GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Daddy ne ya katse shirun ta hanyar bude taro da addu’a ya dubi Umaimah yace “Baby ba komai yasa na taraku ba sai akanki kinga dai abinda ya faru tsakaninki da dan’uwanki kuma kinga irin matsalolin da suka rinqa fullowa qarshe dai ga ribar abinda kuka aikata nan kun samarwa zuri’ar Alh Abdulhameed Yauri Shuwa babu yanda zamuyi daku a dan qaramin family dinnan namu tunda daga ke harshi babu wanda zamu kora amma dai kun sani bakuyiwa zuri’arku da yarku adalci ba musamman keda kike mace yakamata ki nuna kedin mace ce wacce take fatan samun zuri’ar da zatayi alfahari da ita amma qarshe sai kika bige kika lalace wajen biyewa namiji da son zuciyarki saboda rashin tunanin me gaba zata haifar todai yanzu ga abinda gari ya waya yanan Allah ya sani munyi iyakar qoqarinmu na ganin kun kasance iyaye ababan koyi ga yayanku amma hakan yaci tura Umaimah dagake har Hameed nawane babu wanda zanyiwa baki saboda haka nidai na yafe muku batamin din da kukayi bada haqqina ba”

Dakatawa yayi yaja fasali kana ya dora da cewa “inayi muku fatan alkhairi a rayuwarku ta gaba sai Abu na biyu kamar yanda al’adata take kuma nayima yan uwanki Zarah da Jameelah lkcn da sukayi haihuwar fari to kema ga mukullin motar ki sannan ki zabi duk qasar da kikeso a duniya zan biya miki keda yarki kuje ku huta”

Tunda ya fara mgnr take wani irin kuka me ban tausayi kukan nata ba qaramin tasiri yayi a zuciyar duk wani wanda yake zaune a gurin ba har saida Jameelah da Zarah suka tayata,
Tsawa ya daka musu yace “banason shirme tanayi kunayi memakon ku rarrasheta sai ku qara turata ke mgn nakeyi miki ki fadamin qasar da kikeson zuwa nayi miki visa da passport zuwanan da sati biyu saboda saura 5 weeks hutu ya qare ki fara attend lectures”

Cikin kuka da rawar murya tace “Saudia Daddy” dagowa dukkansu sukayi suka kalleta saboda basu taba tunanin wannan zabin ba sunyi tunanin zata zabi Turkey ne saboda duk wanda ya kwana ya tashi a zuri’ar yasan burin Umaimah bai wucce taje Istanbul ba amma sai gashi lkcn da damar tazo Mata ta zabi wata qasar daban.
Kafin kowa yayi mgn Daddy yace “meyasa kika zabi Saudi Arabia Umaimah?” Cikin kuka ta bude baki tace.

“Saboda na kusanci ubangiji na na ziyarci kabarin annabi na roqeshi ya roqamin gafarar ubangiji ya yafemin wannan kayan dana daukarwa kaina nasani Daddy na take sani na aikata zunubi mafi girma wanda laifi biyune a duniya yafishi nauyi a mizani shirka da giba Daddy hukuncin kisane akaina ta hanyar jefewa meyasa bazaka kaini a yankemin hukuncin ba nasan zanfi samun sauqi idan na mutu ta wannan hanyar Daddy wanne jin dadi ne ya ragewa rayuwata Daddy da nasan wannan qaddarar tana cikin abinda zai faru dani ta haihuwa ba aure wlh dana roqi Allah na mutu na huta Daddy meyasa Mama batayi barin cikina ba? Daddy me zancewa Shurafah ranar data girma ta tsinci wannan mugun tabon da rudin zuciya yasamu mukayiwa rayuwarta…..”

Rufe mata baki Jameelah tayi ta rungume yar uwar tata a jikinta tana kuka tana cewa “kidaina fadar haka Umaimah ki daina roqon ki mutu ke bamu da yawa a zuri’ar mu kuma tun ran gini tun ran zane Umaimah waman qaddarallahu haqqan qadarihi haka wannan mgnr take babu wanda ya isa ya canzata naku dakyau ma tunda kinsan uban yarki kuma ya karbi abarsa kuma yanasonta kuma yar dangi ce qarshen dai abin ace idan mgnr aure ta taso tunda mace ce to koda mutane a duniya ko babu indai muna raye kuma muna haihuwa Shurafah zata auru ko a tsakanin yayanmu….”

