NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Inaji ina gani suka tafi suka barni ina kuka, bayan kamar mintin 30 da tafiyar su naji an bude kofar gida an shigo an kulleee………….

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs A.M

Page 19

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

  Gabana ne ya fadi hakan yasa ni dafe kirji na cike da tashin hankali nasan dai dole mijina ya shigo dakina duk da karancin shekaru na amma nasan aure ai.

Gyara zama na nai ina da’da lullube fuskata jin shiru har bayan minti goma yasa ni bude fuskata a hankali, banga kowa ba kuma da alama ba’a bude kofar palourn bama.

Mikewa nai cikin fargaba na yaye mayafina zuwa kafada, fita nai palourn na tsaya ina kallon kokarin da iyayena sukai gun tsara min gida duk da talaucin da muke ciki.

Alhamdulillah kawai na fada ina shafa kujerun dan sun min kyau gashi kuma hadda TV, murmushi nai na juya gun kofar ta window din dake kallon tsakar gidan na leka amma banga kowa ba hakan ya tuna min da Aunty tace min dakwai dakin sa daban a gidan.

Ajiyar zuciya nai inajin wani sanyi a raina sbd da dukkan alamu mijin nawa baxai shigo dakina ba knn.

Addua nai na tofa a kofar palourn na kulle da mukulli na kashe bolb da fan din palourn na nufi dakina, ina shiga na bude wardrobe dita na dauki wata rigar bacci doguwa na sa na shanya kayan a kofar wardrobe din sbd suka iska na kashe fitila na kwanta.

Kasa bacci naj sai juyi nake ina tunane tunane, a bangare daya ina tunanin mamanmu da muhd dasu sumy a dayan bangaren kuma ina tunanin irin zaman da zanyi a gidan nn.
Ganin baccin yaki zuwa ne yasa ni janyo wayata na kunna karatun Qur’ani mai girma, ko minti goma banba da kunnawa wani bacci mai dadi ya daukeni.


Bangaren Noor kuwa tunda ya shigo gidan kallo daya yaima part din amarya ya dauke kansa ya bude dakinsa ya shige.
N
Yana shiga ya cire kayansa ya daura toilet har ya kai bakin kofa ya tuna ynxu fa bashi kadai bane, hakan ya sasa juyawa ya dauko boxer dinsa da jallabiya ya fita.

Bayan fitowar sa daga wanka zama yai gefen katifar sa ya shafa maj da turare ya kwanta.
Shiru yai kawai yana tunanin kalar rayuwar da zaiyi da mace karkashin Inuwa daya a matsayin matar sa, kawai dai yasan zaiyi kokarin yaga ya fita hakkinta gurin ci da sha da kuma sutura.

Hakan daya tuna ne ma yasa shi mikewa ya dauko paper da takarda yana rubuta kayan abincin da yasan zasu bukata….

**
Kiran sallah ne ya tashe ni daga baccin da nake ahankali na bude idona ina kallon saman silin din dakin, tuna wa danai inda nake yasa ni mikewa da sauri ina addua.

Tashi nai na dau hijab dina na kunna fitila, palour na fito na tsaya bakin kofa bayan na bude ina lekawa ganin kamar ba kowa yasa na nufi kofar dake kallon dakina.
Ina budewa naga kitchen ne, burgeni da kitchen din yai yasa ni bata lokaci gun kallon sa, sai da na gaji sannan na fito na bude dayan kofar nan naga bandakin shima ya min kyau sbd ban taba ganin toilet da ya tsaru irin haka ba gashi hadda shower(????)

Ina fitowa daga bandakin bayan nai alwala naji nai karo da wani abu da sauri na dago don ganin abinda nai karo dashi……..


Kallon dada Ammi take kawai ta rasa me za tace mata kuma.

Tsaki dada tai ganin kallon da Ammi take mata tace “shiyasa duk madu ya bi ya raina ki hakurin ki yayi yawa kin ganni nn zamanin da nake gidan aurena kishiya bata isa ta ban tsoro ba sai dai ni na bata wallahi amma dube ki ke kin tsaya kishiya ba gasa miki aka a hannu kin kasa daukan aktin(action????)”

Dariya saudat tai tace “dada action ake cewa ba aktin bafa”

Tsaki dada tai ko kallon saudat batai ta ta juya gun ammi tace “ina jin halimatu wani mataki kikai shirin dauka in kuma baxa ki iya ba ki yarje min naje gun shuman risht(human right)”

A hankali Ammi tace “dada kawai na hakura Allah na tare da mai gaskia a ko’ina shiyasa nai shiru kawai sai dai muyi ta binsa da addua Allah ya dawo dashi hanyar daidai”

“Ameen” cewar dada data kara rafta tagumi tana kallon Ammi, yana daga cikin dalilin da yake sa take kara jin kaunar ta sbd hakurin ta da hankalin ta…


Bude ido tai ta ganta a xaune a wani daki na kasa ba komai a dakin sai tabarma gefen ta kuma akwatin kayan tane da ta zuba.

