GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Durqushewa yayi jikin qofar yana kiran sunan Umaimah sai yanzu yaji wasu zafafan hawaye sun zubo masa ya dade a gurin ganin babu wanda zai fito daga dakin yasashi miqewa jiri na dibansa ya fita ya fada motarsa yaci gaba da kukansa yana buga kansa da sitiyarin motar jin abin yake kamar almara wai shine ya saki Umaimah saki har biyu to me tayi masa meye ya hadasu yaushe ma yayi sakin kuma yaushe ya rubutashi kai ina bazai taba yarda ba wannan gonarsa akeson shiga ayi masa barna.

Daqyar ya iyajan motar ya nufi gdan abokinsa Yusuf dake asabar ce yana zuwa ya tarar dashi tsaye tare da megadi mamakine ya cika Yusuf saboda rabonsa da Hameed tun lkcn daya fada masa zai auri Salmah ya fito ya nuna masa bai amince ba so ko waya basayi kamar aikin asiri ya daina kulasa ko wayarsa ya daina dagawa.
Takawa Yusuf yayi har motar ya bude ya shiga yace “yadai mutumin yau amintakar ce ta motsa asirin ya sakeka kenan…”hadiye mgnr yayi ganin yanda jikinsa yake bari haqoransa suna haduwa ya damqi hanun Yusuf yace “Yusuf wai su Daddy ne sukace wai nine na saki Umaimah da hanuna jiya da daddare har saki biyu yanzu shikanan bloodyna ta haramta gareni….”

A tsorace Yusuf ya dago yace “kamar ya wai akwai wanda ya isa yace ka saki matarka idan baka saketa bane?” Cikin fitar hayyaci yana qara dafe qahon zuciyarsa yace “ru…rubutu nane a jikin takardar amma wlh tallahi bansan yaushe na rubuta ba Yusuf nasani kai zaka gasqatani wlh inason matata bazan taba iya rubuta mata saki har biyu ba yama zaayi na saki Umaimah har saki biyu bayan nasan rabuwa ce ta qarsh….”

Bai iya qarasa mgnr ba saboda numfashinsa da ya fara sarqewa ya fara kokawa dashi tare da danna qirjinsa da sauri yace “kaini gda Yusuf maxa kaini gdana na mutu a dakin Umaimah Yusuf mutuwa zanyi….”

Yana fadin haka ya fara kakarin amai kafin kace meye wannan ya balle murfin motar ya fita ya durqushe a qasa ya fara sheqa aman jini tashin hankalin da Yusuf ya shiga ba kadan bane ya fito ya rirriqeshi yana jijjigashi yana cewa “dama saida na fada maka kada ka auri Salma bakai takeso ba farin cikinka takeson rabaka dashi kaqi ji yanzu ga irinta nan ta rabaka da matar da kakeso kuma Kai dama ba cikakkiyar lafiya ba idan ka mutu ai kowa ma ya huta saki kuma ya saku tunda harka ambata sunan Umaimah a takardar kuma ka dawo hayyacinka ka gani da idanunka Hameed da ace bayan kayi sakin baka dawo hayyacinka ba har kowa ya fahimci baa cikin hayyacinka kayi sakin ba da kana da damar dawo da matarka saboda babu alqalami akanka lkcn da baka cikin hayyacinka amma dawowarka cikin hayyacinka da wuri da kuma karbar takardar ka duba shine ya tabbatar da sakin Hameed Umaimah ta saku kuma ta haramta gareka harsai taje ta auri wani mijin yayi mu’amala ta aure da ita tukunna ta halatta gareka….”

Duk da azabar da yakeji a qirjinsa hakan bai hanashi daga masa hanu cikin azababban kishi ba yace “wlh aa ne babu namijin dazai shiga jikin Umaimah saidai dukkanmu mu mutu babu aure ka kaini gdana nace kada na mutu anan…..” Yana mgnr yana qara qanqame qirjinsa kamashi yayi ya taimaka masa suka shiga motar yaja suka fita ya juyo yace “amma da asibiti muka fara zuwa” daga masa hanu yayi yace “bazani ba gda nakeson zuwa nafiso na mutu na huta meye amfanin rayuwata babu Umaimah” bai sake masa mgn ba saboda yasan tunda ya musa to bazaiyi ba horn yayi a qofar gdan suka shiga ya dauki biro da takarda ya rubuta rubutu kamar haka.

