BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuba masa abincinda tafarayi ne yadawo dashi daga tunanin daya wulla, zuba masa tagamayi sannan takoma kan amal itama tazuba nata tazauna,

===============

Inah mukabar masu bibiyan hanna ne tun fitarta daga gida suka fara binta har tashiga lectures tafito, fitarta daga lecture zuwa shop duk lokacin suna bib bibiyarta Bayan takarasa shop ne daya daga cikinsu fitsari ya mugun kamashi, dama kunsan ance tsautsayi baya wuce ranarsa domin oppotunity come at onces just like mistake come at onces either dakadauki tsaawon shekaru kana kare abu but na lokaci guda kayi sake da wannan kariyar wannan mistake din da za’asamu ayan secound itx really hard to make it up,

Fitsarine sosai yarikeshi wanda bazai iya jiraba gawajen wajen wucewar jama’a balle yayi awajan, yabukaci dayan dayakai shi yayi aiba wata damuwa tunda akwae mutane ashop tun har dasu dawo kafin asallameta,

Rakashi yayi kafin sudawo abinda suke gudu ya auku wandasu basuda masaniya akan faruwar hakanma domin alokacin najeeb yabige hanna haryaji zuciyarsa takamu da sanda, itama hakanne tafaru awajanta luv at first side,

Dawowarsu yayi daidai da fitowarta daga shop din, nan sukaci gaba da binta, wanda saken dasukayi nayan wannan minute din yana daidai darasa rayuwarsu,

Harzuwa lokacin da tajuya me keke napep zuwa gidan antynta harnan suna biye da ita sanda tazo gidanne ta shiga sukuma sukayi parking car dinsu, sunajiran fitanta,

Koda lokacin da najeeb yashigo tareda yaya mahmood yazo wanda yaje hargida yadaukeshi kuma sunriga da sunsan motar yaya mahmood kuma sunsan matsayinsa a wajanta so basu damu daduba motarshi ba koda wani acikinta dake motan nada bakin tinted,

Haka yayita kallon ta harsuka karasa cin abuncin, anty amma kin iya abinci wallahi nima Allah ya bani wacce ta iya girki yafadi haka tareda satan kallanta ta kasan idoh, to Ai baninayi ba cikin zumudi yace wayayi gata Zaune kusa dakai, hmmm yaja gauron numfashi anty amma mijinta yayi sa’a sainaji dama nine wannan mai sa’ar,

Siririn tsaki taja kaifa kafara wuce gona da iri ha’ah ta murguda masa baki, wow???? gaskiya fushi yana miki kyau kamar karkiyi dariya,hakan dayafada ne yasata murmusawa wow to Ai kuma dariyan yafi miki kyau kainama kasa tantancewa

Ahaka yayita jan ta da kalamai masu dadin sauraro harta bashi phone number dinta,
Saida tayi la’asar kafin tafara shirin tafiya,
Bayanda bayiba akan yasauketa agidah amma fir taki,
Haka sukayi sallama da anty kafin tafuto da niyyar wucewa gida batayi mamakin ganin motarsu,
Sanda tayi dan tafiya kafin tasamu abin hawa gida tawuce,

         DUBAI 

Major general MG Abudullahi ne Zaune a office gabaki daya tunda karfe 11:30 tabuga a agogon nigeria wadda yayi daidai da 2:30 a agogon akasar dubai wani irin faduwa gabansa keyi kuma yarasa dalili tunyana daurewa avun har zazzabi yake shirin sa masa ba shiri yabaro office yayi gida amma duk da haka yakasa samun nutsuwa kamar wanda wani mummunan lamari ke shirin faruwa dashi,
Captain ahmad yafada cikin dagun murya cikin tsafin nama wani dan saurayi wanda bazaifi kimanin shekaru 30 ba ya isoh wajen cikin girmamawa yace Gani yallabai yisauri kakiramin Captain bala jiki harayana bari yaciro waya a aljihunsa dan yasan halin ogannasa bayasan wasa barinma daya fahimci ransa yana bace, ringing daya akadauki wZ33iiyyb3rw3rikawa MG wayan yayi ya karba tareda karawa a kunnensa…..

