GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kama hanunta Sa’ud tayi cikin hawaye tace “Sannu bloody kiyi hqr ki daina kukan nan kowanne bawa baya wucce qaddararsa kinji” bude idonta ta rinqayi a hankali harta saukesu tar a fuskar Sa’ud idanunta naci gaba da malalar da hawaye tace “ina Uncle Hameed Sa’ud wanne hali yake ciki ya mutu ko?” kada mata kai tayi tace “yananan Umaimah bazai mutu ba insha Allahu” lumshe idonta ta kumayi daidai shigowar likitan ya fara dubata yace “alhmdllh jiki yayi kyau sai fatan Allah ya mayar dana aika” bude idonta tayi da sauri da tsananin mamaki tace “kamar yafa ban gane ba?” shafa gashin goshinta Sa’ud tayi tace “damuwar da Hajiya ta jefaki a ciki ce tayi sanadin zubewar cikin jikinki Umaimah…” Miqewa tayi a tsorace tace “da gaske ya zube shima Innanillahi wa innah ilaihir raji’un shikenan farin cikin Uncle ya zube meyasa ya zube Dr inason cikina yanzu shikenan nayi biyu babu ba ubansa babushi”

Tausayinta ne ya cika zuciyar Sa’ud ta kamota ta miqe tace “insha Allahu komai zaizo qarshe Bloody nasan akwai ciwo a rabaka da mijinka batare da neman shawararka ba amma babu komai akwai Allah kuma Ina tabbatar miki Hameed bazai iya rabuwa dake ba saboda kece kadai zaki iya zama dashi ki biya masa buqata yanda yakeso kuma ya samu gamsuwa dake ???? saboda haka karma ki wani damu tunda kinji qwari tashi mu qarasa gda kiyi wanka mu nemi abinda zamuci kinji” shidai likitan binsu kawai yakeyi da kallon mamaki “dama matan aurene ku?” Yakasa jurewa ya tambaya kallonsa sukayi a tare Sa’ud ce tayi qarfin halin cewa “eh Hussaina tace am don Allah Dr mace da aka saketa da ciki kuma cikin ya zube matsayin iddarta yake a musulumci?”

Shafa kansa yayi sannan ya zauna yace “ma’anar iddah tana nufin tsarkin mahaifa tsarkin mahaifa kuwa shine yin jini bayan rabuwar aure to wacce aka saketa da ciki kinga bazatayi jini ba harsai ta haihu shiyasa iddarta take da wahala bayan ta haihun da zarar ta haihu to iddarta ta cika ko ranar zaa iya daura mata aure kinga kenan a shari’ance matar da aka saketa da ciki tayi bari koda a ranar da aka saketa ne to ita ta tsarkaka wannan shine amsarki a taqaice wallahu wa rasulihi aalam” yana fadin haka ya miqe ya fita tare da basu sallama Sa’ud ta kama hanunta suka fita a sanyaye jikin Umaimah yake ji takeyi dama zata iya mayar da cikinta jikinta jikinta yanzu shikenan ta fita daga sahun matar auren Abdulhameed?

Wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaro mata da haka suka shiga motar suka nufi cikin unguwar sunyi tafiya me dan tsayi sannan sukayi parking jikin wani dan matsakaicin flat house me kyau saida Sa’ud ta tabata sannan ta dawo hayyacinta ta bude mata qofar ta fito tana daga qafarta daqyar ta nufi qofar da taji Sa’ud din na budewa ta bude mata ta shiga tanabin gdan da kallo wata qofar taga tasa key ta bude nanma Umaimah tasa qafarta ciki wani sanyi da qamshi me dadi ya daki hancinta ta lumshe idonta duk da zuciyarta babu dadi amma taji dadin qamshin ta bude idonta tanabin parlourn da kalloh yayi kyau sosai sai qofofi guda uku da suke a kulle, zubewa tayi a saman kujera tana sauke ajiyar zuciya tanabin parlourn da kallo amma gaba daya hankalinta na wajen Uncle dinta “ko wanne hali yake a ciki?” Abinda ta tambayi kanta kenan.

