BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

K’arfe takwas dai-dai hanna ta zumbula hijabinta tanufii shashin kilishii koda taje a palour tasameta, da fara’a, kilishii ta k’ar6eta sai riritata takeyii, itakuwa hanna taji dad’in hakan, kilishii ne tayi wata y’ar dariyar da kana kallonta kasan ta munafurcii ne tace, y’ata nashiga tashin hankali sosai, lokacin tafiyarsu yareema, gashi kuma kema kika shiga wani hali, ga baki d’aya hankalin mu atashe yake, mungaza sukunii, sunkuyarda kanta hanna tayi tace, ai gashi mundawo umma yanzu hankalin ku zai kwanta, wata dariyar kilishii tak’arayi tace ai kuwa y’arnan, yanzu munjii sanyii sosai.” aff kinga na sha’afah tun d’azu nahad’a miki zobo akan zan aika miki tunda kinzo aisai ki tafii dashi tafad’a tana miqewa, wani irin kwad’ayine yazowa hanna gabaki d’aya yawunta ya tsinke, Allah Allah takeyi akawo zo6on tasamu tasha, Har wani had’iye miyau takeyii.”
Da k’aton jug kilishii tadawo riqe ahannunta, ajiyewa tayi agaban hanna, cikin kunya hanna tace umma a’iina zan samu cup, inaso nasha ne,” dasaurii kilishii takwala wa wata kuyanga kira, umarnii tamata data d’auko cup, bata dad’e ba kuwa tadawo hannunta riqeda cup, ajiyewa tayi agaban hanna sannan tanemi izini ta zuba mata, k’ar6a hanna tayi takafa bakin ta tahausha zuciyarta d’aya, sanda tashanye sannan tatshi zata fita, umarnii kilishii tayi da a d’auki jug d’in abita dashi, godiya tayi sosai sannan tafice.”
Wata dariyar rainin hankali kilishii tayi tacce lallai wannan yarinya, shsshasha ce, kokad’an batasan mai sonta ba, inbanda abinki niceh zan miki zo6on? toko shi mijinnaki baikai wannan matsayinba, taja tsaki.”
Itakuwa hanna tana komawa sashenta, da kad’an kad’an taringa shan zo6on harta shanye tass, dan wani irin kwadayin zo6onne yakamata.”
Sanda tashanye kafin ta tuno bata ragewa Marshall ba, d’aga kafad’unta tayi????‍♀, sannan tace ohow, idan yazo zangaya masa.” dan tunda yafita d’azu haryanzu bataga idanuwansa ba, shirye shirye bikkunan da za’ayi yasa Marshall baidawo gidaba Sai kusan 10:15pm.” hanna na jiransa afalo dan yakanyii wuya ta iya bacci idan baikusada ita shiyasa take jiransa Yadawo.” da sallama yashigo ta amsa masa tana murmushi, yana zuwa ya zauna kusada ita.”
Sannu da dawowa yauwa cutie ya gidan?” Lafiya klau, ya ayyukan? klau cutie na, gaskiya yakamata abarmunkai ka huta haka, uhmm ainakusa fara hutuna, sai nayi months banfita ko nan da door ba, dariya hanna tayi sannan tace,” kahuta Sai kayi wanka naga Kamar agajiye kake, kaman kinsani nagaji dayawa.” yafii 30minute akwance a cinyanta, idanuwansa alumshe, amma Kuma ba bacci yakeyii ba.” hanna na wasa da gashin giransa dake had’e waje d’aya, bud’e idanuwansa yayi yace dear nagama hutun zanyi wanka.” ok tom tashi muje.”
Bayan yafito awankane Har yayi shirin kwanciya, hanna ta dubeshi, afff namanta honey, naje nagaida umma, harta bani zo6o.” gaban Marshall ne yayi mugun fad’uwa Jin ta ambacii zo6o, shikqnsa baisan dalilin fad’uwar gabanba.” shiru yayi baice komaiba, Sai Bayan hanna takwanta Har bacci nashirin ebanta, cutie yakira sunanata, uhmm ta amsa alamun bacci yafara kamata.” kinsha zo6onne?”
Uhmm nasha kayi hak’urii ban bar makaba amma gobe zanyi mana wani.” I LOVE YOU, yafad’a tana k’ara gyara kwanciyarta, uhmm kawaii yace baik’arayin maganaba.”
Kusan 3 nadare hanna ke kwance tana baccinta,
Shikuma Marshall Yana sallah, dan tunda hanna tafara way’annan irin abubuwan, bai iya bacci.”
Bayan ya idarda sallan yazauna Yana addu’oii wani irin ihuu hanna takwala, tatashi tana ihuu tana riqe kanta, tana cewa honey zasu kashenii, gasuncan, wayyo Allah tak’ara sake wani ihunn, tana shirin sauk’a daga gadon, da gudu Marshall yayi kanta.”

