GARKUWA PART 3

Junainah ta sauƙe wani irin masifeffen ajiyan zuciya kamar dai irin ka dade kana neman abu baka samuba ka samu.
Wani irin daɗi takeji na musamman yana ratsa mata jiki da zuciya.
Haka nan taji tsikar jikinta yana tashi tsaye.
Har bakin Part ɗin su. Sukayi parking.
A hankali suka fito.
Shi kuwa Salmanu kayan nasu ya fitar ya ajiye bisa barandar dake bakin ƙofar falon tare da cewa.
“Toh ni zan juya in kin shiga Khadijah kiyi mata barka”.
Da sauri Khadijah tace to.
Kana ta sunkuya ta ɗauki jarkan man Shanu Junainah kuwa galam ɗin zuma ita kuwa Sara ta ɗauki kwaryan ƙoyayen.
Inna Amarya kuwa jarkan madarar shanu.
Sara ce a gaba Junainah na biye da ita a baya sauran na biye dasu.
A can cikin falon kuwa dai-dai lokacin Sheykh ya fito Falon gefen Shatu ya zauna.
Jalal kuwa tsaye yake gefensu yana kallon Babyn dake hannun Sheykh su Jamil Affan Yah Jafar kuwa suna Dinning area.
Haka nan sukeji zuƙatansu na harbawa da ƙarfi da ƙarfi.
A hankali Sara ta buɗe ƙofar tare da turo kai tana mai sallama.
A hankali Junainah ta sako ƙafarta cikin falon tare da buɗe muryarta sama tace.
“Assalamu alaikum Adda Shatu”.
Wani irin ratsa amon sautin muryar ta kunnuwansu Jalal Jamil Jafar Sheykh sukayi tare da juyowa da sauri suka fuskanci bakin ƙofar ɗakin.
Dai-dai lokacin Junainah ta shigo cikin falon.
Cike da mamaki Sheykh Jabeer, Yah Jafar, Jamil, suka zuba mata ido tare da haɗa baki wurin cewa.
“….!
Littafin GARKUWA na kuɗine akwai Normal group 300, akwai Special Group 1k babbancinsu a wurin yawan posting ne ga ac no 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa.
Sai kuyi screenshort na Debit Alert ɗin sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276 ƴan Normal group in baki da halin biya ta ac zaki iya sayan katin mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276.
By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM – &: Cikin zuba mata ido tare da mamaki muryarta da kamanninta suka haɗa baki wurin cewa.
“Wa alaikassalam”.
Shatu kuwa da sauri ta miƙe tsaye tare da nufosu cikin farin cike take cewa.
“Oyoyo Allah sarki My Junnu”.
Da gudu Junainah ta ƙara sa inda take ruggume juna sukayi suna dariya.
Da sauri Shatu ta ɗan ɗago kanta ta kalli Khadija date cewa.
“Wato ma Junainah kawai kika gani ko Adda Shatu shekara biyu baki ganniba ko ki kulani”.
Da sauri ta saki Junainah ta ruggume Khadijah tana dariya tare da cewa.
“Oh Dija ƙorafi”.
Ita kuwa Junainah dariya tayi tare da cewa.
“Oh su Adda Dija kishi akeyi dani”.
Cike da mamaki da kuma farin cikin ganin Junainah Ummi ta kalli Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
“Lalako jaɓɓama mon poi”.
Da sauri Shatu ta ture Dija cikin tarin so ta ruggume Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
“Aunty Amina Inna Amarya marabanku.”
Da sauri suka ɗan juyo jin Sheykh yana cewa.
“Sannunku da zuwa”.
Cike da kunyar sirkai sukace yauwa.
Kana sukabi bayan Ummi dake cewa.
“Ku iso mu shiga ciki.”
To sukace kana sukabi bayanta itama Shatu tabi bayansu.
Sara kuma ta kwashi kayan duk ta kaisu kitchin.
Ita kuwa Junainah jin muryar Sheykh ne yasa ta juyo da sauri.
Ganinshi riƙe da jaririyar ne yasa ta juyo da sassarfa ta nufi inda yake tare da cewa.
“Hamma Jabeer?”.
Tai mgnar tana zubawa Jalal da Jamil ido, da alamun so take taga wanda zai amsa a cikinsu ta gane waye shi.
Cikin sauƙe wata iriyar nannauyan ajiyan zuciya yace.
“Na’am Junainah”.
Da sauri ta ƙara so inda yake, tana isa ta ɗan sunkuyo tana kallon Babyn murmushi mai yalwa tayi tare da cewa.
“Ina kwana Hamma”.
Yana mai kallon yantsun hannunta data miƙo mishi alamun ya bata Babyn yace.
“Lfya lau Alhamdulillah Junainah ya Bappa”.
Da sauri tace.
“Yana lfy yace in gaidaku duka, harda Yah Jafar Yah Jalal da Yah Jamil”.
