BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Can wajen su umma kuwa sunanan suna shiri iya dai-dai gwargwado sunyi k’okari sosai wajan tanadarwa da baki abun buk’ata. “
Alokacinne anty maman amal tace ashirya hanna dan tasan dangin sarauta yanzu haka da mata za’azo kuma zasu bukqcii ganinta,”
Governor na garin bauchi kuwa yasha mamakin ganin cewa MG yasauka agarinsa batare da yasani ba, “
Amma yanzu ankirashi akan cewa jirgin mai martaba yakusa sauka,”
Hakama yakira abokinsa sarkin bauchi yasanar dashi. “
Aikuwa nan ma aka fara shirin tar6an sa.”
Duk ilahiran masu tarban sarkii sun hallara a airpot na Abubakar tafawa balewa.”
Kafin su taso daga kano kuwa sanda zance yakai kunnen fulani kakar MG bakaramin farin ciki tayiba, “
Tunda tajii zancen zuwa tace ai atafar sai anje da ita zataje taga jikanta.”
Dake tana samun kulawa sosai kuma ga kud’ii yasa tsufanta baiyi yawa sosai ba. “
Aikuwa hakanne tafaru aka shirya hadda gwaggonsu khadija k’anwarsu mai martaba da sauran ‘yan uwah zuwa garin bauchin yakubu.”
K’arfe 12 :00 dai-dai jirginsu yasauka a airpot, “
Kai tsaye fada suka wuce,”
Basu d’auki lokacii ba akayi gidan su hanna, “
Alokacin angama shirye komai dan, har Abokan baba samada biyar sun zo tar6an baki da kuma wasu dattijai,”
Yan anguwarsu duk aka had’u, “
Isowarsu ba jama’ar anguwar ba kad’ai har makwabtan anguwar fitowa sukayi dan ganin wa’yannan mutane ak’ofar gidan da suka sauka ne yasa mutane shan mamaki basu k’ara sarewa ba sanda sukaga har Governor awannna tafiyar.”
Da fara’a su Abba da sauran dajjijan nan suka fito suka tar6e su Cikin amince, “
Suka wuce falon Abba dasu,”
Su kuma matan Cikin gida suka wuce aka wuce shashin mama dasu,”
Ammah ta window take leqe yayinda wani irin bakin ciki yacika ta har wani dushu dushu take kallo. “
Data sani takeyi marar adadi dabata rabata da najeeb ba da tabarta dashi akan ace ta auri wannan dan banzan mai kud’in.” abin bakin ciki ma yanda algaitu ya ciki anguwar tako ina algaita ansan dangin sarauta sun shigo, “gaba ki d’aya anguwar sai ta d’auki kamshii dan duk yanda suka wuce akwai masu bin wajan da turaren wuta na gaushi. haka al’adinsu yake har indai za’aje neman aure a gidan sarauta to anguwar sai tasan da zuwansu.”
Jiri ne yafara ebanta Aikuwa awajan ta sulale ak’asa Batasan yanda takeba. “
Gashi hafsat tatafii makarnat rabi’ah kuma tana gidan anty maryam jiya da tazo tare suka tafii.”
D’aki aka shiga nan akafara gaigaisawa Cikin mutumta juna.”
Nan da nan bada 6ata lokacii ba suka fara abinda yakawosu lokacin an kawo musu kayan motsa baki, “
Alokacin Momy kadija kanwar Abba tatashi tafita sai gata tashigo da dogarawa har guda goma sha biyu kowa da akwatii ahannunsa yashigo dashi ajiyewa sukayi sunayi suna kirari a matar yareema ahaka suka gama suka fice da baya-baya,”
Kallon kayan suka tsyayi nan aka musu bayanin kan cewa kayan naganii inaso ne. “
Nan mama tace ai atafar kayan sunyi yawa saidai arage,”
Fulanii ce tace ai matar yareema ta cancanchi fiyeda haka dan haka k’arna k’ara jin wannan abun ai muma yar muce. “
Ahaka sukayi ta hira kamar da ansaba da juna.”
Fulani ce tace aishin zaku kawomin kishyata naganta ne kosai nabi duk dakunan ina bincikawa, “
Dariya dukansu sukasa Momy khadija ne tace wa Fulanii,”
Umma wannan kishiyarde ta tsorataki tun daga jinta kika rikice gabaki d’aya saikin ganta. “
Dariya duka d’akin ak’asa sannan Fulanii tace to ba dolena naji kishi ba,”
Tanason kwacemun wannan had’adden miji wanda ni kad’ai keda irinsa. “
Nanma dariya akayi sosai, sannan anty mmn amal tatashi tashiga d’aya daga Cikin d’akunan,”
Can jimawa tafito hannunta riqeda hanna kanta rufe da qyale amma fuskanta abud’e yake kanta yana k’asa, “
Tundaga nesa suke kallonta suna masha Allah,”
Dan hanna tayi kyau sosai.”
