NOVELSUncategorized

DIYAM 69

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty Nine: Mrs Abatcha

Assalamu alaikum

Naga votes dinku, kuma kamar yadda nayi tsammani kusan 99% sun goyi bayan a fito da Saghir. Inda aka samu rabuwar kai shine akan lokacin da za’a fito dashi, kafin biki ko bayan biki. I followed the majority kamar yadda
nayi alkawari amma na rubuta in such a way that suma minority din zasu samu satisfaction.

Thank you.

We are almost done insha Allah.

Ta lumshe idonta tare da jingina kanta da jikin kujerar da take zaune akai tana murmushi mai sauti wanda yafi kama da dariya. Murjanatu da take zaune kusa da ita tana cin abinci ta dakata da abinda takeyi tana kallon Diyam sai ta bude ido tace “what? Menene ya faru kike dariya ke kadai?” Diyam ta daina dariyar da take yi amma bata ce komai ba sai Murjanatu ta warce wayar daga hannunta ta karanta message din nan take ta mike tana tsalle tana kiran Judith, Judith tana fitowa tayi mata bayanin cewa auren Diyam za’ayi sai itama ta kama murna suna rawa a tsakiyar palon, Diyam tana zaune tana kallon su a ranta tana jin kamar ta tashi suyi rawar tare amma sai ta hana kanta.

Sai da suka gama tsallen murnar su sannan Murjanatu ta zauna tana haki ta jawo phone dinta, Diyam ta bude ido tace “hey, me zakiyi?” Murjanatu tace “su Adama zan gaya wa” Diyam tace “ai za’a gaya musu a can, ki barsu kawai saji a can” Murjanatu tace “yanzu su Adaman ma kunyarsu kike ji? To Papa zan gayawa ma, in ce masa gaki nan kin saka waya a gaba kina ta dariya kin kasa rufe baki kina murna zaki auri dansa” nan da nan Diyam ta mike ta murde hannun Murjanatu ta karbe wayarta ta tafi daki tana cewa “nayi seizing phone dinki, bazan baki ba sai anyi hutu”.

Tana shiga dakin Murjanatu ta dauki tata phone din ta kira Sa’adatu wadda a lokacin suna tare da Falmata sai suka kira Adama da taje school a lokacin suka hada conference call sannan Murjanatu ta basu labarin abinda yake faruwa. Duk sunyi murna sosai musamman da yake wannan shine biki na farko da za’ayi a gidan su. Sa’adatu tace “oh su yaya Aliyu za’ayi aure, I wonder ta yaya suke magana da Diyam din da wannan turbunanniyar fuskar tasa” Murjanatu tayi dariya tace “wallahi in kunga dariyar da yakeyi mata ko, zaku dauka chanja shi akayi gaba ki dayan sa” sun jima suna hirarrakin su sannan suka lissafa kwanakin da ya rage kafin bikin sai kuma suka fara tsare-tsaren events din da zasu shirya. Sai da suka gama Murjanatu tace “Allah yasa ya yarda, zamu iya gama shirya komai yace shi ba za’a yi wa matarsa kwalliya a shiga da ita cikin mutane ba, kishi ne dashi kamar me”.

Sai da suka gama Murjanatu ta dauki wayar ta kai wa Diyam har daki ta mika mata tace “thank you for letting me use your phone” sai ta ajiye ta fita da sauri tana dariya. Diyam ta dauki phone din ta duba numbers din da Murjanatu ta kira, sai tayi murmushi tana mamakin zumunci irin na wadannan mutanen, sam basa nunawa Aliyu yan ubanci ko dan akwai wayewa sosai a tare da su?

Daga gida ma Mama ta kira Diyam ta yi mata bayanin duk halin da ake ciki, sai kuma ta umarce ta data kira Rumaisa suyi shirye shiryen abinda zasu yi kafin tazo gidan.