Sake rungume Aunty Jameelah tayi tana wani kuka mecin zuciyar me imani itama Zarah kwantowa tayi a jikinta itama kukan takeyi tace “mu rufe mgnr nan tsakanin mu kada ta fita waje Umaimah don Allah koba Hameed ne uban Shurafah ba a qaramin family dinmu zamu karbeta mu riqeta saboda bamu da yawa muna buqatar yawaita a duniya abu daya ya rage Daddy kayi ka mayarwa da Umaimah da Hameed aurensu su riqe yarsu cikin aminci da kulawa”

Saurin dagowa tayi ta kalli Aunty Zarah ta girgiza kai tace “na roqeku kubar mgnr nan koda son Uncle Hameed zai kasheni na hqr da aurensa har abada kada kayimin dole Daddy hakan zaisa na rinqa kallon kaina a matsayin marainiya mara gata kuma bazan taba farin ciki a rayuwata ba Daddy bazan boye maka ba na tsani Uncle Hameed….” Ba qaramin girgiza kowa kalmarta ta qarshe tayi ba amma babu wanda yayi qoqarin sake maimata mgnr saboda suna ganin kamar ciwon abinda ya farune yasata furta haka.

Murmushi Daddy yayi yace “Shikenan Uwar masu gda tunda bakya raayin zama dashi babu meyi miki dole amma kinsan aure dolene akanki bada jimawa ba saboda haka zan baki shekara guda ki shayar da amaryarta ki fitar da miji kiyi aure sannan kamar yanda kika zaba zamu tafi Saudi dani dake da Hajiya sai Hameed da zamukai a dubashi acan saboda ciwonsa yafi qarfin asibitocinmu na nan sai kuma Yayarki Jameelah da idan kun gama umararku zaku wucce Turkey ki cika burinki na zuwa Istanbul kafin ki mutu”

Dariya tayi me hade da kuka ta miqe cikin tafiyarta da bata koma Normal ba ta matsa kusa da Daddy tayi kissing hanunsa ta rungumeshi ta kuma fashewa da kuka tana jera masa dubun gdy murmushi yayi yace komai nayima uwata ba faduwa bane fatana dai karta qara irin kuskuren da tayi a baya” jinjina masa kai tayi ya rungumeta yace Allah yayi miki albarka yabaki miji na gari wanda zai riqemin ke amana”

Amsawa kowa yayi da amin Daddy ya sake rufe taron da addu’a tare da yima yarinya Shurafah addu’ar shiriya da kariyar ubangiji kowa ya tashi ya nemi gurin kwanciya inda Daddy ya fice ya koma asibiti gurin Hameed.

Koda suka koma daki Aunty Jameelah ce ta hauta da fada wai bata kyauta ba da tace ta tsani Hameed tanajinta tayi mata shiru taci gaba da feeding din yarta har saida taga ta qoshi ta canza mata Pampers ta kwantar da ita tare da kissing din jajayen lips dinta tace “sleep well my lovely daughter kiyi dreaming dina kinji” abin dariya yabawa Jameelah sosai tace “oh ni Jameelatu Umaimah da ya hauka ya qaru wannan ya zakiga hauka gurin uwarki” dariya tayi tace “Allah Aunty bansan haka iyaye sukeji ba sai ranar da Hameed ya tafi da yarinyar nan wlh hankalina gushewa yayi ban iya sanin komai da nayi ba saida aka bani labari Aunty wai dama haka kukeji akan yayanku tab aini wlh babu mai dukar min Shurafah gara ka bugeni daka bugarmin ita dan zan iya rufe idona na ci mutuncin uban kowa”

Dariya sosai Aunty Jameelah da Aunty Zarah sukeyi Aunty Zarah tace “harda ubana ko?” Kunyace ta kamata don tama manta da Aunty Zarah a gurin ta kwanta tace “Allah aunty dan bakisan abinda nakeji bane” murmushi tayi tace “kafin kiji na rigaki ji Umaimah” da haka sukayi bacci.

UMMUH HAIRAN CE…✍????

[1/22, 4:45 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GIDAN UNCLE

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

PAGE FOURTY ONE

Kwanaki bakwai tsakani Umaimah tayi shar da ita baby Shurafah tayi wayonta tayi qiba kalar fatarta kalar fatar iyayenta kamarta da mahaifinta ta fito sosai Daddy ya gama musu komai na tafiya qasar Saudia duk tsayin lkcn nan Umaimah bata taba zuwa ta duba Hameed ba kuma ko a baki bata taba tambayar ya jikinsa ba.

Kwana biyu tsakani jirginsu ya daga qasar Saudi tun ranar da Daddy yace Hameed ya tafi da Shurafah rabon da ta sanyashi a idonta sai yau data hangeshi a zaune saman welchair kansa yayi gefe sai gyara masa kan yakeyi gefe ta koma ta zauna har lkcn tashinsu yayi suka shiga jirgin suka daga zuwa qasa me tsarki itadai bata cewa kowa komai game da Hameed din ba kowa yana jajanta jikin nasa amma banda ita da tayi qasa da kanta ta zubawa yarinyar ido wasu hawaye masu zafi sunabin kuncinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button