To be continued

Ur’s

  z33iiyybawa

BIBIYATA AKEYI

بسم الله الرحمن الرحيم

Writing by
©zaynab bawa
(Z33iiyyb3rw3r)

Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels

Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S

Wani sahabi yace, rana mun kasance muna Sallah a bayan Manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku'u sai ya ce Sami'Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da "yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.

.

Page 83
*

Riqeta yayi, tayin saurin shigewa jikinsa tana kuka tanacewa Wallhy zasu kamanii.”
Shhhhh yasa hannu abakinta dear bbu wanda xai kamaki.” kiyi shiru.”
Shirun tayi tana ajiyar zuciya addu’oii yaringa tofamata Amma duk da haka tak’i sakeshi, Kuma tak’yin bacci.”
Kiran sallah ne yasashi yatashi yanufii band’aki kank’ameshi tayi tace Ina zakaje?” toilet zanyii alwala ankira sallah.” girgiza Kai tayi Kamar mai shirin yin kuka tace dan Allah kayi sallah anan kada kafita, murnusawa yayi sannan yace tom dear taso muje muyi alwala, tare kuwa sukayi dan ko nan dacan bataso yamatsa, bayan sun idarda sallan ne yace cutie jeki kwanta nizan futa.”
Girgiza masa Kai tayi hawaye na shirin zuba, matsowa kuasada ita yayi yace ya rabb, bazan fitaba maza wipe ur tear’s, bbu musu ta goge hawayan,” Jan hannunta yayi yakwantarda ita Shima yakwanta kuasada ita.” addu’a yayi ta mata Har tayi bacci.” Sanda yaga baccin nata yayi nisa ne, yazare jikinsa yafice, dan biki za’ayii a government house, na murnar cigabanda k’asar tasamu na marshall.” 7:00.am dai-dai, hanna taji Ana tashinta, cutie, cutie, uhummm ta amsa cikin muryar Mai bacci, tashi maza, bak’i zasu fara zuwa baki shiryaba.” toh tace tana k’okarin miqewa, tashi tayi tazauna tana murmurza idanuwanta.” cikin shagwa6a tace wallhy ni hone,,,,,,,, saurin yin shiru tayi ganin yadda ta bud’e idanuwa bataga komaiba.” wani tsorone ya ziyarcii zuciyarta.” tashi tayi jikinta Yana 6ari tayi bandaki, Kai tsaye bud’ewa tayi kozataganshi, nanma Wayan Kuma batajii bud’e k’ofa ba.” suran wayanta tayi tafuta, abakin k’ofa tatsaya tatambayi wani soldier nan yashaida mata ai tun asuba yafita, bata iya komawa cikin gidanba, Kiran labba tayi tace, habibty dan Allah kizo yanzu kitayani zama, toh labba tace sannan takashe Wayan.”
Kiran hameeda tayi nan ma tace da’allah tazo.” jiran labba tayi Sanda tak’araso sannan suga shiga tare.”
Tad’ii suka zauna yii, ba’adade ba kuwa saiga hameeda nan tashigo itada hafsat, dagudu ta rungume hafsat tana murnar ganinta.”
Sunfii 15 minute suna hira kafin hanna taji muryar ammah, aikuwa da gudu tatashi tayi Kan Amma, itama Amma murnar ganinta takeyii.” sauk’a sosai hanna tamata Har tarasa mame zata kawo mata.” Ammah batafii 20 minute ba tatashi tace Jalal na jiranta amota.” kuka hanna tasaka tana cewa haba Ammah na, wata na nawa bangan Kiba? Da kina zuwa zakice Zaki tafii.”
Jawota Ammah tayi tana fad’in haba d’iyata, kibar kuka, zuwa jimawa zandawo dakyar ta lallasheta tayi shiru.”
K’arfe 4 dai-dai akafara walima, zuwa 6 aka gama, mama batazoba, saboda su karima.”
Hanna sashinta tawuce, bayan angama, tayi sallah ne tashiga kitchen, tafara had’a masa abincii, bata d’auki lokacii ba tagama dan dama bawani Mai nauyii bane.”
D’aki tashiga tayi sallan isha, tafito tashiga kitchen dan dawoda abincin dining.” da k’arfii ta ji muryar Marshall Yana cewa cutieee, itama da k’arfin ta amsa, yess honey, am home, ok boo am coming tafad’a tana wanke hannuwanta tafito.”
