GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Katse mgnr yayi saboda numfashinsa da yake sama da sauri ya dafe qirjinsa yayi waje a guje da sauri Daddy yabi bayansa ya riqo hanunsa ya juyo da sauri zuciyarsa na tafasa idanunsa na fitar da hawaye yace “ka qyaleni Daddy wlh kasheta zanyi na kashe kaina kowa ya huta na gaji Daddy na gaji wanne irin rarrashi ne banyi yarinyar nan ba wanne irin qasqantar dakai ne banyi mata ba koda ace a cikin hayyacina nayi mata laifin da take iqirarin nayi mata indai tanada imani ya kamata ta tausayamin….”

Daidai lkcn sukayi sallama Prof Khair ya shiga motarsa ya tafi ita kuma ta tako cikin takunta na isa ta raba ta gefensu zata gifta ya cafko hanunta da qarfi ya finciko ta ta fada jikinsa babu kunya yasa hanu ya matseta yace “wlh tallahi billahillazi La’ilaha illah huwa babu wanda ya isa ya rabani dake don kece rayuwata Umaimah ko zaa kasheni kuma ko zan rasa komai nawa a yau sai an dauramin aure dake idan kuwa akaqi wannan karon zan saceki sacewar da babu wanda zai sake ganinki har abada” yana fadin haka ya fizge hanunsa daga na Daddy Hajiya tayi saurin riqeshi tace “Alh kayi wani abu kace wani abu wlh Hameed ya haukace baa cikin hayyacinsa yake ba zai iyayin komai Alh yaronnan mukaishi asibitin mahaukata a duba kwalwarsa” daga mata hanu yayi yace.

“Babana shiga gda zaayi yanda kakeso a yau da wani bacin ran gara wani Umaimah zo inason ganinki” sakinta yayi ya zube a gurin yana kuka me gigita tunanin kowa da ban tausayi yace “babu inda zani Daddy ni zakayi wa wayo wlh yau saina kwana da Umaimatu kota halin qaqa nasani tana sona toshewar qwalwarta yasa ta kasa fahimtar hakan waye zai aureta ya riqe mana yayanmu idan bani ba so take dole saita tozarta amanar Allah so take dole sai twince sun tashi sun fuskancin cewa su marayune meyasa zata bijirewa saqon zuciyarta bayan nasan babu son kowa a cikinta sai nawa meyasa bazaku kalli idonta ba kalli Daddy Hajiya kalli idonta wlh sona kawai nake hangowa a ciki so take ta kasheni ta kashe kanta bayan tasan ba cikkakiyar lfy ce dani ba itama kuma nasani zuciyarta ta kamu da irin ciwon da yake damun tawa zuciyar”

Daqyar Daddy da Hajiya suka bambareta daga jikinsa suka jata suka shiga da ita gdan suka kulle parlourn ya miqe yana buga qofar da qarfi yana cewa “ku bude bude Daddy zan balle qofarnan wlh saika bani matata ai donni kadai aka halicceta bazan yarda ku rabani da matata ba…..” Surutai dai rututu na rashin kan gado haka Hameed yakeyi kamar zautacce yana dukan qofar kamar zai balleta saida ya gaji ya hqr ya fita ya shiga motarsa ya nufi gdansa ya bude dake an gama aikinsa tsaf har ya zuba komai na amfani ya fada daya cikin dakunan ko qofar bai rufeba jikinsa yana bari zuciyarsa na tafasa yana dafe qirjinsa da qarfi yana nishi da kakarin aman wahala.

Shi kuwa Daddy yana shiga da ita ya zube akan gwiwarsa ya ruqo hanunta yace “badon ni ba badon na isa dake ba don girman Allah Umaimatu ki duba maraicin twince da wasiyyar mijinki Sulaiman ki bani dama ta qarshe na daura auranki da Hameed yaron nan ya garu sosai sonki zai kasheshi Umaimatu ya zakiyi da haqqin ran dan’uwanki idan ya mutu saboda ke bayan kinada yanda zakiyi ki taimakesa….” zubewa tayi ta rungume Daddy tana kuka me ban tausayi tace “kada ka qara roqona akan wannan Daddy zan iya bada rayuwata na fanshi taka balle wannan wlh indai hakan zai zama farin ciki a gareka na amince da auren Abdulhameed indai hakan zai zama farin cikinka na amince wlh na amince Daddy” tana fadin haka ta miqe da sauri ta fada daki saman gado ta fashe da wani kuka me ciwo tana cewa “Allah ka yafemin laifin da nayi maka ka sake jarabta ta da auren Abdulhameed Allah ka dubeni ka kawomin dauki cikin buwayarka Allah na roqeka kabani ikon yima mahaifina biyayya”