Sanda sukayi waya da Sadauki kuma sai yace mata “guess what? Na sayi fili zan yi gini” tayi dariya tana rike baki yace “au, dariya ma na baki ko?” Tace “I tot zaka sayi gida ne kawai, ko kuma ma ka riga ka siya” yace “hmmm, nima na dauka zan siya gidan ne, but then an opportunity presents itself to me, na saka a nemo min gida sai dillalin ya gaya min akwai wani fili ma in ina so, sai na bincika na gano ashe fili na ne, filin mune Diyam da Baffa ya siya mana zamu gina gidan mu, all these years ba’a gina shiba har sai daya dawo hannun mu. And now I hired wani construction company da aka bani labarin sa a Abuja ‘Moon Construction Company’ sunce zasu gama komai within a month. Ina ganin ai yayi ko? Tunda muna da kusan watanni biyu nan gaba” 

Diyam taji dadi a ranta tana jinjina hikima irin ta ubangiji. Tace “yayi sosai ma” yace “zasu turo min samples na building plans dinsu, sai mu zaba ni dake sannan sai su fara”  sun jima suna hirarrakin su sannan suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai ya cigaba da zama hannunsa rike da phone din yana kallon hotonsu shi da ita da yake kan screen din wayar, a Oxford suka dauka sanda yaje, selfie ne yayi musu suna tsaye a gaban motarta shi yana murmushi ita kuma ta turo baki tana hararar sa. Yayi murmushi saboda ya manta me yayi mata a lokacin take hararar sa kuma yasan itama kanta in da zai tambayeta ta manta. Ya saka babban dan yatsansa a hankali ya shafa fuskarta a jikin hoton sai kuma yayi sliding din hoton sama ya nemo number din one of his lawyers ya kira “barrister akwai maganar da nake so zamu yi Please, lets meet in my office in an jima. Okay, thank you”.

Diyam har ta fara sabawa da rashin Bassam a school, duk da dai kullum in ta kalli empty kujerar kusa da ita sai taji babu dadi. Sai a lokacin tayi nadamar rashin exchange din numbers da basu yi ba at least da yanzu ta kira shi tasan halin da yake ciki. And then one day, suna gab da fara exams din su sai gashi ya shigo ana tsakiyar lecture. Yayi ignoring lecturer din da yake masa kallon yazo late yana distracting din class sai ya wuce empty seat din kusa da ita ya zauna ya juyo yayi mata murmushi sannan suka mayar da hankalinsu kan lecture din da ake yi. Sai da aka gama lecturer din ya fita sannan Diyam tace masa “welcome back prince Sadiq” ya juyo yana kallon ta da mamaki dan shi dai ba zai iya tuna sanda ya gaya mata daga inda yake ba, yace “Prince? Yaushe na gaya miki haka?” Tace “ba ka gaya min ba, Aliyu told me” yace “shi din ya akayi ya sani?” Tace “okay, ba direct ya gaya min ba, kace ka taba ganinsa a gurin daurin auren yayanka a abuja last year, shi kuma yace daurin auren da yaje abuja last year na jikan sarkin Abuja ne, so, in yayanka ya kasance jikan sarki to kuwa kaima jikan sarkin ne, ko ba haka ne ba?” Ya dauke kai yace “an baki A1 a fannin bincike” tayi dariya tace “tell me everything. Dame da me ya faru? I hope komai ya warware yanzu and you are back to your old self again” 

Yace “well, bayan mun rabu naje gurin aunty Hafsat but she refused to see me. Nayi iyakacin kokari na amma abin yaci tura but sai na ci sa’a uncle Zayed ya dawo, dama yayi tafiya ne lokacin da muka samu sabani dan haka bai ma san abinda ya faru ba, I explained everything to him kuma na dauki laifina sai ya saka ni a gaba muka tafi Nigeria tare” ya danyi dariya yace “ba karamin taimako na Allah yayi ba da muka je tare dashi, da maybe in Daddy ya fara jibgata sai na kwanta a asibiti” Diyam tayi dariya tace “anya kuwa bakayi girma da duka ba?” Yace “not to my Daddy, ba ruwansa da girma na wallahi dukan tsiya zaiyi min Mami kuma ba zata hana shi ba. But Allah ya taimake ni Uncle Zayed ya shiga maganar, and my grandparents too, sai komai yazo da sauki musamman tunda na karbi laifina kuma na bada hakuri. And now Ya Ameen ne ya dawo dani tare da wife dinsa Humairah itama zata fara karatu. She is an artist, yana so ne ta samu qualifications din kawai” suka yi shiru Diyam tana tunanin ina ma dai itama nata family din zasu zama irin haka in ɗa yayi wa wani family member laifi sai iyayensa su danne son da suke yi masa su hukunta shi har ya zamanto su ake bawa hakuri ma. 

