GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da Aunty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah basu sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba.

Haka sukaci gaba da gabatar da ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace.

“Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?”

Jinjina masa kai tayi cikin kunya yayi murmushi yace “amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canza miki raayi ba?” Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace “naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wucce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah”

Dagowa tayi da sauri tace “aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba” kallonta yayi da sauri yace “meyasa?” Qasa tayi da kanta tace “Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba”……..

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/23, 4:34 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace “shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba amma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya ba”

Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice.
A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kanta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan department din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi aranta Saudat Alfah itama sabuwar daluba ce matashiya meji da gayu da tsayuwar naira a jikinta tunda ta shigo makarantar Allah ya hada jininta da Umaimah itama sanadin Shurafah Saudat Alfah itama matar aure ce da yaranta biyu tana auran wani custom tun Umaimah na janyewa abotar tasu harta saki jiki suka zama abokai sosai ita Saudat namiji take goyo Sudais kusan saanni ne da Shurafah.

Semester ta fara nisa sosai su Umaimah yan makaranta itadai karatun kawai tasa a gabanta amma rabin hankalinta yana wajen su Daddy da kullum sukayi waya saidai yace musu jiki yana kyau sosai a haka har suka cinye semester sukayi hutu a cikin hutun ta takurawa Daddy kan cewa tanaso taje ta gano jikin Hameed Daddy yaso hanata zuwan amma yanda yaga ta damune yashi dole ya qyaleta dake ya dawo dazai tafi suka tafi tare.

Kai tsaye asibitin da yake suka nufa suka shiga dakin tana rungume da Shurafah tunda suka shigo ya Hameed dake zaune jingine da matashin kai ya ya zubawa Umaimah ido ya kasa ko qiftawa sai yawo yake da idanunshi akanta kamar wanda ya warke daga ciwon makanta ajiyar zuciya ya sauke ta dago kanta da tayi qasa dashi tun kallon farko da sukayima juna idonsu ya qara sarqewa da juna a hankali ya daga hanunsa ya miqa mata alamun yana buqatar tabashi wani abu.

Cikin sassarfa ta qarasa gabansa ta dora masa Shurafah a jikinsa ya qurawa yarinyar da itama shidin take kallo ta qura masa ido sai bangale masa baki takeyi shima murmushin shima yayi mata tare da dagowa ya dubi Umaimah da taketa kallonsa ya rame sosai hancine kawai da ido sai dan qaramin bakinsa da yake motsawa a hankali alamun magana yakeson yi mata amma muryarsa bata fita sosai.
Shigowar Daddy da likitocin ne yasata neman guri kusa dashi ta zauna a sanyaye taji ya ruqo hanunta ta dago da sauri suka hada ido ya lumshe nasa a hankali ya bude tare da cewa “Kina kulamin da Shurafah yanda ya kamata kuwa?”

Yayi mgnr da murya me rauni a salube ta jinjina masa kai ya janye hanunsa daga nata tare da cigaba da kallon yarinyar yanajin qaunar da baitabaji akan sauran yayansa ba game da yarinyar dagata yayi a hankali ya dorata a qirjinsa.

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/23, 8:05 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: G.U

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Likitan ne ya dubi Daddy sukayi larabcinsu ya miqawa Hameed hanu sukayi musabiha suka juya suka fita Daddy ya dubesu yace “zuwa sati idan ka qara warwarewa saimu tafi gda ko babana?” Lumshe idonsa yayi ya bude Daddy yayi murmushi yace “gadai Umaimah tazo ta kawo maka Shurafah nima hankalina ya kwanta yanzu zamu iya tafiya”

Daddy ne ya taimaka masa ya miqe kasancewar komai a asibitin ake masa babu abinda suka dauka sai kayansa yana rungume da Shurafah Daddy yana riqe dashi haka suka fita motar asibitin ta daukesu zuwa masaukinsu dakin da Daddy ya kamawa Umaimah nan yakaiwa Hameed kayansa ya juya ya fita ya barsu su biyu zama yayi a gefen gadon yana binta da shu’umin kallonsa me kashe mata jiki bata iya ce masa komai ba sai neman guri da tayi ta zauna a saman resting chair din dake gefen gadon ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kansa daga kanta yace.

“Ina buqatar zan kwanta na huta” da sauri ta dubeshi ya sake kawar dakai yace “ina nufin Ina buqatar privacy zaki iya fita kice da Daddy ya kama maki wani dakin” dagowa tayi zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace “banason surutu kuma banason takura kitashi kije ki kwanta dare yayi”

Jikinta a mugun sanyaye ta miqe ta nufi gadon idanunta ya ciko da hawaye ta sunkuya zata dauki Shurafah ya daka mata wata tsawa data sata saurin yin baya yace “get out for my room” da sauri ta juya ta nufi qofar dakin ta bude a tsorace ta fice daga dakin.

Miqewa yayi ya kwantar da Shurafah dake bacci yasha magungunansa ya kwanta tare da janyo yartasa a jikinsa da haka bacci ya daukesa.
Umaimah kam a tsayawa tayi jikin qofar dakin zuciyarta nayi mata wani zafi da ciwon irin korar da yayi mata takeji wai ta fice masa daga dakin wasu hawaye ne masu zafi suka ziraro mata ta zauna a parlourn saman carpet zuciyarta nayi mata suya wannan ko wanne sabon wulaqancin rashin lfyr tasa tazo masa da ita oho.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button