BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

K’arfe shida dai-dai hafsa ta dawo daga makaranta,”
Ganin mutane cin cirindo acikin gidansu suna fitowa daga shashin mama. “
D’akin ammah tawuce nan tasamu ammah afalo a sume da gudu takarasa tana fad’in ammah, ammah, jijjagata tafarayi ganin bata ko motsi yasa tanufi fridge da gudu ta ebo ruwa ta fara yayyafa mata.”
Koda ta yayyafa mata wata nauyayyan ajiyar zuciya tasake, “
Can kuma kamar wanda aka zabureta ta mike tana cewa na shiga uku wallhy boka ka cuceni daka bar yarinyar nan zatayi aure kuma dan gidan sarki Allah ya’isa tsakanina dakai.”
Nan tayi shiru tafara dube dube afalon nan idonta yadauka kan hafsat da take binta da kallon tuhuma. “
Mai Mai ta kalmar tayi tace boka,” boka fa kikace ammah? tana magana kuka na k’okarin kwace mata, “
Ammah dama kina zuwa wajen boka dan ya cutar min da ‘yar uwa?”
Cikin in ina ammah tace um um malami nefa fa, “
Cikin kuka da tsawa hafsa tace ina bambamci ammah har indai zakije wajan wani da sunan ya cutar da d’an uwanka wallhy bokane ba malami ba,” Cikin kuka tahad’e hannuwanta biyu???? ammah na rokeku kudena 6atawa malamai suna idan zaku kirqsu da bokansu yafi, d’an jan numfashi tayi sannan taci gaba da cewa, “
Ammah nifa hanna bawai bana sonta bane karkiyi tunanin bazanji zafin cutarda ita da kikayi ba wallhy ammah dole sai naji zafi dan ‘yar uwa tace,”
Hasalima abinda yasa nakejin haushinta irin yanda baba yake nuna bambamci atsakanine, bayaga haka bbu komai soyayyarta nanan dan k’are azuciyata.”
*(gaskiya iyaye yakamata mu kula duk irin soyayya dake tsakanin yara har indai zaka nuna kafison d’aya ko kuma kafi kula da d’aya to jin haushin ‘yan uwa zaishiga tsakani dan Allah iyayenmu akiyaye.” nuna bambamci d mahaifin *hanna* yakeyi tsakani shiyakawo jin haushi tsakaninsu amma bawai dan’ d’aya baison d’aya ba dan Allah zank’ara roqon iyayenmu akan mukiyaye hakan idan yayi tsananin har gaba yake haifarwa tsakanin ‘yan Uwa)
Jikin ammah ne yayi sanyi, wani irin nauyin d’iyarta ne ya rufe ta, “
Yarda tahaifa itace ke gaya mata gaskiya.”
Duk ilahirin gidan na tsaye abakin k’ofar ammah duk jikinsu yayi sanyi jin abinda yafaru,”
Shiga ciki sukayi nan idanuwan ammah yafara zuru-zuru kamar wanda tayi k’arya kodayake ai abinda tayi yafii k’arya. “
Kowanne yasamu wajen yazauna abinda su ammah basu saniba shine tun farkon fara maganar suke tsaye,”
Dan zuwa hafsa ganin mahaifiyarta akwance saita sakee k’ara wanda itakanta batasan lokacinda tayiba hakan yayi sanadiyar janyo hankalin gidan, “
Sun zo shiga sukaji abunda ammah ke fad’a wanda sunada tabbacin idan ta sun shiga bazasuji komai ba yasasu tsayawa.”
Kuka sosai ammah takeyi takasa cewa komai.”
Babane yayi gyaran murya, sannan ya kalli hafsa da kanta ke sunkuye ga baki d’aya kunyar kowa ya rufe ta yace. ” Kiyi hakuri d’iyata nasan nayi kuskurenda mafi akasarin iyaye suke aikatawa, “
Ki yafeni bawai dan nafison hanna bane yasa haka,”
Dukanku ina sonku kuma ‘ya’ ya nane kuma inasonku dan haka Kiyi hakuri kicire komai aranki hakan bazata sake faruwa ba da ikon Allah. “
Cikin muryar kuka tace babana na yafe maka, dukda nima nasan irin biyayyar da hanna take maka nima bana maka amma in sha Allah daga yanzu zakazaka sameni me yimaka biyayya.”
Allah yamuku albarka baki d’aya aka amsa da amin. “
Sannan yajuya da kallonsa wajen Ammah yace kin kyautawa rayuwarki,”
Kin cutarda ‘yarki Wallhy nayi danasanin aurenki Allah ya wadai irin halinki hak’ika wannan magana tayiwa hafasat zafii amma kuma, Ammah ita tajawa kanta. “
Sunkuyarda kai tayi Sannan tace dan Allah kuyafeni wallhy son zuciyane yajamin haka,”
Nayi danasani wannan rayuwa da nad’aukarwa kaina, “
Wai yau yar cikane takemun nasiha ita take gwadamun abunda nakeyi ba dai-dai bane,”
Wayyo Allah na kaicona. “
Dan Allah kutaimaka ku naima mun gafarar hanna bansan dawani ido zan kalleta ba na cutarda ita tuntana jaririya,”
Wallhy har kunyar kallonta nakeyi. “
Jikin mama ne yayi sanyi tabbas tasan care Ammah ta shiryu dan ita tazauna da ita na kimainin shekaru ashirin da biyar 25 kuma tasan halinta tasan tunda tafara neman gafara to tabbas ta shiryu.”