To be continue

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
Zaynab Bawa (Z33iiyyb3rw3r)

This Page is sincrely dedicated to u My dear Ayeshert Aly garkuwa u r such a wonderfull person i want u to know that u r _amazing so much love u

Page 7

*_

Saurin karban wayan yayi tareda karawa a kunnensa, yafara, magana duk da bawae jin maiyake cewa nayiba amma nafahinci yanayin sa yasauya dan damuwar da take fustarsa ta sassauta, duk da dama bawae yakasance mutum mai fara’a bane amma akan iya gane lokacin dayake cikin bacin rai,

Sauke wayan yayi daga kunnensa tare da sauke wata nauyayyar ajiyan zuciya
Bawae dan yagama yadda da abinda Captain bala yace bane, amma hankalinsa yadan kwanta, domin yasamu sassauci daga yanda zuciyar sa ke bugawa,

Mikewa yayi akujerar dayake Zaune, ya lumshe idanuwansa, abubuwa kala kala yake sakawa acikin zuciyarsa

================
Bata isah gida ba sai karfe biyar na yamma, tura dan karamin kofar dake jikin gate din gidansu tayi tashiga da sallama duk da tasan bakowane awajan dazai amsaba amma yanada kyau shiga gida da sallama,

Cikin gidan tawuce kaitsaye, tasamu ammah zaune tana yanke, farcen kafanta, sannu da gida ammah tafada koda batasa ran amsawaba, amma dabi’ar tane koh bazata amsaba saita gaishe ta,

Idontane yakai kan kayan dake jikinta, ke zonan tayi saurin kwala mata kira, yitayi kamar batajiba dan idan zaka shekara kana ce mata ke bazata amsaba,

Sanin halinta ne yasa tayi saurin cewa hanna badake nakeyiba juyowa tayi au banji lokacin bane, Wani kululun bakin ciki ne yatokareta, aranta tanacewa yarinya batasan komai ba sai rashin kunya, afili kuma tace A’inah kikasamu wannan kayan jikinki ?????

Kallon gefe da gefenta tayi sannan tadago tace wanne???

ungo naki wannan najikinki mana to aini banga wani kaya ajikina ba nawane, oh namanta ashe ance idan mutum yafara tsufa yanada saurin mantuwa,

Tana fadin haka tayi saurin juyawa, dantasan abinda ta aikata don kokadan ammah batasan tsufa, Saurin shigewa sashin mama tayi tabar Ammah nata surfa ashar,

Shigewa tayi tana dariya afalo tatararda mama Zaune tana kollon wisal hausa, kewani irin shashancine haka zaki shigowa mutane daki babu sallama kamar wata tababbiya, turo vakinta tayi mana nayi sallama fa bakiji bane, kyaji dashi dai tafada tareda juyawa taci gaba da kallonta,

Wucewa tajeyi mama tayi saurin tareda keh A’inah kikasamu wannan kayan kuma, mama gidan anty na’ilah fah naje, shine kika samata kaya kaimama me shiga tsakanin yaya da kanwa fa zaiji kunya.

Uhm kawae tace tacigaba da kallanta, Bayan mangaruba kamar yadda suka saba kowa nacikin gida yana Zaune, antadi saikuma yan habaice habaicen daba’a rasasu acikin gidan, itade hankalinta gabaki daya baya wajensu yanakan phone dinta,

Jira takeyi kawae kiran najeeb yashigo, amma shiru saida
Har tayi shirin kwanciya tagama cire rai da kiransa, dan harta kwanta bacci, taji wayanta yafara ringing, koda taga number ne tarigada tasan waye yasa batayi Gigin daukaba sanda ta katse,

Tajira koda’a sake kira amma shiru harataji haushin kanta naja masa aji datatsaya yi gashi yanxu yakikira, Wani irin haushin kanta takeji nakin daukan wayan

Kusan 30 minute yakara kafin yasake kiranta, mai halidai bayafasa halinsa dan sai wayanna dab da tsinkewa kafin tadaga, shiru tayi takiyin magana, sallama yamata daga nasa wajan, amsawa tayi adakile,

Kingane waye A’a tabashi amsa shiru yayi danransa yadan sosu datace masa A’a kuma yasan bawai bata gane waye bane saitsan tsan rainin wayo,

Shitunda yakema bai taba kiran mace taki dauka ba saiyau, najeeb neh, oh yakake, lafiya ya mama da baba, kowa kalau, yayikyau amma meyasa kikace baki ganeba, hmm tace kawai tana masa magana cikeda rashin sabo,

Haka yayita jan ta dahira mai dadi hartadan sake dashi sai wajen 11:00 sukayi sallama dan bacci ne tab a idonta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button