GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

“To dama wanne tsautsayine zai dawo da ita ta zauna dake itama ta samu yanci bautar da tayi miki a bayama ta rainon yayanki da kula miki da gdanki kina gantalin yawon aikin banza ta isa yanzu lkcn kula da mijinta ne itama da ita ta shayar dashi farin ciki tayi masa maganin matsalarsa dake kika kasa ta bashi lkcn da kika kasa bashi kinga dama jinin dake yawo a jikinta shine a jikina ita zata iya dani tunda irinmu daya bazata gaza kamar yanda kika gaza ba tana da dadi sosai” yana gama fada Mata ya shige dakinsa ya datso qofar yanajinta tana dukan qofar kamar zata balleta tana kiran sunansa harda na iyayensa tana qare masa zagi tare da tsinuwar diban albarka a haka yaran suka shigo gdan driver yaje ya daukosu suna shigowa dakin Umaimah suka nufa suna kiran “Aunty mun dawo zo kiga assignment dinmu ki kawo mana dakin ta nufa kamar mahaukaciya ta finciki charge dake jikin surket ta rufesu da duka kamar Allah ya aikota tana zaginsu tana fadin “dagaku har uban naku kutumar ubanku zanci ita ta haifamin ku tsinanniyar yarinyar da take neman rabani da ubanku to wlh duk shegiyar yarinyar dana sakejin ta kiramin sunan yarinyar nan sainaci wancan kwarton mazinacin fasiqin uban naku” yanajin irin tujarar da takeyi yasan duk dan ya kulata ne don haka ya bawa banza ajiyarta.

Sai yamma liqis ya fito daga dakin yana daura agogo bata parlourn sai yaran suna zaune sai matsar hawaye sukeyi Nihal ce ta taso ta rungumeshi ta sake fashewa da kuka tace “Uncle me Aunty tayiwa Mom take zaginta kuma yau da safe bata bamu abinci ba da zamu tafi islamiyyah sai bobbo da biscuit Uncle yunwa mukeji Maliha har kuka ta rinqayi a makaranta saida Mu’allimah ta siya mata cheese sannan tayi shiru” ransa ne yayi mugun baci wai kamarshi ace yayansa suna fita basu karya ba kawai saboda sakacin uwarsu kama hanun yaran yayi yace “kuyi hqr Auntynku batada lfy tana asibiti kuzo muje kuganta sai kuci abinci acan” murna suka hauyi da tsalle da kansa ya cire musu kayansu yasa musu wasu ya jasu suka fice daga gdan suna zuwa asibitin ya nuna musu dakin suka shiga da gudu lkcn an cirewa Umaimah roba ta biyu ta jinin tana zaune ta jingina da pillow da gudu suka nufeta suna murna suna tsalle itama taji dadin ganin yaran saboda ta saba dasu koya ta yini bata gansu ba sai taji babu dadi haurawa sukayi saman gadon suka rungumeta Maliha tasa kuka tace “Aunty shine jiya Uncle ya daukeki kika tafi kika barmu kikaqi dawowa kiyi mana break yau sai haka muka tafi bamu karya ba nayita kuka a makaranta inajin yunwa” Nihal ce me wayo tace “Aunty kin rame kinyi fark meye yake damunki aka kawoki asibiti?” murmushi tayi vta shafa kansu tace “banida lfy ne amma naji sauqi da ganinku kunajin yunwa ko?” Daga Mata kai sukayi tace “no wonder indai yarana sunajin yunwa Ina ganewa Hajiya dake zaune tana kallonsu tana murmushi tace “kaji yan jakar uba ina iyayen naku da suka barku da yunwa” kawar dakai Umaimah tayi tace “mudai ki bamu abinci yarana suci Hajiya idan sunci sayi miki bayani” Nihal ce tace “mu Mom dinmu bata sonmu yau ma duka tayi mana saboda mun tambayi ina Aunty”

Daidai lkcn ya turo qofar ya shigo tare da sallama dago kanta tayi da sauri idonsu ya sarqe guri guda yanayi mata kallonsa me narkar da zuciya murmushi yayi mata tare da ajiye kayan daya dauko mata da shopping din da yayo yace “Hajiya sannu da qoqari yame jikin?” Ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa abincin ta zubo jallop din shinkafa ce data wadatu da alayyahu da kifi banda sai qamshi takeyi ta miqawa Umaimah ta karba tare da zaunar da Maliha ta fara basu abincin a baki sunata zuba mata santi itadai batace musu komai ba saboda yanda takejin qwayar idonsa na yawo a jikinta muryar Hajiya ce ta katseta tace “idan kaga dama kaje Daddyn ku yana nemanka yanzun nan ya fita zashi gdanka” amsawa yayi da “to” ya miqe yace bari naje na biyasu kudinsu na dawo dakatar dashi Hajiya tayi tace “aa aikai ka gama aikinka saura namu ubanka ya biya komai” dagowa yayi da sauri ya kalleta yace “amma Hajiya…” Dakatar dashi tayi da cewa “karkace min komai Hameed wlh da zaka yarda ma daka daina zuwa inda nake saboda idan na ganka jinake kamar na kasheka”

UMMUH HAIRAN CE…✍????

