BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Najeeb an sallameshi a asibiti jikinsa yad'anyi sauki saidai damuwace fall arayinsa danko abinci baya iyacii balle magana," 

Iya tambayoyin duniyarnan ammasa amma bbu amsa duk ‘yan uwansa hankalinsu yatashi ganin halinda d’an uwansu yake. “
Koda yayansa yakira anty maman amal Bata fad’a masa tasan komai ba saidai tad’an canja muryarta bakaman yadda yasaba jiba sai yabar hakan a hidimar biki.”

Washe gari da safe ko karyawa basuyiba hanna tasa labba dole sanda takaita gida. “
Ahaka tatashi takaita,”
Ummii na falo taga shigowar labba, “
Cikin gajiya tazube akan kujera,”
Ummii ne tace habibty daga ina haka da sassafennan? “
Wallhy ummii hanna ce tace saina kaita gida wai zataje tasha magani batajin dad’ii,”
Cikin nuna kulawa da damuwa ummii tace Allah yasauwake, “
Ameen ta amsa atakaice.”

K’arfe uku suka fara shirin yin bud’ar kai wanda za’ayishi acikin fada. “
Saikusan 4pm kafin akagama shiryawa,”
Alokacin hanna tadade da isowa Bata wani dad’e awajenba da damu labba tatashi tarakata wajan moddibbo, “
Ba su d’auko lokaciba suka dawo dayake addu’oii kawai suka kar6o,”
Sannan suka juyo. “
Sunsamu angama kawai suka wuce gida hardasu amira,” wanda gobe zasu koma, “
Labba ne tasamu ummii adaki akan sallaya ta idarda sallah.”
Sannu ummii, “
Yawwa Sannu inakika shiga?”
Naraka hanna kun moddibbo ne, “
Murmushin tayi danko sunan hanna aka ambata takanji son yarinyar aranta.”
Yanzu wajen mai martaba zanje naji zancen yanda suka tsaya akan zancen jiya sunje tambaya, toh tunjiya bamu samu dama munyi zancen canba shiysa yanzu zanje, “
Murmushin fuskar labba ne yafad’ad’a, Allah yasa andace amin tace.”
Sannan tamike tayi shashin mai martaba afalo tasamu mai martaba. “
Cikin fara’a da girmamawa tagaidashi,”
Cikin tsolaya tace nabiyo sawu ne, dariya mai martaba yayi sannan yace ohh uwar yaro ba hakuri anaso aji yanda zance yakaya.”Murmushin tayi sannan tace bakasan yanda yaronnan yake zuwa yazaunamin ba Koda bai furta ba amma nagane nufin shi. “
To ai muntsaida zance da iyayen yarinyar amma munaso yaran su dai-daita kansu yanda abun zaizo Cikin sauki.”
To Allah yasanya alkairi aciki da amin ya amsa Suna Cikin zancen saiga MG yashigo da sallama amsawa sukayi sanna yasamu wajen yazauna gaidasu yayi suka amsa masa. “
Zama yayi nan mai martaba ya labarta masa yanda sukayi da mahaifan yarinyar.”
Wani irin fad’uwa gabansa yayi danshi yana shakkar tunkararta baisan mai zaifaru ba. “
Murmushin ya kakalo sannan yamusu sallama da godiya yafita.”
ya yanke shawarar jibi ya tunkareta dan yasan rana mai mahimmamci ne arayuwarta. “
Da safe su amira da mama suka fara shiri jitaayi duk garin bbu dad’ii daga ita har hameedan, dan da tafiyar da hanna za’ayi amma tafasa batason abinda zai had’ata da Najeeb kokadan kuma tasan har inde tatafi zasu iya had’uwa.”
Babe yanzu jibi nefa birthday d’ina wednesday amma bazaki zauna ba? “
Srry Beb wallhy mom ce tatakura Nima banso komawaba,”
Badan ransu yasoba su kayi sallama su amira suka tafi, kuma duka bakin sun watse sai d’ai-d’aiku. “
Haka sukaji wani irii bbu amira arannan sunyi bacci sosai, wanda tunda akafara bikin basu sameshiba,”
Washegari sukaje sukayi odering duk wani abunda zasu buk’atq gobe. “

To be continued

Ur’s
Z33yb3rw3r
[12/2, 9:31 AM] Anty Jamila D Ili: BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim

_
Writting by

© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )

My first novel

Page 39

*
Bata nufi ko ina ba sai garden tazauna akan resting chairs, sai kuka takeyi, kamar wanda danshi aka aikota duniya. “

Ganin yanda take yasa moddibbo nufan wajen, tsayawa yayi ya gama nazari akanta, dafa kanta yayi, daogowa tayi takalleshi farine soll tsoho mai farin gemu yanada tsayi madaidaicii," 

