayin yanda kyawun larabawan Dubai yake
Karasowa tayi dauke da murmushin dake kara fitoda kamanninsu da MG Abudullahi zama tayi kusa dashi tadafa shi sannan tafara magana cikin harshen larabci
Meyake dmunka haka naga gabaki daya yanayinka yachanja lokuta da dama nakan fada maka kacire wata fargaba bbu wata wacce xatasamu miji kamarka tace bataso kanada kyau da mulki da kuma dukiya bbu wata mahalukiayar da zata kika
Shiru yayi nayan wasu dakika sannan yace ummee bana so asoni dankyawu na ko kudi kowani mulki danake tattare dashi
Mutane dayawa bawae sunasona bane wasu tsoro nane yakesawa sununamin so wasu kuma dan dukiya da mulki yasa suke sona bawai har zuciyah ba wani zafaffen huci yafitar yakara damke hannun ummi dayake rike dashi ummee tajawoshi jikinta ahankali tafara shafa kansa batareda tace komaiba
Aranta kuma tanace Allah kasaukakawa wannan bawa naka wannan jarabawar da ya tsinci kanshi aciki tana tausayin danta ace yakamu dasan wanda basumasan ko tana existing ba
================
Yauma kamar kullum shiri tayi tsab nazuwa makaranta doguwar rigane ajikinta ta yane kanta da gyalen rigar wadda hakan yafito da sihirtaccen kyawunta wanda ba lokaci daya kake kollonta kagano wannan kyawunba
Jakarta ta zara direct dakin babansu tanufa dasallama tashiga sanda ya amsa sannan tashiga tagaisheshi ya amsa da fara’arsa kinfuto kenen eh baba yanxu zanwuce dari biyar yaciro yabata godiya tayi masa sannan tatashi yafibata dakyakkyawar addu’a wadda yakamata duk wani mahaifi yayiwa diyarsa lokacin da zataje wani waje nadaban