A wannan daren Daddy bai zauna ba yana fita ya kira Yusuf da mijin Aunty Zarah a masallaci bayan sallar magaruba ya fadawa limamin cewa yanada daurin auren yayansa biyu yabada komai aka daura auran akan sadaki dubu dari biyu suna shiga gdan ya fadawa Hajiya takuwa rangada guda ta daga hanu sama tace “Allah na gde maka daka sake gwadamin wannan rana Umaimatu na matar Hameedu na wayyoh dadi kasheni na huta” tasowa tayi zata fito taji mgnr Hajiyan ta koma da sauri ta zauna tana fadin “Hasbunallahu wa ni’imal wakil Innanillahi wa innah ilaihirraji’un Allahummah ajjirni fi musibati wa’akalifni khairin minha yanzu nice matar Hameed mutuwa ta tazo ya zanyi da jarabar Hameed” shigowar Hajiya ne yasata dagowa ta dubeta hawaye nabin kuncinta tace “Hajiya yanzu shikenan an daura aurena da Hameed Hajiya kwanana ya qare nama sani bazan iya dauke lalurarsa ba kamar yanda na dauka a baya Hajiya ki taimakeni….”

Rufe mata baki tayi da hanunta tana girgiza mata kai tace “kiyi hqr Umaimah Hameed zai canza baza kiyi irin zaman da kukayi a baya ba wlh ni kaina da farko banyi farin ciki ba amma yanzu ina farin ciki sosai saboda na yarda kuma na gasqata Hameed sonki yakeyi da gaske baso irin na sha’awa ba” da wadannan kalaman tayita rarrashin ta har ta samu ta saurara da kukan dama ta fara shiryata da magungunan su kasancewar saura sati daya aurenta da prof Khair saboda haka ta dora daga inda ta tsaya tunda tariga tasan halin dannata ba sauqi gareshi ba.

Yusuf ne ya nufi gdan Hameed din da nufin yi masa kyakkyawan albishir get man din ya tambaya ko megidan yana ciki yace masa eh yayi parking ya shiga yanata kiransa yana cewa “dallah malam ka fito haukanka yayi rana Allah dai ya yarda kuma ya amsa addu’ar ka Umaimatu ta dawo garek….” Tsayawa yayi cak mgnr ta maqale a maqogaronsa saboda ganin Hameed din kwance a qasa cikin amai yayi kaca² sauri ya saki ihu ya matsa ya dagoshi yana jijjigashi yana fadin “mun shiga uku Hameed kada ka mutu Daddy ya baka matarka ya daura aurenku…”

Riqeshi yayi cikin wata wahalalliyar murya yace “yay…ya daura in…ina Umaiman tak…” Muryarsa ce ta sarqe daidai lkcn Daddy suka shigo da gudu suka qarosu suna salati suka tattageshi sai asibiti likitoci suka rufa a kansa suna ceto rayuwarsa bai farka a ranar ba sai washe gari ya farka da qwarinsa saboda yasha drip babu qarya qyam ya miqe yana layi Daddy ya riqeshi ya kalli Daddy yayi murmushi yace “idan naje gdana yanzu zan tarar da bloody tana jirana?”

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[2/5, 9:08 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍????: GU

Murmushi Daddy yayi yace “aa tana gda saita yaye twins sannan zata tare…” Yanda ya wani zabura ne yasa Daddy yin shiru da mgnr yace “aa Daddy bazan iyaba tana karatu ni kuma baa qasar nan nake aiki ba tunda an daura ta tare a gdanta kawai na rinqa zuwa duk qarshen wata kafin ta gama karatun”shidai Daddy bai kuma ce masa komai ba likitansa yashigo ya kalleshi yayi murmushi yace “aa shugaban masoya ka miqe kenan shikenan ni kuma tawa kasuwar zata mutu buri ya cika”

Dariya sukayi dukkansu amma bandashi da duk ya qosa yaje gda yaga sanyin zuciyarsa saida suka gama cike²nsu sannan suka bashi dokoki suka tafi Daddy yanayin parking bai jira tsayawarsa ba ya balle murfin motar ya fita ya shiga gdan Aunty Zahrah ya tarar da Umaimah a zaune a parlourn taci kukanta har idonta ya kumbura gabansa ba qaramin faduwa yayi ba saboda yanda ta watsa masa wani dan iskan kallo ta kawar da kanta taci gaba da abinda takeyi qarfin hali irin na Hameed baisa ya hqr da abinda yayi niyyah ba yaja qafarsa ya qarasa ya tsugunna a qasanta ya dora hanunsa a saman cinyarta yana qare mata kallo yanajin qaunarta na azalzalar zuciyarsa yace “ina cikin farin ciki wanda ban taba shiga irinsa ba a rayuwata bloody kin dawo rayuwata”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button