Bassam ya cigaba da cewa “Mommy, my grandma, tace wai in zabi budurwa a cikin cousins dina in place of khausar, but nace mata ta barsu duk na gode, saboda duk wadda na zaba din za’a iya forcing dinta dan a faranta min and I don’t want to end up like Saghir dinki, in zauna da matar da bata so na, so I decided zan jira, rayuwar ai yanzu ta fara ko? Zan jira har Allah ya hada ni soulmate dina da zata soni kamar yadda kike son Aliyun ki” ya karashe da sigar tsokana. Ita kuma tayi murmushi tace “ka lallaba ni in baka kanwata” yace “wacce kanwar?” tace “Murjanatu” ya daga hannu yace “no, no, no. Thank you so much but no. Wannan yarinyar samarinta sun kai cikin container”.

Suna tare har aka tashi. A lokacin ne ta bashi labarin itama cigaban da aka samu a nata bangaren, ya taya ta murna sosai da sosai sannan shima ya tambaye ta game da shirye-shiryen da take yi. Ta daga kafada tace “ba fa abinda zanyi ni, ina naga friends din ma da zan shiryawa event. Nasan dai Inna zata yi taron yan uwa da abokan arziki and that will be all” Bassam yayi shiru yana kallon ta sannan yace “kinsan wani abu? Matar yayana dana gaya miki mun taho tare zata fara school itama, zan hada ki da ita ina tunanin you two will like each other. Zaku iya zama friends” Diyam tace “no, ni bana son friendship da yayan masu kudi” yayi murmushi yace “babanta ba mai kudi bane ba, mai rufin asiri ne. Kuma bafulatana ce irin ki” tace “in babanta ba mai kudi bane ba ai mijinta mai kudi ne” Bassam yace “that makes the two of you” sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, the mare thought of Sadauki as her husband yana saka ta murmusawa.

Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki ta bashi labarin dawowar Bassam. Wannan shine dai dai saboda boye boye shi yake kawo zargi in a relationship. 

Kamar wasa sai ga Bassam ya kawo wa Diyam Humairah har gida. Sai Diyam taga cewa ashe duk abinda take tunani a game da Humairah ba haka bane ba, na farko she is young, dan Diyam tana ganinta ta san cewa ta girme ta. Ko kuma dan tana da baby face ne? Da suka zauna suka fara hira sai ta fahimci tana da saukin kai sosai da kuma addini. Ta karbi babyn da yake hannun Humairah tana yaba kyawunsa tace “masha Allah, ya sunansa?” Humairah tace “Abubakar, Ayman ake ce masa” Diyam tayi murmushi tana tuna mitar da Bassam ya taba yi akan cycling suna daya within a family. Amma ai honor ne ko? Kowa yana burin ya haihu yayi wa iyayensa takwara. 

Nan da nan Diyam ta dauko zani ta goya Ayman, tana tuna sanda Subay’a take jaririya. Wannan yasa Humairah ta kara sakin jikinta saboda hausawa sunce mai ɗa wawa ne. Sun jima suna hira, suka yi hirar similarities dinsu sannan suka yi hirar differences dinsu, a take kowacce a cikin su ta fahimci cewa tayi kawa. 