Tana zaune Sa’ud din ta shigo ta cire hijjab dinta tana murmushi tace “tashina kenan daga bacci kika kirani kinga ko rigar baccin ban cire ba na zari hijjab na fita” kawar da kanta tayi gefe saboda batason hayani ko surutu itama bata qara yimata mgnba ta bude daya cikin qofofin ta shiga bata jima ba ta fito ta bude dayan dakin tace “bloody ki shiga ki kwanta kafin na sama mana abinda zamuci nasan zuciyarki tana cike da zargi na da tarin tambayoyi akaina da kuma tunanin meyene yasa na daukoki na kawoki nan to kiyi hqr zan baki amsa nan da yan mintuna”

Tana gama fada mata haka ta riqo hanunta suka shiga dakin data bude mata mamaki ne ya cika zuciyar Umaimah ganin dakin a shirye tsaf kamar na matar aure gado wadroop madubi da bedsat komai dai akwai sai wata qofa da take nuna alamun bathroom ne qarewa dakin kallo tayi kafin ta zauna a gefen gadon ita kuma Sa’ud ta fita ta shiga daya qofar ta fara hada musu abinci.


Kusan awansu hudu da zuwa asibitin amma har yanzu bai farfado ba ko numfashi baya iyaye saida taimakon na’ura daga Hajiya har Aunty Zarah ba qaramin tashi hankalinsu yayi ba sun ma manta da baiwar Allah Umaimah da halin da zata iya shiga sai kaiwa da komowa sukeyi tare da likitocin a haka har dare yayi sai goma saura Zarah ta dubi Hajiya tace “Hajiya wai meye yayi coorsing din matsalar nan ne Ina matansa da banga kowacce a gurinnan ba?”
Gaban Hajiya ne ya fadi ta miqe da sauri tace “na shiga uku na Zarah amanar Allah wlh na manta da ita” tana fadin haka ta fita da sauri ta tari dan sahu ta nufi gdan tun daga parlourn ta fara ganin gdan a hargitse dakinta ta nufa tana qwala mata kira amma shiru tura kanta tayi a dakin ta fara dube² amma babu alamar mutum a gurin kunna light din dakin tayi idanunta ya sauka akan inda Umaiman ta zauna dazun taga yanda jini ya bushe a gurin da sauri ta shiga ta banka qofar bandakin amma babu wata alama ta an shiga toilet din sake fita tayi tana kalle² a parlourn sai yanzu idanunta ya kai kan Nihal da Maliha da suke kwance a qasa kan tiles suna bacci matsawa tayi da sauri gurinsu tana haskasu fuskarsu duk tayi jirwaye da alamun kuka sukaci har sukayi bacci hankalinta ya dada tashi ta nufi wajen gdan ta fara qwalawa me gadi kira ya iso da gudu ya rusuna tace “ina Umaimah?”

Da sauri ya kalleta yace “banganta ba nidai bayan ansa yallabai a mota kun tafi naga wata motar tazo amma banga wanda ya ke ciki ba kuma bata dade ba ta fita…”bata tsaya bata lkcn sauraron shirme ba ta juya gdan tana safa da marwa itakam taga ta kanta da yaran daga nema musu sauqi ta jangwalo fitina yanzu ina Umaimah ta tafi wata sani a garin wa take dashi a garin bayan su da zata wajenshi ta zauna? Tambaya ce mara amsa Hajiya take yiwa kanta har tana runtuma tuntube saboda tashin hankali.
Debe yaran tayi ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu ta kuma shiga dakin Umaiman itace leqe har qarqashin gado miqewa ta kumayi tana rarraba idanu ya shege a rabon gado sai yanzu ta lura ma duk wani abu da yake mallakin Umaimah babushi a dakin zubewa tayi a qasa tana karanto Innanillahi wa innah ilaihir raji’un kanta yana wata muguwar sarawa a fili tace.

“Na shiga uku ni Zulaiha yau naga bala’i me hakan yake nufi Baby ta gudu saboda na rabata da abinda zai cutar da ita? Allah ka sani bada wata muguwar manufa nayi hakan ba Allah naji tsoron kada yaron nan ya hallaka ta ne Allah ka fitar dani kunyar duniya ka jefa marainiyar ka hanu na qwarai” tana maganar tana kuka me ban tausayi wayewar garin yau tayi danasani tafi dari tilon danta yana kwance baisan inda kansa yake ba ga marainiyar Allah ta gudu “wallahi saboda ni bazaka rayu cikin tsinuwar mahaifiyar kaba Hameed ka sakeni saika sakeni Hameed ba wannan dalilin ne kadai yasa takeson ta rabamu ba akwai wani qulli a zuciyarta…” kalaman Umaiman ne suka rinqa dawo mata tare dana Hameed din lkcn da yake kuka yana cewa “ki barni na rayu da farin cikina Hajiya nayi miki alqawarin bazan qara kusantar Umaimah ba har abada Hajiya ita kadai ta ragemin wadda takejin tausayina Hajiya kada ki rabamu tana sona kuma kema shaida ce inasonta babu wanda ya isa ya raba tsakanin hanta da jini…..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button