GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????writting by
~Binta Umar~
~[MAMAN ABDUL WAHABU~]

~Mrs Ahamad gwadabe~

Bissimillahi rahamanir rahimi

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

~WANNAN LITTAFIN QAGGE NE DA GA NI BINTA WANDA YAGA YAYI DAIDAI DA RAYUWARSHI A RASHIN SANI NE~

~_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATA SAI KAYI MAGANA~
08089965176

INA ALFAHARI DA MASOYA NA MASU SON RUBUTU NA ALLAH YAKARA KAUNA TA DAN ALLAH????

ban yadda wani ko wata ya joya min littafi ba batare da izini na ba Ayi hattara

~DEDIGATED TO: MY FAN’S~

????1

Ba kajin komai a gurin sai busa gami da sarewa da sawun doki kowa a gurinshi kokari yake yaga wucewar sarki Almustapah ma Adalin sarki kenan Wanda Al’umarshi take jin dadin mulkinshi gami da Adalcin A tsakanin talaka da mai kudi babu Wanda ya ware a ciki kowa nashi ne ,

Gurin ya karade da hayaniya can jama’ar dake gurin suka fara jiyo wata Murya cikin Lasifiqa Ana cewa jama’a Ku dakata Ku nutsu kafin fitowar mai martaba sarki mai Adalci yanzu Yarima Mai jiran gado zai fito tare da ta wagarshi Allah yaja da ran Yarima Almansor takawar ka Lafiya ,gaba salamin baya Salamun Dan sarki jikan sarki sarauta gadarta kukayi bata haya bace wannan tsantsan tace a jini take

Ba fade sai faman zabga kirari yake yi har yanzu bamuga fitowar Yarima Al’mansor ba ni kaina na qago in ga waye wannan Yarima n ,da ake tai wa kirari haka lailai sarauta ikon Allah masu Abu da Abunsu!

Bakin shi yaqi yin shiru har ila yau zabga kirari yake gami da banbadanci ga Yarima Amma shiru kakeji tamkar an shuka dosa Wanda a keyi dominshi babu Alamarsa,

Wani mugun tsaki Balaraba taja A fili tace Aikin banza Kawai Mtsss gaskiya wannan ma Dan rainin hankali ne kawai ya fito shine sai ya tsaya bata mana lokaci dubi fa time tafada tana kallon Agogon dake daure a hannuta gami da kallon kawarta Bushira wacce suke zaune a tare A wata katuwar rumfa cikin “yan Uwansu dalibai da’Alama Saukar Alk’urani Sukayi ganin tarin Alluna gami da kyauttuka a zube a gurin,gefen maza daban na mata daban hakanan gurin zaman malamai daban ,gurin zaman iyayen yara daban gurin zaman manyan baki daban ,sai wani guri keban tacce Wanda a ka tanadar wa da mai martaba domin zama shida Mai jiran gado Wato yarima gurin yasha shinfidu iri iri na Alfarma ga wasu bayi biyu a tsaye a bayan kujerun hannuwansu riqe da wasu tafka tafkan mafitai suna fiffita tun kafin Masu sarautar su zauna a gurin,

Bashira tace wallahi kuwa dama naji rade radin cewa ae mugun girman kai ne dashi Yariman shiyasa ban so Malam Idiris ya kawo saukar fadar sarkin ba yafi kawai dacewa sarkin yaro makaranta mu karbi Allunan mu sabida kin San sha’ani da masu sarauta a kwai matsala ,

Tsaki Balaraba tayi a karo na biyu cikin gadara tace wallahi Dan kar in tashi in yi tafiya ta Abin ya zama laifi gurin Malamai dama mutum yayi kaurin suna komai sai ace kai ,da tafiya ta zanyi babu wani banzan da zan tsaya batawa kaina lokaci a kanshi sauka ce dai nayi nasan nayi ae ba lailai bane sai na karbi Allon ba,

Ke Balaraba! Bushira tafada cikin mamaki tace kardai maimar taba kike zagi kin San dai nan ba gurin gadara ba ne gami da girman kai Dan haka ki iya bakinki,wallahi ,kasa kasa Balaraba ta karashe zancan tana waiwayawa bayanta domin dogarawa ne ke waye dasu ko wanne riqe da gora Kansu yasha tafka tafkan rawani idonsu ranbade da kwalli sai zarewa sukeyi

Babu wani tsoro ko kadan a Furucin ta tace ke rabu dani Dan Allah shikkenan sai in zauna a kan wani ina batawa kaina lokaci sanin kanki ne fa su Sadiya suna can na jira na kin san basu da kowa sai ni nasan suna can a takure ,shikkenan sai in zauna wani ya bata min lokaci,nifa ba da sarki nake ba,ke kin San da Wanda nake yi tafada tana wani ciccije baki!

