BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL
BIBIYATA AKEYI COMPLETE HAUSA NOVEL

Marshall yana fita shahainsu yawuce kai tsaye, mukarrabansa na biyedashi abaya, shahin yayi k’ura sosai tunda hanna ta6ata bbu wanda yak’ara shigansa.”
Zama yayi akan carfet dirsham bai damu da dattinsa ba yace, hava hanna yaya zakimun haka?” mena miki haka, zataki tafii kibar zuciya ta cikin kunci? ashe duk maganganun da kike fad’a da gaskene? ashe dama tafiya zakiyi ki barni yasa kike fad’amun irin wannan maganar?
Hawaye ne yabiyo kuncinsa, wanda rabonsa dasu tun yana yaro, yana yaronma bazai iya recalling lokacin ba.”
Baidamu daya goge hawayen ba, dan koya goge wasu zasu biyo baya, kuma aganinsa hawayen dake zuba a idanuwansa, sune sassauci agareshi, zaiso sufii haka yawa ma, zaiso ace yayita kuka, har indai hakanne zaisama masa sauki,
Lokacii d’aya kansa yasara yahau ciwo, cikin ransa yana tunani yanzu awani hali, hanna ke ciki da juna biyu.”
Sunbatu kawai yafarayi,
Hawayen na zuba yak’ara cewa meyasa zakimun haka, kinyi alqawari bazaki bazaki fad’amun irin magan ganunda ke sani cikin damuwa ba, balle yaje ga tafiya ki barni.”
Yanda kasan wani zaucecce yaketa maganganu , wasun kanma koya fad’i bazaka gane meyake nufii ba.”
Marshall yakai 3day’s bbu wanda yakalli kwayar idanuwansa, yana cikin shashinsu, koda anzo ana bugawa baya kula kowa, yanaji yake sharewa, mai martaba yakira baba yasanarda shi abunda ake ciki.”
Sosai baba yaji bbu dad’i aranar yakamo hanya yazo garin, yana isa ya wuce fada, dake shikad’ai yazo Ko driver bai d’auko ba.”
Sosai mai martaba yaji dad’in ganinsa, bayan sun gaisa ne mai martaba yasa aka kira masa ummii, takai 15minute kafin ta iso, duk tarame gabaki d’aya ta lalalce, bayan sun gaisa ne, baba yad’an nisa kafin yace, shawara ce nakawo, wanda ina tunanin shine mafita dashi damu kuma baki d’aya, mai martaba ne yace, muna jinka, dan yanzu dolen mafita muka zauna nema, baba yacigaba da cewa, ni aganina abunda zai zama maslaha damu dakuma yaronnan shine kawai, ak’ara masa aure, gaban ummii ne yayi wani mummunan fad’uwa, tace haba da Allah, wai ce muku akayi hanna baxata dawo bane Ko kuma?” girgiza kai kawai baba yayi yace Ko d’aya ba’ace hanna bazata dawoba, kuma shi ai mijin mace hud’u ne, koda tadawo saidai tayi hak’uri, amma Ganin wata kusada shi zai rage masa damuwa,zai rage yazauna yana tunani, mai martaba baice komai ba juya maganar kawai yakeyi, sai dayaji kowa yayi shiru sannan yace, amma kana ganin hakan shine mafita bbu wata hanya? Girgiza kai baba yayi sannan yace gaskiya idanma da’akwai wata hanyar nidai bansanta ba.”
Mai martaba yace, toh Allah yaza6ar mana mafii alkairi, da ameen baba ya amsa, sannna yacigaba da cewa, baka ganin er k’aninka, naga kusan kamarsu d’aya da ita hanna d’in ai sai ka tambaya masa ita, dasaurii ummii tacafe, tace wah wai hameeda kuke nufii, amma wannan babban cin amana ne, er uwartata xaku aurawa mijinta dan bbu idonta, wallhy Allah bada yawuna za’ayi wannan auranba, tatashi tafice tana sharar kwalla.”
Binta da kallo sukayi su dukansu, sannan mai martaba yace, kasan halin mata da wani irin abuu, abunda Allah ya halasta su zasu nemi haramta maka shii.”
Nan sukayi sallama suka tashi akan baba zai wuce su zauna suji yadda za’ayi shida, abba.”
Umma nashiga d’aki tafashe da kuka, kawai tana jajanta abunda ake shirin aikatawa baiwar Allah.”
Labba ne tamatso kusada ita tace, ummii menene yafaru?”
Wani abunne yasamu yayan?”
