BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL


Malam Sulaiman yana aiki a company madara ta cowbell wanda yake sharad’a dake ya jima yana aiki sai suka bashi gida a Badawa sai ya bar hayar da yake yana murna ya koma gidan kansa tare da iyalinsa.

Matar shi Mariya ‘yar nan makotansu ce sukayi auran soyayya suna da yara hud’u maza biyu mata biyu Hauwa’u itace ta farko tayi aure a giginyu kusa dasu tana da ‘yarta d’aya Islam. Aminu shine na biyu yanzu haka yayi diploma da dabara yana so ya cigaba DOMIN ya samu digree babu kudi sai buge-buge yake, Asma’u itace ta uku gurin iyayen ta, ta kasance Mara jin magana me taurin kai tunda ta taso haka take da bushashiyar zuciya ko fada suke da yara bata kuka, tana tsananin kama da mahaifin ta sosai shiyasa yake mutukar kaunar ta duk abunda tayi dai-dai ne

Asma’u tana da kyau na ban mamaki da tsarin jiki me kyau b’aka ce amma ba sosai ba Sam baza a sakata a layin farare ba, tana hanji da manya ido gami da k’aramin baki, tana da yalwar gashi kanta da gira gashin idonta gazar-gazar dasu sun kawata mata ido tana manya nonowa a tsaye k’yam dasu sharp dinta ya futo sosai cikinta a dame yanayin tafiyar ta sauri-sauri yanayin zafin ta da yanayin saurin bakinta domin wata maganar ma in ta fada mutum bazai ji ta saboda saurin bakin ta.

Mimi marainiya ce ‘yar k’anwar Mariya ce Umma kenan mahaifiyar su As’amau ta d’auko ta ta shayar da ita tare da Asam’au Mimi ta girmi Asma’u da wata hud’u.babu Wanda zai ce ba Mariya ce ta haife ta ba duk abunda za tayiwa Mimi tare take musu shima Sulaiman ya rike ta amana kamar ‘yar cikinsa

Yanzu haka suna da shekaru goma sha shida a duniya matakin karatu kuma sunyi saukar alk’urani me girma, b’angaran boko kuma suna ajin k’arshe a suna jarrabawar futa makarantar da sukeyi ta kudi ce sosai da sosai wan Baban Mimi shine ya tsaya musu dake lecturer ne yana da hanyoyi da dama suna gane karatu sosai da sosai.

Alina ‘yar wani hamshak’in me kud’i ne anan unguwar babanta me fada ajine Sam bai damu da abunda ‘yayansa suke ba shima sharholiyar sa yake da Matan bariki duk ‘yayansa maza ne Alina ce kawai mace shiyasa duk shekara momynta sai ta had’a mata birthday a guri me tsada anyi b’arnar kudi sosai Tuntuni ‘yan class d’inmu suke zargin Alina da karuwan ci, nice me zak’ewa ina cewa k’arya ne tunda basu ganta ba to su daina shedar zurur, Alina tana ji dani sosai a jinmu ganin yanda nake kare ta gurin kawayen mu, masifa ta yasa idan na saka baki sai suyi shiru ita kuma sai ta mik’o min tamfatsetsiyar wayarta k’arar Samsung ina karb’a zan shige karkashin bainci in bude ma’adanar aje video na fara kallon blue film dake tana dasu sosai a wayarta ina fara kallon a jikina zan san ya sanja tsigar jikina ta tashi k’uruciya ban San kome ye ba, zan ta mutsu-mutsu in naji suna nishin nan sai naji idona yana wani irin Abu,, yayin da zanji nonowana suna k’aik’ayi amma don jaraba bazan fasa gani ba, sai nagama zan futo ina matse cinya ta, ranar duk karatun da akayi ya wuce ni haka zan yini sukuku dani.

Mimi Sam bata San me nake kalla ba domin ko da wasa bata lekowa saboda tsoran masifa ta sai zatayi ta damuna da tambayar me yasa taga idona sun kankance sunyi jajazur, kawai zan ce Mata kaina ne yake ciwo shikkenan sai ta bar maganar

Muna komawa gida nake zubewa kan katifarmu in ta murk’ususu ina jin wani fleengs Wanda ban san ko menene ba, sai in kwana in yini kafin in samu sassauci amma fa sa’i da lokaci marata zatayi ta daurewa ban san KO menene ba, haka Umammu zata gaji da tambaya ta tayi shiru ta k’yaleni.

