GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Lumshe idonsa yayi ya kwanta a gadon dake facing din na Umaiman ya zuba mata ido yace “qanwata ce kuma matatace iyakar abinda zan iya fada muku kenan” murmushi nurse din tayi tace “kamar ku kadai ta Isa ta bayyana hakan…” banko qofar da akayi ne yasasu miqewa da sauri a tsorace ya nufi gadon da Umaimah ke kwance ya nuna Sadiya dake shigowa da hanu yace “kada ki qaraso nan ki tsaya anan wlh idan kika bari na waiwayoki zakisha mamaki idanma baki sani ba ina qara sanar dake Umaimah matata ce ta sunnah wacce take iya dauke lalurata Sadiya kiyi a hankali kada ki dauki haqqin marainiyar Allah batajiba bata gani ba wlh batada laifi saboda itama batasan da aurena akanta ba….”

“Ina ruwana Hameed kai wannan ta shafa cin amana ba ni zakuci amana saboda kai tsinanne ne mayaudari maci amana azzalumi ni zakaci amana ka fakemin da wata qaryarka wai matarka ce to na rantse da Allah ba matarka ba ko uwarka ce saina kasheta saidai Khadijah ta dawo duniya ta haifi wata kuma kaima saika tafi inda ta tafi…” Zabura tayi a guje ta nufi gadon Umaiman yayi wani tsalle ya tareta tare da riqeta ga dukkannin qarfinsa ya hankata baya ta fadi Tim a qasa kafin yayi wani yunquri ta kuma tasowa ta fakaceshi ta haye ruwan cikin Umaimah shima kanta yayi a guje ya tunkudata qasa ya zare belt din wandon jeans dinsa yace “wlh kika qara tabata sainayi miki abinda bantaba yimiki ba kashe yar mutane kikeson kiyi Sadiya me tayi miki wanne irin haukane wannan kawai don takasance matata to ki sani aurena da Umaimah hadin Allah ne haukanki bai isa ya rusheshi ba abinda yasa na boye aurannan kenan saboda nasan ke mahaukaciya ci shigowar Hajiyansa ne yasashi yin shiru da bakinsa gadan² tayo kansa kafin ya ankara yaji ta daukeshi da wani gigitaccen mari ya dafe gurin da sauri ya dago kansa yace “Hajiya…” sake zabga masa mari tayi tana kuka tace.

“dama abinda yasa ka dage sai anbaka ita kenan Hameed irin taka amanar kenan me yaja hankalinka harka lalata tarbiyya marainiyar Allah na tabbata Umaimah bazata taba banzatar da tarbiyyar da kayi mata ba saidai kai ka banzatar da taka itama ka lalata mata tata meye ribarka Hameed qanwarka ka lalata harda ciki Innanillahi wa innah ilaihir raji’un wannan wacce irin baqar rayuwace wacce irin qaddara ce Hameed da kanka da kanka ka ketama Umaimah haddi ka cucemu Hameed kaci amanar maraici bazanyi maka baki ba amma da sannu zaka girbi abinda ka shika” tunda ta fara mgnr kansa na qasa harta gama ta juya ta nufi gadon da Umaiman takekai ta ruqo hanunta cikin tausayawa tace “Allah ya isanki Umaimah Allah ya isar miki” miqewa Sadiya tayi ta kalleshi tace “zaka dawo ka iskeni har gda wlh saidai koni ko kai azzalumi”

Yanajinta amma bai iya tanka mataba harta fice zuciyarsa mugun tafasa takeyi yasan duk bayanin da zaiyiwa Hajiya bazata saurareshi ba saboda haka yaja jikinsa ya fita ya zauna a kujerar dake qofar dakin, daidai lkcn da Umaimah ta bude idonta ta saukeshi akan Hajiya ajiyar zuciya Hajiyan tayi tace “sannu kinji Umaimah” daga Mata kai tayi cikin sarqewar murya tace “Hajiya ki tafi dani gdanki Aunty Sadiya da Uncle zasu kasheni wlh Hajiya kasheni zasuyi” kama hanunta tayi tace “wa ai dama kin gama zaman tsinannen gdannan ni dama tun farko banso zamanki ba dandai wannan azzalumin ya nace ne kuma Daddyn ku ya goya masa baya yanzu ga abinda gari ya waya” kwallar dake zubo mata Hajiya ta share mata tace “kiyi hqr wlh saiya gane kuransa wannan ai zalumci ne shekaran jiya yaje yake fadamin wata shashashar mgn saboda Daddyn ku yace yabarki ki fitar da miji bayan Daddyn ku ya tashi yake cemin wai yayi miki miji ashe abinda yake nufi kenan Allah ma ya rufa mana asiri da cikin ya zube da munga ta kanmu don wannan me raayin riqau din ba bari zaiyi a zubar dashi ba macuci kawai”