Dan tunda suke ko yi hakuri bata ta6a ji dai-dai da baba ta ta6a cewa ba. “
Babane yace gafarar hanna zaki nema dan ita kika cutar,”
Juyawa tayi gun hanna gwuiwo winta azube ak’asa tana neman gafarar ta, tana cewa hanna nasan na cutar da ke iyakacin cutarwa kiyafeni hanna hatta saurayinki da kuka rabu kwanakii ma nice silar rabuwarku ni nasayarda komai na mallaka na rabaku kinga Allah ya nunamin ikon sa kinga irin mijin daya baki. “
Kukane ya kufcewa hanna jin cewa rabata da najeeb akayi har yanzu sonsa bai ragu kokad’an azuciyar taba kuma haryanzu ko d’igon son MG bata fara jiba.”

Tashi tayi aguje tabar dakin, wani irin tausayin kanta da najeeb ne yarufeta. “
Kuka tayi iyakar iyawarta dan yanzu abin yadawo mata sabo fill.”
Dakyar umma ta lallasheta tayi sallah, Sannan tashiga tad’aurawa su adda hindu abinda zata samu sucii irin wanda akeso masu jego su sha. “
Tana zaune ita kad’ai ad’aki hafsat ta shigo, zama tasamu waje tayi Sannan tace hanna wato bazaki yafewa mahaifiyata bako,”
Nasan tayi laipy amma yakamata ki yafe mata. “
Ta nemi gafarki fa.”
Ce miki akayi ban yafe mata ba.”
Kin yafe mata ne amma baki gaya mata ba kinsan haryanzu kuka takeyi taki sauraron kowa gani takeyi in baki yafe mata ba, zata shiga wani hali,”
Nisawa tayi Sannan tak’ara cewa hanna kinsan yanda d’iya da mahaifiya suke duk laipynda ta aikata bazanso ganinta Cikin tashin hankali ba,”
Hanna plz kiyafe mata, “
Hameeda Ce tace hanna plz let d bygone be bygone.”
No family is perfect we argue and fight, sometimes we stop talking to each other but hanna family is family, luv will alway’s be there. “
Ganin sunason damunta kawai tafuce tabar masu d’akin basu bitava suka zauna ad’akin itada Hameeda.”
Tana futa taga bbu kowa zuruf tashige d’akin Ammah kamar mai tsoron karwani yaganta, “
Azaune tasamu Ammah nata rusar kuka kamar ranta zai fita har wani dushi dushi take kallo,”
Zuwa hanna tayi tazauna agabanta Sannan tasa hannu tashare mata hawaye, “
D’agowa tayi tace hanna sa hannu tayi ala66anta tace shiiiishshsh Ammah kidena kuka na yafe miki Allah yayafe mana baki d”aya.”
Cikin kuka tace hanna nagode, nagode Allah yamiki albarka, “
Amin hanna ta amsa Sannan tace Ammah dan Allah kimin alk’awarin bazaki sake cutarda niba,”
Kar sai na saki jiki dake ki k’ara cutarda ni. “
Ammah bama niba ko wani dan Allah karki k’ ara cutarda wani,”
Girgiza kai Ammah tafayi kuka nak’ara k’ok’arin kwace mata tace hanna ki yarda dani na gyara halina wallhy yanzu ko kwaro bana iyajii zan cutar balle kuma d’an adam.”
Jijjiga kai hanna tayi Sannan tace Ammah ciki abinci dan nasan rabonki da abinci tun da safe, “
Murmushi Ammah tayi tanajin son hanna nashiga zuciyarta,”
To ‘yata jeki kawo mana abincin sai muci tare nasan kema bawai kinci bane dariya hanna tayi Sannan tace nikam Ammah complex zansha wollah bazanci tuwo ba. “
Ammah ne tamiqe tace mukam ai saida tuwo, bari kiga nashiga ne eba inyaso sai kishiga ciki akwai complex d’in .” K’arfe tara dai-dai su adda hindu suka isoh gabaki d’aya ta shigata, “
Jin tsayuwar mota yasa hanna dake d’akin Ammah mikewa tace su adda hindu sun iso,”
Ammah ne takalleta tace dama tana hanya ne, “
Eh Ammah yau ta haihu tafad’a ta zumud’i,”
Haihuwa shine dan rashin hankali zasu kamo hanya. “
Fita duka sukayi daga bakin hanya Ammah taga duk sunyi laushi daga ita har jaririn,”
Aikuwa nan tajasu sukayi shashinta batareda su mama sunsan da zuwansu na, “
Bata zauna ba ta kunna heater na toilet d’in tashiga yiwa adda hindu wanka,”
Sanda tagasata sosai sannan ta koma kan jaririn shima ta wankeshi tass ta nad’eshi. “
Dama kafin ta Fito hanna tahad’a mata tea mai kaurin gaske nan danan ta shanye ita kuma hanna tayi shashin mama tad’auko farfesunda tayi mata da kawo sata agaba Ammah tayi Sanda taci tasha romo sannan ta kawo mata tuwo dkyar taci tuwon tukunna tasamu k’arfin jikinta, “
Ammah ce tace ta kwanta kafin nan Aikuwa tana kwanciya bacci yayi gaba da ita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button