Da sauri ta ɗan juyo jin Affan na cewa.
“Banda ni kenan”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“A a harda kai mana”.
Sai kuma ta juyo tana kallon Sheykh tare da yin ƙasa da murya tace.
“Hamma Jabeer me sunanshi”.
Murmushi yayi tare da yin ƙasa da murya kamar yadda tayi yace.
“Affan”.
Cikin gyaɗa kai, ta ƙara matsowa zama tayi gabanshi tare da miƙa sawunta cikin zaƙuwa tace.
“Hamma Jabeer bani ita mana”.
Da sauri yace.
“Junainah zaki iya kuwa inafa tsoron kada ki kada ita”.
Da sauri tace.
“Zan iya mana”.
To yace kana ya sunkuyo ya ɗaura mata yar bisa cinyarta, yasa hannunshi ya tallabe kan Babyn.
A hankali Jalal yayi wani irin rumtse idonshi da ƙarfi.
Jamil kuwa cikin sanyi ya taso ya taho kusa da ita, matsawar da yayine yasa Yah Jafar hangota.
Miƙewa yayi da sauri ya nufo tsakiyar falon.
Ido suka zuba mishi ganin yadda yazo ya tsuguna gaban Junainah da Babyn da Sheykh ɗin.
Da sauri Junainah ta ɗago kanta ta kalleshi cikin zuba mishi ido cikin ido tace.
“Ina kwana”.
Shiru yayi bai amsa ba, sai hannunshi da yasa kan sawunta yatsun ƙafarta ya ɗan kama tare da rumtse idonshi.
Da sauri ta kuma cewa.
“Ina kwana?”.
Shiru bai amsaba sai kuma ga hawaye na zubo mishi.
Hakane yasa ta juyo da sauri ta kalli Sheykh cikin rauni ido cike da hawaye tace.
“Hamma Jabeer baya mgn ne? Meyasa yake kuka.”
Ta ƙarashe mgnar hawaye na zubo mata.
Da sauri Jalal ya tsuguna gabanta tabbas ta tuno mishi abu da yawa kam Mameynsu sabida masifar kamar da sukeyu.
Haka nan yaji son yarinyar yana ratsa dukkan sasan jikinshi gaba ɗaya.
So irin na ƴan uwataka so irin na wa da ƙanwa
Cike da mamaki Sheykh yake kallon Jalal da yasa tafin hannunshi yana share mata hawayenta.
Wanda ita kuma haka ya ƙara tunzura zubowar hawayen nata.
Cikin rawan murya tace.
“Hamma Jabeer meyasa yake kuka?”.
Cikin wani irin yanayi Jamil ya tsuguna shima ya zama sun zagayeta sun sata a tsakiya.
Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin bisa kanta cikin rauni yace.
“Nima ban saniba Junainah wata ƙil yana tsoron kada ki kada Baby ne ko kuma muryarki ce tayi iri ɗaya da muryar Mamanshi”.
Cikin shessheƙan kukan da haka nan taji ya kubce mata tausayin mutumin ya rufeta cikin rauni tace.
“A a bazan kada itaba, Ummey na ta koya min yadda ake riƙe yara ai lokacin da mukaje gidan Abboi da yarinyar Maman Idris to Ina Maman nashi”.
Sai kuma ta ɗan musukuta ta gyara zamanta tare da gyara riƙon yarinyar.
Cikin sanyi Jamil yace.
“Mamanshi bata nan”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Ina take?”.
Tai mgnar da alamun tausayawa.
Sheykh ne ya ɗan sunkuyo ya kalli ƙwayar idonta a hankali yace.
“Mugayanen magauta sun sabauta rayuwarta sun ɓadda ita”.
Kanta ta jingina jikin Jalal dake gefenta cikin sanyi da rauni tace.
“Ayyah Allah ya isan mata, Allah zai saka mana”.
Sai ta kuma kalli Yah Jafar ɗin da tsananin kamanninta da Mameynsu ne da kamar murya ya sashi zubda hawaye a hankali tace.
“Kayi haƙuri Yaya zamuyi ta mata addu’o’in, kuna Ummey na zata zama mamanku, kuna so ko?”.
Da sauri Sheykh ya gyaɗa mata kai ganin yadda ta ƙarashe mgnar da zuba musu ido”.
Affan kuwa gefen Sheykh ya zauna yana mai kallonsu cike da al’ajabin yanayin da suke ciki Especially Jalal da ba kula yara yakeyi ba.
Ummi kuwa a can cikin ɗakin Shatu, tayiwa su Aunty Amina iso.
Bayan sun zauna ne, Sara data kai kaya kitchen ta kawo musu ruwan.
Kana ta fito ta koma Kitchen taci gaba da aikinta Ummi na biye da ita a baya.
A falon ta tsaya tare da zubawa ikon Allah ido.
Muryar Junainah dake iri ɗaya sak da muryar da bazasu taɓa mancewa da itaba a duniya.