Tunda na gano kallon blue film din nan ne yake saka ni shiga irin wannan halin sai na daina in Alina ta bani wayarta ko da wasa bana bude video sai dai in kalli hotuna in wuce zatayi ta damuna da cewar ki shiga video akwai sabbi sunyi sosai zasu d’ebe miki kewa, masifa nake mata ince na daina kallo ita taje tayi tayi tunda baza ta daina ba. Sai tayi min Dariya kawai ta bar maganar saboda tasan halina.

Mota ce ta banke mahaifin mu yayin da yake kan mashin d’insa ya Bari gurin aiki da niyar komawa gida take a mutu ko shurawa baiyi ba, mun shiga rud’u da tashin hankalin rasuwar Babanmu nayi kuka kamar babu gobe kasan cewar nasan shine jigonmu madogararmu ni da ‘yan uwana Yaya Aminu bashi da k’arfi Asalima buge-buge yake na makaranta Aunty Hauwa’u kuma mijinta bashi da k’arfi itama ‘yan sana’oi take a gidanta tana rufawa kanta asiri.

Kun San dai yanda Aikin company yake baka da fansho balle garatuti farin cikinmu guda shine gidan da muke ciki Company ya mallakawa Babanmu ta kardun ma suna hannunsa bamu da fargar wannan.

Tunda ‘yan uwan Babanmu sukayi mana taimako na marmari sai kowa yaja zugarsa suka gudu suka barmu da wahalar mu,

Inda Allah ya taimake mu ma abokan aikin Babanmu lokacin da suka zo. Gaisuwa sun bamu kudi sosai har da masu kayan abunci fa sutturu shine muka rufa kanmu asiri

Ummamu da Aunty Hauwa suka fara harkoki da sauran kud’in da sukayi mana saura a hannu Inda Aunty Hauwa take shiga kasuwar kwari tayi sare sare na atamfofi mayafai da takama tazo ta raba cikin unguwar su, ita kuma Umammu ta fara sana’ar siye da siyarwa na cikin gida kamar su mai kalanzir gwayi bussasun kayan miya da ice da sauransu, da wannan muka dogara Yaya Aminu ya dage yana ta karatu inda k’aramin kaninmu me bina kenan Mussad’iq yake k’aramar makaranta zasu jarrabawar futa.

Wannan shine tak’aiaccan tarihin Asma’u

Cigaban labari

Mimi tace.” Anya Asma’u shawarar da kika fada tayi kuwa wallahi ba lalle ne aunty Hauwa ta yarda ba kin San halinta.”

Nace muje muyi wannan k’aryar zanje gurin SQ in karb’i kati bashi in sa a wayata zan bugawa aunty in lallab’ata ko tazo gida tace hakane.”

Mimi ta gyda kai kurrum tace.” Shikkenan muje Allah yasa kar Ummamu tayi fushi wallahi tausayin ta nake ji.”

Nace.” Nasan yanda zanyi da ita kawai kiyi addu’a kar Allah yasa Ya Aminu baya nan kin san halin masifarsa ko Ummamu ta hak’ura zai iya tun zurata.”

Mimi tace.” Hakane to Allah yasa muje mu tarar ya tafi makaranta.” Nace.” Amin dai.

Muka futo a tsane ke muka doshi kofar gidanmu yara na shiga wasu na futowa masu siyayya kasan cewar safiya ce yanzu.

Umammu na zaune a kujera ‘yar tsuguno tana durawa wata yarinya kalanzir cikin wata kwalba mukayi sallama muka shiga.

Amsawa tayi ba tare da ta dago kai ta kalle mu ba ta sallami yarinyar ta futa muka k’arasa kusa da ita Tare da zama kan tabarma da ke shimfide a tsakar gidan

Nace.” Ummam….. Dago min hannu tayi Tare da fadin .” dakata!” Shiru mukayi gabanmu na fad’uwa ni da Mimi tace.” Daga gidan ubanwa kuku a ina kuma kuka kwana.”

Tuni na sanja shawarar k’aryar da muka shirya bakina na rawa nace.” Daga gidan Kawu Yunusa mike.”

Cike da mamaki take kallona tace.” Me ya kaiku gidansa bana son k’arya fa.”?

Nace.” Ummamu ki yarda damu wallahi daga gidan sa muke kuma anan muka kwana ai kin San wannan kawar tamu Alina ta bayan layin nan ‘yar gidan Alhaji Santana ko.”

Umammu tace.” Na santa mana me ya hadaku da ita mara tarbiyar yarinya.”

Mimi tayi sauri tace.” Umammu kiyi yafe mu jiya munyi miki k’arya zamuje gidan aunty Hauwa wallahi ba can muka je ba Alina ce ta gayyace mu birthday dinta shine muka je can.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button