Tare suka shirya abinci sannan suka zauna suka ci a plate daya, suna cikin ci Murjanatu ta shigo tayi joining dinsu itama. A nan ne take bawa Humairah labarin cewa an kusa auren Diyam da yayanta, sai kuma hirar ta koma kan hidindimun aure da kuma zamantakewa ta aure har sai da Murjanatu ta mike tace “wannan hirar tafi karfina kar kuje ku kona ni tun kafin in tafasa”.

Komai ya tafi normal har Diyam ta kammala exams dinta, a cikin lokacin sau biyu Sadauki yana zuwa Oxford Diyam tana koro shi Nigeria saboda tace karatu yake hanata yi in dai yana can din. A dole ya hakura ya dawo Nigeria amma da sharadin cewa kullum zasuyi video call sau biyu.

Ranar da zata dawo Nigeria Sadauki ne yace zaije ya dauko ta, amma sai ya gaya wa Asma’u ta shirya Subay’a su tafi tare. Subay’a kam murna take tayi ta kasa rufe bakinta saboda farin cikin zata ga mommyn ta, dan haka bata damu bama da wate zasu tafi tare dashi. Shi ya fito da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga sannan ya zagaya ya zauna yana tsokanar ta “Subis yanzu duk wannan kwalliyar ta mommy ce? Dama ashe kin iya kwalliya haka shine ni ba kya yi min sai mommy ko?” Ta sunkuyar da kanta tace “bani nayi ba ai, aunty Asma’u ce tayi min” yace “to gaya min, me kika tanadarwa mommy?” Ta bude hannu tace “babu komai, ai ni bani da kudi” yace “to me kike so ki siya mata” tayi shiru sannan tace “sweets” yayi murmushi “wato kin san ta da shan sweet ko?” Sai tayi shiru bata ce komai ba. Yace “kina so in kai ki ki siyo mata?” Ta gyada kai kawai, sai yace “a’a, in dai kina so to sai kinyi magana da baki ba da kai ba. In kuma baki yi ba bazan siya miki ba” tace “ina so” yace “to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana” a hankali tace “uncle Aliyu” yayi murmushi ya shafa kanta yace “good girl”. 

Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace “menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?” Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace “to me kike so?” Tace “rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba” sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa “mommy tace zaka fito min dashi ko?” Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace “daddyn ki zai fito little girl. I promise you” sai kuma yayi murmushi yace “amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends” ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace “now, let’s wait for your mommy”.

Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay’a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace “I miss you so much little girl” Subay’a tace “I miss you too mommy”. Ya karaso ya tsaya a kansu yace “na gane matsayi na” ta mike tana kokarin daukan Subay’a yace “ke! Careful kar kisa a daga min biki” ta harare shi tace “wato bikinka ne a gaban ka ko?” Yace “a yanzu, yes” Subay’a tace “uncle bikinka za’ayi?” Ta fara tsalle, “zanje gidan ka inga amaryarka” ya daga ta sama yace “karki damu, kece yar zaman daki”.

Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace “ina zamu je?” Bai kalleta ba yace “kawunan ku zanje in siyar” tayi dariya “ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar” ya kalleta yace “siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay’a ta mirror yace “kinci sa’a we have company” ta murguda masa baki, yace “ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci”.

Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace “Mrs Abatcha, welcome to your home” ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace “wow” yayi murmushi yace “shall we?” Kafin ta bada amsa Subay’a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa “uncle gidanka ne wannan?” Ya fito yana cewa “gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke” sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa “Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana” Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare. 

Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za’ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay’a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace “amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa” yayi murmushi yace “am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan”.

Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari’ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta “thank you”.

Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba? 

Jin bata ce komai ba yasa yace “lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai” ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace “babu irin imagination din da bana yi that’s why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn’t know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din” Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay’a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa “thank you. Mun gode Allah ya kara arziki” baice komai ba shima yana kallon Subay’a sai zuwa can yace “zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay’a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake” ya juyo yana kallonta yace “naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa ko akasin hakan. But it is beyond me dan haka sai bayan biki”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button