Qaddarar ki rabani da farin cikina ya hadani da baqar ashana irinki wlh baki isa kici gaba da zama dani ba ni Hameed na saki matsiyaciyar mace irinki Salma saki uku”

Yana gamawa ya bude motar ya fita da sauri a duqe yake tafiyar har ya shiga cikin bangaren Salma ya danna kai ya shiga qanwarta ya gani a parlourn baiko kula gaisuwar da takeyi masa ba ya shige dakinsa ya zare wata qatuwar belt a jikin wandonsa ya bude qofar ya nufi dakinta ya tarar da ita kwance ta baje gindi tanashan iska ya kawar dakansa tare da sanyawa dakin key ya fusgota daga gadon ya fara nada mata na jaki kamar mahaukaci tun tana ihu da dasasshiyar muryarta da kukan neman daukin daran jiya ya qarar da ita harta daina motsi bai daina jibgarta ba yayi mata fata² da jiki sannan ya cilla mata takardar yana haqi yace aje aci gaba da zawarci Hameed yafi qarfin ki la’anallahu”

Bude qofar yayi yana budewa yaga uwarta a parlourn ko kulata baiyi ba ya fice jiri na dibansa ya nufi inda Yusuf yake jiransa a mota amma kafin ya qarasa ya yanke jiki ya fadi da sauri Yusuf da megadi suka nufoshi suka rufar masa Yusuf na danna masa qirjinsa yana kiran sunansa wayarsa ya zaro a kidime ya kira layin Daddy bugu daya aka daga yace “Daddy Hameed ne bashi da lfy muna gdanshi ka Kira likita akwai matsala”
Yusuf yana aje wayar suka kinkimeshi suka nufi bangaren Umaimah dashi suka kwantar dashi a parlour sai gumi yake hadawa zuciyarsa na bugawa da qarfi baafi minti ashirin ba Daddy ya shigo shida Dr Saleem wata Allah ya fara yimasa sannan suka fita dashi zuwa asibiti suna zuwa aka shiga dashi aka fara bashi taimakon gaggawa wannan karon bai shiga commer ba amma baisan inda kansa yakeba…….

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[1/31, 2:24 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GU

Gumu tayi gumu hankalin wannan family ya tashi wannan karon lamarin yafi qarfin fushi saidai addu’a saboda Hameed yana asibiti Umaimah ma tana asibiti har satin suna ya zagayo duk inda taso cirewa kanta damuwa da soyayya gami da tausayin halin da Abdulhameed yake ciki ta kasa saboda a jininta yake ji takeyi kamar ta cire ciwon ta mayar jikinta duk da a cikin qahon zuciyarta tanajin ciwon cin mutuncin da yayi Mata a daren da tafi buqatar taimakonsa da kusancinsa a daren ya yanke shawarar datse igiyoyin aurensu saida tayi sati biyu tana jinyar rabuwa da masoyinta a asibiti kadan ya rage itama zuciyar tata ta harbu amma jininta in yana kaiwa dubu ma to ya kai ga kuka babu dare babu rana tazama kamar zautacciya duk wata kalmar bakinta bloody ko ya jiki kace mata to amsarta bloody.

Hakan ba qaramin daga mawa su Hajiya hankali yayi ba kakace taga abin na Umaimah ya zama kamar tabuwar qwalwa hakan yasa tasa aka sauke mata qur’ani sannan akayo mata rubutun dangana aka rinqa bata tanasha satinta uku da haihuwa suka koma makaranta sabuwar motar da Hameed ya siya mata wacce yace itace gift dinta ta haihuwar Shuraif ita Daddy ya bata take zuwa makaranta da ita kamar yanda ya kafa mata doka har yanzu haka take bata fasa ba niqaf ne kawai bata sawa saboda dama a dole take sanya shi saboda farin cikinsa.

Saida yayi sati biyar a asibitin yana jinya sannan ya fara samun kansa shima da sunanta ya tashi a bakinsa Hajiya tana tausayawa dan nata tasan kafiyarsa shima da rubutun zatasa ayi masa saboda tasan akwai badaqala a gaba.
Haka suka koma gda dashi duk yawan gdajensa amma yaqi komawa ko daya daga ciki shima dakinsa tunna samartaka yasa Daddy dole saida ya gyara masa ya koma cikinsa sai lkcn ne Hajiya ta samu damar zuwa ta debowa Umaimah kayanta tsaf shikuma yasa gdan a kasuwa saboda ko gdan bazai qara zuwa ba balle ya tuna da baqar rayuwa da baqar ranar data riskesa a gdan ranar dabai taba tunanin zuwanta ba a rayuwar aurensa da Bloody dinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button