Abinka da zuciyar mace duk saitaji babu dadi aibata Uncle din da Hajiya takeyi lumshe idonta tayi daidai lkcn daya dawo dakin yace “Hajiya ta farka ne?” Tsawa ta buga masa wadda tasa Umaima bude idonta tace “ban sani ba dan iska mara imani ubanka zakayi mata idan ta tashin kaga Abdulhameed idan baka fita daga rayuwar Umaimah ba wlh saina sallama ka…” kallonta Umaimah tayi taga yanda yake zubar da hawaye tace “Kayy Hajiya kibari don Allah kinga fah kuka yake don…” bige bakinta Hajiya tayi tace “eh lallai gskyr hausawa da sukace baa dan iska daya wato ke har tausayin wannan annamimin bawan kikeyi ko to zan qyaleki dashi idan ya gama daibe albarkar jikin naki a banza kya nemi tudun dafawa kuma wlh kaji na rantse saikayi dana sanin abinda ka aikata tunda kaci amana ka rubuta ka ajiye amana sai tacika”

Bai iya cewa da Hajiyan komai ba sai gaban Umaman daya matso ya kamo hanunta doke masa hanu Hajiya tayi tace “kul baka kiyayeni ba shashasha kawai babban kawai yanzu Hameed badon Allah ya duba maraicin yarinyar nan ya kawo shegen cikinnan daka kunsa mata ya zubeba daya zamuyi kenan to wlh ka fita daga idona na tsani halinka Hameed na tsani mutum maci amana baka moreba Hameed” bazai iya jure kalaman nata ba saboda haka ya juya har yakai bakin qofa ya tsaya yace “laifi nane dana boye muku gsky tun farko da ace na fada muku Umaimah mata tace da baku zargeni ba nasani Hajiya dole dama zan fuskanci wannan matsalar tunda nakasa hadiye qwalamata na sauketa akan Umaimah a lkcn da yake bai kamata ba kamata yayi ace na sanar daku matatace kafin wannan lkcn amma duk da haka inaso dake da Umaimah da Sadiya dama duk wanda yake zargina ya sani niba mazinaci bane Hajiya baki haifi fasiqi ba bantaba shuka a haramtacciyar gona ba kuma banacin itaciyar da Allah ya haramta min Hajiya koda ace ma zina nakeyi da Umaimah wannan ta faru yakama ace kuyimin uzuri nima dan Adam ne ba waliyyi bane ni inada buqatar inda zanke zuba ruwana idan na tara tun farkon aurena naso hana Sadiya aiki kukace ban isaba nasha kawo muku matsalata kuma kin kasa yimin maganinta sau nawa nazo nace muku inason qara aure amma saiku hanani kullum burinku na farantawa Sadiya wacce nine na daukota na kawota cikin family dinmu babu ruwanku da matsala babu ruwanku da damuwata Hajiya nayi hqr shekara bakwai Ina fama da matsala daya a halin inada wata matar bayan ita to me kikeso inyi idan ban nemi haqqina ba a gurin Umaimah shekara biyar tana matsayin matata ina rainonta Hajiya ko tari nake a asusun qasa yaci ace yayi cikar da idan na fasashi zai bani abinda nakeso Hajiya nasha fada miki Umaimah tanada miji kina daukan zancena wasa to ba wani bane mijinta nine matatace”

Yana fadin haka ya juya ya fice tare da jan qofar da qarfi a mugun fusace ya dauki motarsa ya nufi gdansa yana zuwa yayi parking ya nufi cikin gdan tun tsayawar motarsa tajishi saboda haka yana shigowa ta tareshi da bala’i tace “ai dama nasan dole ka dawo fasiqi la’anallahu wanda baisan Allah ba ka shammaceni Abdulhameed bantaba tunanin haka daga gareka ba saboda kaikam kwai dan akuya….” bata ida qarasawa ba ya dauketa da mari ta dafe gurin da sauri tace “kan ubancan ni ka mara Hameed tabdi wlh ka mari bala’i na rantse da Allah saika gwammace baka sa hanu ka mareni ba ihu kwarto jama’a kuzo ga kwarto Allah ya tsine maka Abdulhameed Allah ya isa tsakanina dakai azzalumi maci amana kisa tsaf saina kashe shegiyar yarinyar nan saidai idan bazata gdannan ba” murmushin takaici yayi yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button