Bushira tace wallahi balaraba ki rage wannan zafin kan naki sai ki riqa Abu cikin gadara tamkar wata “yar wani ki yi tunanin nan fa gidan masu mulki kika shigo wallahi ni dai babu ruwana to!!

Mtsss ke nifa wallahi babu Wanda zan ji tsoro uwata da ubana kawai zan ji tsoro sai Allah da Annabi Amma babu wani mahalokin da ya isa yana kashi ina kashi in ji tsoro ni babu ruwana da wani sarautarsa,

Shiru Bushira tayi ganin Balaraba tana faman daga murya dama dama tayi kaurin suna a makarantar ,bata karacewa mata komai ba,

Can suka kara jin busa gami da sarewa wannan bafaden dake tsaye bakin katowar kofar da Mai martaba za fito yayi saurin zubewa a gurin kanshi a qasa gami da dunqule hannunshi Alamar jinjina, cikin banba danci yace Allah yaja da ran Yarima Almansur sarki mai farin baya baka fito ba sai da ka shirya mai takalmin karfe wannan haka yake sarautar ma suna taci in kana guri ,Dan gidan Fulani Dan gidan zainaba Dan gidan Fadim……

Tsitt! Bafaden yayi sakamakon da katar dashi da Wanda a keyiwa banbadanci yayi,

Nayi ta kokarin in ga fuskar sa Amma ina nakasa gani sakamakon tarin jama’ar da ta take masa baya da yawa daga cikinsu Abokannanshi ne sai “yan uwanshi da kyar da jibin goshi na hango bayanshi sakamakon sunkuyawa da bafaden dake take masa baya yayi domin tattare masa rigar da yake sanye da ita domin samun damar zama cikin kujerar Alfarmar da a katanadar dominshi.

Wannan bafade da yake ta zuba kirari yakara dawo wa kusa dashi fadi yake tuba nake yi Jimina A gafarci na Tuba!!

Wani Abokinshi mai suna Shahid ya kalle shi yace kaje ya yafe maka Amma ka kiyaye gaba kasan sarai ba ya son wannan Abinda kake yi masa saunawa naji yana hanaka”

Sunkuyawa yayi yace tuba nake ranka yadade bazan karaba ,In sha Allahu,

Daga Kai shahid yayi yayi masa Alama da ya tafi,

Tunda ga can nesa balaraba take ta faman daga kai domin hango Dan mulki sunan da tasa masa kenan ,Amma ta Gaza ganinshi, takasa daurewa sai tamike tsaye cikin wayancewa tana gyara daurin zaninta gami da gyara zaman hijab dinta,

Da kyar ta hango shi ba sosai ba sabida yadda fadawa suka kewayeshi kuma da a kwai taxara mai yawa a tsakaninsu da inda take zaune,

Idan ba’idonta ne yake mata gizo ba sai taga Yariman da a ke tawani zuzutashi yaro kankani, tabbas ko ita ta girmi wancan yaron tafada cikin zuciyarta gami da komawa ta zauna tana tabe baki,

~BINTA UMAR ABBALE~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA

YARO DA KUDI

GIMBIYA BALARABA
????????????????

????

Acigabah da gashi✍????
[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????Writting by

~[Binta Umar]~
~MAMAN ABDUL WAHABU~

~MRS AHAMAD GWADABE~????

WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR
08089965176

????2

Ko min ti biyar bai yi da zama a gurin ba mai martaba sarki Almustaph yafito tare da mutananshi ,nan da nan guri ya nutsu ,fadawa ne a bayanshi cikin Nutsuwa ya riqa ratsa mutune fuskarsa a sake yana karbar gaisuwa,

Ya na zama wani bafade ya gyara masa zaman Alkyabbaur dake jikinshi ,da sauri yaje ya zauna jikinsu na rawa gami da yin gurfene sai kace wani mai nai man gafara,

Cikin Nutsuwa mai gabatarwa ya mike ,yayi gyaran murya cikin lasifiqa yace Masha Allah ,Alhamdullhi yanzu zamu fara gudanar da wannan taron sakamakon fitowar mai martaba Allah yaja da ranka ya kara maka lafiya gami da Adalci,

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button