Zuwa tayi ta zauna acan d’an nesa dasu tafara gidansu ahankali Cikin fara’a suka amshe yayinda Momy khadija taja hannunta zuwa gabanta, “
Tsugunawa tayi ta rungumeta sannan tace welcome to our family dear,”
Hakan kuwa ba karamin dad’ii yayiwa su mama da umma ba sunsan sunakai ‘yarsu yanda ake sonta Ahaka kowacce mata tayita rungumeta Cikin farin ciki. “
Daga k’ arshe fulani tariqeta gam kamar za’a kwaceta tana cewa aikwa bari mu gaisa ko,”
Aikuwa hanna taji dad’ii janta datayi yisukeyi kamar zasu cinyeta dan kowanne acikinsu murna sukeyi sunga matar yareema pics kam alokacin tasha bbu adadii. “
Fulani kam riqeta tayi gam tana cewa Allah yamiki albarka,”
Allah yamiki albarka, abunda take nana tawa kenan hannunta na riqe dana hanna duka biyun wanda hakan sanda yayi sanadiyar da yasa hanna zubda hawaye. “
Data tuna lokacin da ko mashinshini bata da shi har abin gorii yazama sai gashi waiyau itane Cikin dangin mujinda zata aura suna sonta kamar su halaka.”
Fulani ne talura da hawayen ahankali tasa gefen gyalenta ta share mata bata bari kowa yaganii ba ta Girgiza mata kai ko ba’a fad’a ba tasan kukan farin ciki takeyi. “
Dan duk wani labarinta moddibbo yasanr da fulani shi yasa takejin son yarinyarda tausayinta.” Maza kuwa suma awajensu sungama yanke shawarar za’ayi aure nan da wata d’aya da satii biyu. “
Ahaka Cikin farin ciki aka gama komai kowa sai yaba halin kowa yakeyi dan daga wajen kowa anga halin karamcii,” Daga mata aka futo da huhun goro da caton na mint da dabino, kowane gida abinda ake kaimusu kenan, “
Duk anguwar bbu gidanda baisamu huhun goro da caton d’in mint dana dabino ba kuma,”
Kuma ko ina idan aka shiga sai an shaida musu cewa na neman auren hanna ne, “
Duk gidanda aka shiga sai anyi mamaki dan tunda suke sunsan ba’at6a sallama ta cewa anzo wajen hanna ba sai gashi yau dogarawa ne ke raba goronta kuma wai hakanma goronda za’akai na neman auren wata shine ake rabashi kowane gida,”
Bayan angama komai suka fito sukasa akira musu matan su tafii. “
Nan wani bafade yashiga yasanar dasu da suka taso tafiyane fulani ta bud’e gyalen hannata cusa mata wani d’an karamin akwai sannan aka fita rakasu.”
Bqyan sun tafii ne ya auwal yayi waya ya shaida musu tun jiya adda hindu ta haihu, ta haifa d’anta namiji wanda tun jiya yaki fada ne dan bayaso yaraba musu hankali. “
To be continued
Ur’s
Z33yyb3rw3r
[9/24, 8:45 AM] +234 810 367 2210: BIBIYATA AKEYI
_
Bismillahirahmanirrahim
_
Writting by
© zaynab bawa
( z33yyb3rw3r )
Alhamdulillahi am feelling much better,”
Thank u all for d du’a, care. Massages, luv.”
Luv u all ❤. “
Page 48
*
Murnane ya 6arke agidan, ga murnar auran hanna ga kuma na haihuwar adda hindu.”
Basu tsaya jan lokacii ba aka shaida masa akan ana sallamarsu su wuce bauchi. “
Dan ga baki d’aya yanzu zaman su zaifii yawa a bauchi tunda shirye shiryen biki za’a fara duk da da d’an sauran lokacii amma kuma yakamata komai afara tanadinsa da wuri.”
Awashe gari kuma abba zai wuce kano,” domin aikinsa. “
Umma kuma sai anyi suna zata koma.”
Da yamma su adda hindu suka kamo hanya itada yaya auwal, “
Alokacin da su abba sukaji bakaramin fad’a sukayiwa su umma ba.”
Abba ne yana fad’a yana cewa inbanda shashanci yarinya da d’anyan jego zaku d’aukota kuma jegon farko ko wanka bata samu ba. “
Fad’a sosai abba da baba sukayi,”
Hakuri kawai suke bayarwa dan suma yanzu sun fara danasanin cewa suzo da sukayi ga gari da nisa tsakani tafiyar samada 3hour. “