Girgiza mata kai ummii tayi, sauke ajiyar zuciya Labba tayi, ummii ne tace kayya er nan daina wata ajiyar zuciya ina maraban wani abu yasameshi, da abunda ake shirin aikata masa yanzu.”
Riqo hannun ummii Labba tayi tana zazzaro ido sannan tace, me za’ayi masa?”
Aure zasu masa, ummii tabata amsa atakaice, aure kuma ummii?”
Eh aure kuma wai er uwarta hameeda, subhanallahi hameeda ummii?” wannan wani irin cin amana ne, nan danan idanuwanta suka fara zubda kwalla.”
Tatashi dasaurii tafice dagudu, bata tsaya ba sai sashinsa, tana zuwa tafara bugawa kamar wata mahaukaciya, jin bugun yayi yawa yasa yatashi, dakyar yabud’e, kofan.”
Dagudu Labba tashige jikinsa tana kuka, bubbuga bayanta yafarayi, amma bai iya magana ba, sanda tagaji dan kanta tad’ago tadubeshi tace, yaya Allah aure zasu maka, suwa? ya tambaya, su abba, mana, d’agota yayi yace kai Labba kodai bakiji dakyau bane?” ni nace musu inason aure?” Allah kuwa yaya wai kuma da hameeda, zaro ido yayi yace hameeda kuma labba, eh Allah yaya, ajiyar zuciya yasauk’e yace to ai yazo gidan sauki, zuwa gobe, zanshawo kan matsalar har indai hameeda ce, dawatace sai in damu.”
D’agowa tayi tadubeshi tace Allah yaya, d’aga mata kai yayi yace, Allah kuwa acikin week d’innan zan shawo komai.”
Sai alokacin hankalin Labba yad’an kwanta, tadubeshi tace yaya kaci abincii ne, girgiza kai yayi yace banjin yunwa ne, yakamata kaci ai tabashi amsa takaice.”
Tashiga kitchen tahad’a masa abincii, dakyar yaci, sanda yaci kuwa tabar shashin, taje tafad’awa ummii Yanda sukayi, Allah yasa adace kawai ummii tace.”
Baba ya isa gidan abba suka zauna, sukayi magana, abba fur yak'ii yarda, sanda baba ya nuna masa bacin rai, ya ce, idan kanaso kanunamin bani nahaifeta ba shikenan, amma ni nadauka yarana da naka duk d'aya ne, nan danan abba yarikice, har idanuwansa suka ciko yace haba yaya, wannan wani irin magana ce, baba ne yace idan bahaka kake nufii ba, mai yasa zanyi magana kace bahaka ba."
Kayi hak’uri yaya wallhy hameeda erka ce duk Yanda kakeso kayida ita.”
Tom nagode idan kashiga kayiwa matarka magana kajii, nima idannaje zanmata magana.”
Ahaka sukayi sallama.”
Abba ya tashi yashiga gida jikinsa bbu kwarii.”
To be continued
Ur’s
Z33iiyyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI
بسم الله الرحمن الرحيم
Writing by
©zaynab bawa
(Z33iiyyb3rw3r)
Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels
Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S
```Alhmdllh am so much bless, addu'anku sunyi aiki, godiya Mai yawa```
================
PAGE 92
*
Yau ma kamar wancan karon sassafe sadiq yatashi yatafi ruga d’an d’auko malam,
Dake malam baisanda zuwansa ba, kuma baishirya ba, sanda yajirashi ya shirya, sai 1:00.suka iso, yana zuwa yabaukaci ganin hanna, kawota akayi sai zazzare idanuwanta takeyi kamar wanda tayi k’arya, dasaurinta tak’arasa gefen inne tazauna.”
Cikin damuwa inne tafara yimasa magana, tace, malam duk randa nabata ruwan addu’oii nan, saitayi k’ok’arin halaka kanta kokuma abunda yake cikinta, kuma tanashan wuya sosai.”
Malam ayad’anyi shiru kafin yace, maganar gaskiya yarinyarnna turan aljanu aka mata, kuma ahalin yanzu idan aka matsa sai anciresu, kafin su fita zasu cutarda ita kokuma abunda yake cikin ta, zasu iyayin sqnadiyar cikin, idon inne ya cikciko tace yanzu wannan yarinya wani abu zatayi dahar za’a tura mata aljanu, mutane kokad’an bbu imani.”
Malam ne yadanyi jim kafin yace, Aibasai tayi musu wani abunba, yanzu d’an adam ake kiwo, ba dabba ba.”