Zabura tai ta mike ta fito tsakar gidan mutane ta gani sun kusa talatin yara da manya da samari da yan mata.

Cikin tashin hankali take kallon gidan ganin kasa ne mai dauke da kofofi sun kai goma sha biyar.

Gidane daga gani kasan family house ne irin na gargajiya.

Ganin fitowar ta yasa wata mata wacce zata kai shekaru 38 tace “amarya kin fito knn dama ynxu nake cewa aje a taso ki kiyi mana girki tunda girkin kine sai kinyi kwana bakwai kina mana girki.”

Sauran matan gidan ne suka fashe da dariya suka ce hakkun maganar ki uwar masu gida.

Wanj hura hanci matar tai jin abinda aka ce mata.

Kallon tara saura takwas tai ma uwar masu gida tace ke a suwa zaki sani girki a wannan kaza min gidan ina habyby yake dubai yace zamu yana ganmu a nan kuma.

Wani mari taji an dauke ta dashi tana juya wa taga Alh Bashir da mamaki ta dafe fuska tace mai nai ma ka mare ni ina ne nn.

Wani banzan kallo yai mata yace nan shine gidan auren ki ga dakin ki can anan zaki zauna dama ba ke da uwar ki masu son abin duniya ba to ynxu ya zakuyi.

Anan kauyen anan zaki zauna kuma kar ki sake ma iyalai na rashin kunga duk cikin su babu sa’an ki yanzu wuce muje daki ki ban hakkina so nake na koma kano ynxu kafin uban daki na ya dawo.

Haka ya ja ta suka shiga daki tana masa turjiya ya kwantar da ita a kan katifa ya sa mata karfi ya biya bukatar sa duk ta cika gidan da ihu amma ko a jikin sa yana gamawa ya fito ya shige dakin da yake mallakin sa ya kintsa ya fito yai ma matansa sallama ya ficewar sa ya tafi.

Yana tafiya uwar masu gida da matar sa ta uku suka shigo dakin a kwance suka ganta ta bude kafafuwa ta wargeje sai kuka take tana kiran umma.

Cike da mugunta suka kama ta da duka sai da suka ga ta daina motsi sannan suka debo ruwa suka watsa mata suka juya suka fice.

WANENE ALH BASHIR

Alh Bashir ko ynxu muce malam basharu haifaffen kauyen zaria ne anan ya tashi yayi karatun islama maraya ne wanda kanin baban sa ya rike sa.

Yana fara mallakan hankalin kansa ya shiga gari ya fara buga bugan neman kudi har ya shigo garin kano anan Allah ya hada sa da wani mutum yake masa aiki, sai ya zama kamar babban yaron mutumin don y sake masa sosai.

Matan sa uku ynxu ya kara data hudu duk suna zaune a kauyen su.

Matar sa ta farko rahama wacce ake kira da uwar masu gida masifaffiya ce ta gaske haka kuma mace ce mai zafin kishin masifa ga makirci ta iya, yayanta goma sha biyar

Sai ta biyu hafsa wacce ake kira hansai ita dai dadan sauki sbd bata shiga harkan mutanen gidan amma fa in taku ta hado ku sai anje gaban mai gari, ya’yanta goma itama

Sai ta uku kaltume ita kam taso dame su gaba daya a mugun hali sai dai kasancewar uwar masu gida masifaffiya ce yasa ta kwantar da kai tana ma uwar masu gida bayyana ya’yanta 7 itama

Sai kuma amarya walida yar gatan umma da baba.
..


Da sauri na dago don ganin abinda nai gamo dashi wani irin faduwa gaba na yai ganin………..

More comments more typing

Mrs A.M????

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

    Written by 
        Mrs A.M 

Page 20

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

  Bature na gani a gabana yana sanye da jallabiya kansa sanye da hula irin ta sanyi, da sauri naja baya ina kalle kalle ganin ba sarki sai Allah yasa na fara ja baya ina yarfe hannu na kamar wacce aka zane.

Bangaren Noor kuwa shima kusan hakan ya faru da shi sbd kwayar idonta daya gani sai da yasa gabansa fadi amma yai ta maza ya dake yana kallonta ganin sai yarfa hannu take.

Cikim kidima da tashin hankali na cigaba da juyawa don ganin inda zanga mijin da aka aura min ya fito amma banga kowa ba hakan yasa na juya gun sa nace “kaga Bature don Girman Allah kayi hakuri ka fita wallahi amarya ce ni jiya jiyan nn aka kawo ni kar mijin nawa ya fito ya ce na kawo nasa namiji gida.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button