Wayam tagani babu kowa afalon da k’arfiii tace honey where are you?” Jin shiru yasata shiga d’ayan falon nanma shiru babu kowa, Kuma da’alamu ba’a bud’e k’ofaba.”
Komawa tayi nan danan jikinta yad’auki rawa, kudin dinewa tayi Akan Kujera, sai Kusan 11:30 taji k’arar bud’e k’ofa lokacin tayi kuka harta gaji, abubuwan dataji a wannan lokacii naban tsoro baya fad’uwa.” Jin bud’e k’ofa tayi saurin juyawa.” ganin Marshall dasaurii tak’arasa da gudu ta rungumoshi, tana cewa honey kafita dani daga gidannan, wallhy akwai aljanu aciki nibazan iya zamaba.” kuka takeyii Kamar ranta zai futa.”
Rungume ta yayi sosai Yana rattshinta, Amma hanna ta birkice masa, bayanda baiyiba daga baya Kuma tafara ihuu Kamar wata mai aljanu.”
Da k’arfinsa yariqota ya rungume tsam ajikinsa.” bayadda batayi ta kwace kanta ba, Amma takasa, dan ko jijjiga bayayi.” Sanda yaga tadaina muzul muzul yad’agota, idanuwansa sunyii jawur, yarasa maiyake damun hanna, yarasa tayadda zai shawo Kan matsalarta.”
Ido ya k’ura mata ganin yanda take sauk’e ajiyar zuciya.”
K’ara maida ita jikinsa yayi, ganin bacci yad’auketa yasashi tashi da ita yanufii Sama, kwantarda ita yayi sannan Shima yawanta agefenta, Sanda yakai 2hours kafin yatashi yad’auro alwala, yafara nafila.”
Bashi yatashi daga sallaya ba, saida yauma Kamar jiya, da ihun hanna, yaukam Har Gari yawaye bbu wanda ya k’ara rintsawa acikinsu.”
Gari na wayewa Kuma wani irin bacci yad’auketa,”
Sai 12 tafarka,”
Marshall yab’oye damuwarsa kwataa kwataa yakii gayawa ummii maiyake faruwa, dan gani yakeyi Kamar zaishawo Kan matsalar.”
Ahaka ya wunii bbu yanda yajeshi Yana tareda hanna itama bataso yafitan dan haka yazauna.”
Saida 9 nadare yayi suna zaune akujera, sallamar intisar ce ta ziyarcii kunnuwansu.”
Amsawa sukayi ta shigo tazauna, gaisheda Marshall tayi tazauna, sannan ayatsine tadubii hanna tace sannuu, hanna Kuma ko kallonta batayiba. Balle tasan tanayii.”
Miqewa Marshall yayi yace yawwa tunda ga intisarnan barina shiga wajan ummii na nemo Miki kindirmon kijiranii yanzu zandawo.” to kawaii tace yamata peck a forehead ya fice.” haryad’an fara tafiya yatuno bai tambayeta da yamrii takeso kokuma furaba, juyawa yayi yakoma palour d’in.” muryar intisar ce takatseshi daga magarnarda yake shirin yii, tana cewa aike banza ce tunda nafad’a miki Saina rabaki dashi Kuma baki hannani kusantar yanda yakeba.” idon Marshall harwani k’ankancewa sukeyi tsabar 6acin rai, idanda kalmar daya tsana arayuwarsa bai wuce a ambacii rabuwa tsakaninsa da hanna ba.” cii gaba tayi dacewa, Kuma nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba, sai kin d’andani rashinsa akusadake.” hanna wacce kwataa kwataa batason hayaniya ta lumshe idanuwanta ko tanka mata batayiba.”
Wata tsawa Marshall yadaka mata wacce ba ita d’aya ba Har hanna Sanda tarazana, Yana k’arasowa wajan yad’auketa da marii, bata ankara ba yak’ara mata wani.”
Saida tafad’ii Kan kujera yanunata da yatsa yace fucemin, fucemin nace tun kafin na tattaka ki.” da gudu tafice tana kallon tara-tara wani ikon Allah ne kawaii yakawota sashin kilishi, Jin kukanta kilishi tafito da gudu, ganin fuskar intisar akumbure, Maiya sameki? tafara tambaya, cikin kuka intisar tafad’a mata abunda yafaru.” Wata ashar kilishi ta lailayo tasake, dan kaza kazansa Akan wannan matar tasa zaimiki haka to wallhy nayi rantsuwa saina rabasu, saita fara haukar Tata da gaske, yanzu bakad’an takeyiba?”
To wallhy saitayi haukan gaske.” Kuma aure Kamar kin aureshi angama tafad’a tana surar wayarta tayi ciki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button