????RILLIANT WRITERS ASSOCIATION ????
( Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)

GIDAN UNCLE
( Love and romantic story)

SHORT AND TRUE LIFE STORY

MALLAKAR
????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
®FAUZAH

Wattpad???????? realfauzah

www.fauzahtasiu41@gmail.com

Alhmdllh a madadina da iyalaina munayiwa daukacin al’ummar duniya barka da shiga sabuwar shekarar gogerioun calendar duk da dai mu munci wata hudu a tamu ta musulumci Allah ya hadamu da alkhairan cikinta sharrikan dake tattare da ita Allah ya kade manasu yanda muka shigeta lfy Allah yasa muga qarshenta lfy idan kuma bamu da rabon gani to Allah ya karbi ranmu muna cikin musulumci muna masu aikata ayyukan alkhairi sannan yasamu a ceton Muhammadur rasulullahi (S.A.W).

PAGE ELEVEN

A salube yake kallon Hajiya lallai ta dauki lamarin nan da zafi saboda tunda yake da ita ko baqar mgn bazai iya tuna ranar data fada masa ba amma yau gashi tana neman tsine masa, cikin rashin qarfin gwiwa ya matsa jikin gadon na Umaimah yace “sannu Babyn Uncle ya jikin yanzu inane yake miki ciwo?” ya fada yana dora hanunsa a saman kanta ajiyar zuciya sukayi a tare cikin sanyi muryarta tace “da sauqi” murmushi yayi yace “ok kuzo mu tafi kada ku dame Aunty kunga batada lfy ko?” Nihal ce tace “Mudai anan zamu zauna gurin Aunty da safe ta dafa mana tea tayi mana wanka” Maliha kam kuka tasa wai a dole bazata koma gurin uwarta ba.

Daqyar ya shawo kan yaran suna kuka suna komai yajasu suka fice daga dakin itama Umaimah gawayen ta share batason ko kadan taji yaran suna kuka jinshi take har cikin lakarta, Hajiya kam haushine yakusa kasheta ita a tunaninta mgnr data fadawa Hameed dince tasa Umaimah kuka.

Kwanansu daya a asibitin yazo da safe dazai tafi aiki ya dubata ya jima sannan ya tafi office a CBN Kano yake aiki, bayan tafiyarsa babu jimawa Dr Saleem ya basu sallama suka tafi gda yayar Hameed Aunty Zarah tazo gdan saboda Hajiya ta kirata ta zayyane mata komai suka hadu a parlour sukayita Allah wadarai da abinda Hameed yayima Umaimah abin takaicin harda Daddy shima ya biye musu yace “wlh badon Hameed dana bane babu yanda zanyi dashi dasai nayi qararsa an fiddawa marainiyar Allah haqqinta jiya fah tsabar ya rainamin hankali na kirashi inayi masa fadan kuskuren da yayi sai cemin yayi shifa baiyi wani laifi ba Umaimah matarsa ce laifinsa daya daya boye mana gsky danaji rainin hankalin nasa yayi yawa sai nace ya tashi ya bani guri kawai saiya fashemin da kuka waishi ba mazinaci bane idan bamu yarda da abinda ya fada mana ba mubashi dama ya gabatar da wasu daga cikin shaidun da suka shaida daurin auransa da Umaimah fada na haushi dashi kamar zan cinyeshi amma bai fasa fadamin ba shifa matarsa yayi mu’amala da ita ba wata ba har yana neman yimin rashin kunya wai gobema idan yana buqatarta zai nemeta yayi duk abinda yaga dama da ita tunda shi yasan ba zina yakeyi ba saboda haka Hajiya sai kinsa tsaro sosai akan yaronnan saboda idan kikayi sake zaa samu matsala tabbas shima mgnrsa abar dubawa ce saboda haka zanyi binkice sosai kuma nace ya gabatar min da shaidunsa nanda kwanaki uku idan ba hakaba zan sauki matakin shari’a akansa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button