Yanzu nakaoma zanyita yi mata addu’a da sauk’an qur’ani, yanzu zaikai kaman yaushe haihuwanta?”
Diddi ne tace, ba lallai ya k’arasa nanda wata biyu ba.”
Toh in sha Allah nan da wata biyu zata samu sauki, dan yanzu Allah kad’ai yasan halinda danginta suke ciki.”
Jijjiga kai inne tayi tace, hakane dole zuri’arta zasu kasance cikin tashin hankali da zullumii.”
Allah yabata lpy, dukansu suka amsa da amin, sai bayan la’asar, sadiq yamayar da malam.”
Marshall ne zaune da kayan soldier's, ajikinsa rabonsa da saka kayan yakai 7month, yarame kam sosai, amma Sun masa kyau sosai, wayansa yad'auko yayi dialing numb d'in, captain Ahmad wanda ayanzu yadawo genaral Ahmad, yana shiga kuma aka d'auka, baijira wani sabon zance ba, yace kasameni a shahi na."
Kusan 30minute kafin yak’araso sanda yakirashi yanemi izinin, shiga kafin yashigo, ganin agonnasa ayanayin daya dad’e bai ganshi ba yasa yak’araso dasaurii, yana fara’a, wajan zama yabashi, sannan yace magana nakeson muyida kai sannan kuma, ina neman alfarma, dasaurii, G Ahmad yace hava, yallabai yanzu har zaka nemi abuu awajena, sai ka kirashi da, taimako, kafadeshi kawai kai tsaye amtsayin umarni, Murmushi Marshall yayi sannan yace, yanzu zaka goyi bayan nayi aure?”
Aure kuma yallabai kokadan bazan goyi baya ba.”
B’atan madam ba hakan yana nufin bazata dawo bane, wallhy yallabai Ko 10yrs zatayi kajirata, dannasan idan itane awajanta, itama jiranka zatayi.”
Yak’e Marshall yayi akaro na biyu sannan yace, kuma er uwarta sukeso na aura, girgiza kai G Ahmad yayi yace, gaskiya hakan baidace ba,
Jijjiga kai Marshall yayi yace shiyasa nakeson kataimaka mun yau daddare kaje gidansu amatsayin, kana sonta, banso kab’oye mata komai, inason kaida ita, ku nunawa iyayenmu kun dad’e kuna soyyaya, dannasan nata wajanma bayarda zatayi ba, idan kaje mata da wannan maganar zatayi saurin amince wa.”
G Ahmad ne yace indai hakan zaitaimaka, to nayarda zan aureta, zanje yau nasameta, nagode Marshall yace, Ahmad ya girgiza kai yace bbu godiya atsakanina dakai.”
Ya tashi yafita.”
Dad’i ne yakama Marshall nafarko yarabu da aurenda akeso ayi masa, nabiyu kuma, na cikawa hanna burinta, dan bai manta lokacinda tace masa, inason kacikamun burina kasa, C. Ahmad ya auri hameeda.”
Tashi yayi fuskarsa ad’an sake yanufii sashin mahaifinsa.”
Su kansu sojojin sa sunyi mamaki, yanda yau suka ganshi, yana cikin kuzarinsa, da sallama yashiga, falon mahaifinnasa, amsawa mai martaba yayi dan ya dad’e baiji shi da irin wannan muryar ba.”
Koda zaiyi sallama saidai yayi ciki-ciki, kallonsa mai martaba yakeyi, har yak’arasa shigowa,
Yazauna yana gaidashi, shi kansa yaga fara’a kwance fuskar mahaifinsa, alamun yaji dad’in ganinsa ahaka.”
Mai martaba ne yacigaba da cewa, dama gashi inason muyi magana, sosa kai Marshall yayi yace to ai gani abba.”
Gyaran murya mai martaba yayi yace, dama inason na fad’a maka munyanke shawrar yimaka aurene, zaro ido yayi, sannan yayi kamar baisaniba yace, aure kuma abba, eh aure tunda kakasa daukan qaddara, kuma er uwar matarka zan aura maka, wacce kenan abba?, er gidan k’aninsa, kamar da gaske Marshall ya nuna firgici yace, abba budurwar Ahmad nefa, wani Ahmad? Dan gidan kanwan ummii mana, abba shine saurayinta, yaya za’ayi haka, k’anina nefa kamar yanda nakejin affan haka nake jinsa, kuma ku kad’ai yasani matsayin iyayensa, zai d’aukeku masu sonkai idan kukayi haka.”