Sunkuyarda kanta tayi dan wani irin kwarjini yamata, “sunkuyawa yayi ya zauna da nishi alamun tsufa ta kamashi,”
Cikin sigar kwantarda hankali yafara magana irinnasu na dattawa,”
Jikata nasan kina Cikin damuwa amma kisani kuka ba shine mafita ba. “
Akullum ki yawaita addu’a shine maslahar damuwarki, sunkuyarda kai tayi ta cigaba da wasa da yatsunta,”
Murmushi irinnasu na manya yayi sannan ya cigaba da cewa, mai nene dalilin da zaisa iyayenki su za6a miki miji amma ki bijre musu? “
Sunkuyarda kai tayi hawaye d’aya nabin d’aya sai yanzu take danasanin maganganun data fad’a musu kuma agaban wa’yanda sukazo neman auranta.”
Baijira amsarta ba yaci gaba da cewa, “
Kinsan cewa bbu wanda yake da mahimmanci a rayuwa irin mahaifa, kikasance Akullum mai san faranta musu,” girgiza kanta tafarayi hawaye d’aya nabin d’aya, ” ahankali ta furta ba haka bane,”
Toh menene Jikata?”
Yatambaya Cikin sigar lallashi, “
Girgiza masa kai tayi, Murmushi yayi dan tabbas yasan akwai abunda take boyewa.”

To kifad’amun dalili har inde bakyaso nazargeki akan kin yiwa mahaifanki biyayya, ” bansan cutarda wanda yake tareda nine ko kadan banso wani yasake cutuwa kamar yadda najeeb yacutu,”
K’ura mata ido yayi nasan gaskanta abinda yake tinani,”
Cikin hikqma yace kidaukeni matsayin kakanki, danni nadaukeki ajikata kifada mun duk wani abinda yake faruwa da rayuwar ki karki boyemun komai, in sha Allah tare zamu nemo mafita, “
Cikin yarda da tsohon tafara bashi labarin duk wani abinda yafaru har izuwa kwanciyar najeeb a asibiti, dogon numfashi yaja sannan yace mata, jikita tunda naganki nasan kina tareda sihiri ajkin ki saidai baida k’arfii dan atunanina yawan addu’a da kike ya ne yasa abin baiyi karfii ba amma in sha Allahu da addu’a zamu yakesu bbu wani abinda yafi karfin addu’a, ” mutane musani bawai dan kinada damuwa sai jitafi wajen wani yace zai miki aiki awarware sihiri shine masalaha ba A’a akwai addu’oii dayawa acikin qur’anii mai girma wanda su kadai sukan iya samawa dan adam waraka dan Allah mukiyaye zuwa gun wasu malaman yawancinsu bokayene suke k’arya dasunan malamai Allah yakare

Nasiha yamata sosai sannan yace ga addu’a kiringa karanta ta kartabace abakinki da yardar Allah duk wani mai nufan ki da sharri zai koma kamsa waraddal lahul lazina kafaruh bigaizihim lam yanalu khaira wakafal lahul mu'umininal qital wakanal laahu qawuyan azizan hakima
Wannan addu’a hakika tana maganin sharri dakuma mai nufinka da sharri ahaka yayita mata nasiha sannan yace taje tasamu mahaifanta tabasu hakuri, “
Jikata d’agowa tayi tayi kalleshi, gobe kizo gidana ki kar6i sauran addu’oiin, sannan zansa ayita saukan alqur’anii,”
Sannan abu na karshe bawai danna fito a dangin abadallah ba yakasance yaro mai hankali, duk duniya banda mahaifanki banga wanda zaisoki sama dashi ba, “
Yasoki tun baki mallaki hankalin kankii ba, yasokii tun bakisan kankii ba inatunanin duk wanda zaki aura abayansa yake amma inaso kiyita addu’an zabin alkhairii,”
Allah ya miki albarka amin ta amsa d’an hira suka ta6a sannan yatshi har bakin kofan tarakashi dake yatsufa ahankali yake tafiya sanda suka isah bakin falon taja tatsaya alamu yamata akan tashiga bbu musu tashigo shima yabi bayanta abakin kofa tatsaya ta durqusa guiwaowainta duka biyu sannan ta sunkuyarda kanta, “
Cikin rawar murya ta ce abba dan Allah kuyafemun nayi kuskure amma in sha Allah bazankara maimaita kamarsaba.”
Mai martaba ne yayi magana wanda dama tun maganarta tafarko Bata 6ata masa raiba yasan dole da dalili, gashi yanzu yanda tatsuguna tana neman afuwarsu yasa yarinyar k’ara shiga aransa, Cikin sigar gamsuwa yace tashi kice d’iyata baki mana laipyn komai ba Allah yamiki albarka ahankali ta amsa sannan tatshi sum sum tafice, ” mai martaba suka fito sun tsaida zancen su na iyaye kowa ya amince amma sunaso yaran su dai-dai ta kansu, godiya mai martaba yayita musu Ganin haka yakarasa suka tabbatar lallai wannan al’amari nada mahimmancii.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button