BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Muna zaune a rumfa ni Mimi Ummanmu muna karyawa sai ga Yaya Aminu ya shigo hankali a tashe! Umma tace.” Yaya ka dawo kuma.”? Cike da tashin hankali ya zauna kusa da ita tare da fad’in” Umma ina naga ta futa zuwa skull gari ya hautsine!!! Tace.” Me yake faruwa ne. ” yace.” Wai ina redion ki ne tun jiya ake tashin hankali a gari an je an kone company nan me zaman kansa. ” tace.” Wane company ni ne.”? Baki na rawa Aminu yace.” Amjadu AbulAbbas materials dummmm!!!!!? Gabana ya buga na tsurawa bakin Yaya Aminu ido ina kallonsa. Umma tace.” Ni ko a bakin wa naji wannan sunan.”? Mimi tace.” Bakin aunty Hauwa.” Tace “yawwa hakane ” sai kuma ta rafka salati tana tada hannunta cike da tashin hankali.
Ni da Mimi muka kalli juna rai duk babu dad’i. Umma tace.” Ni ina zan sani redio ta ta lalace dama wayata nake kunnawa to kasan jiya bamu kwana da wuta ba.” Yaya Aminu yace.” Aikuwa gari a hargitse yake domin ‘yan kasuwa sunan nam suna zanga-zanga kuma an hana futa da abun hawa. Umarni daga governor. “
[10/27, 12:00 AM] ????: Umma tace.” Gaskiya na jinjina wannan al’amari ikon Allah ko meye ya haddasa gobarar oho. ” yaya Aminu yace.” Mutane dai suna zargin ‘yan adawarsa ne, wasu kuma suna zargin da sa hannun gomnati har yanzu dai an kasa gano meye ya haddasa gobarar.” Cike da al’ajabi Umma tace.” Ai dole yaron nan yayi makiya da mahassada wallahi tunda yana son talakawa da tsoron Allah, kaga kuwa masu kud’in kasa zasu sanya shi a gaba.” Yaya Aminu ya mike tare da fadin ‘Bari in karb’i wayar Garba yayi rocouding din muryar shi lokacin da yake jawabi ke kanki Umma ki ka sauarari maganar sa zaki San abun shiryayye ne.” Futa yayi ya barmu da jiki a sanyaye, niko tsabar zura jiki sai na fara tunanin ko a wane hali yake ciki.har na k’agara Ya Aminu ya kawo wayar inji muryarsa wani irin mugun tausayin sa na damun zuciyata, to b’angaran Mimi ma haka yake domin ita har ta fara k’ananun hawaye.

Ya Aminu ya shigo da waya a hannunsa ya zauna kusa da Umma ya kunna mata voice din Amjadu lokacin da yake magana da ‘yan jarida jiya.

Tunda ya fara maganar nayi sak! Ina sauraron sa, muryarsa radau! Kamar Wanda baya cikin tashin hankali babu karaya da rawar murya a lafazin sa, kana ji kasan shine me gaskiya, Umma tace.” Ai daga jin wannan maganar ma kasan shiryayyiya ce makirci ne, kawai da hassada kuma zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi.” Yaya Aminu yace” Wallahi kuwa Umma, nake fada miki, guy yayi a rayuwa yana mutukar kaunar talaka da cigaban matasa Sam dukiyarsa bata rufe masa ido ba, dukiyarsa ta talakawa ce gami da mabukata da marayu, to Kin San an ce mutum tara yake bai cika goma ba, duk da haka mutanan gari suna zarginsa da neman mata wai har hotal ne dashi da karuwai suke watse wa.” Umma tace.” Wa’iya zubbilah kai jama’a mutane ba a iya musu dama hakane duk inda Allah ya daukaka bawa to sai ya samu yan hassada Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu.” Yaya Aminu yace” ameen suma ameen. Suka cigaba da tattauana maganar.ni da Mimi shiru babu bakin magana, tunda ya Aminu ya fara maganar sa nake addu’ar Allah yasa sharrin mutanan gari ne guy baya Neman mata, domin a lokacin ji nayi wani irin Abu yazo min wuya na bakin ciki. Wani gefe na zuciyata Yace min a kanki zaki gazgata shin shi din mane min mata ne ko kuwa bayan ke ga Alina,, kuma zuciyata ta dinga min sak’e-sak’e a kanshi gefe guda kuma ina tunanin ko wane hali yake cikiA yaanzu


Duk inda aka zauna can kenan gungun matasa da magidanta ‘yan kasuwa kai har da ma’aikatan ma suma wasu daga cikinsu suna jajanta al’amari, waya kuwa Amjadu har daina d’agawa yayi da k’arshe ma da abun ya dame shi, rambow yasa ya kashe wayoyin gaba d’aya. Ya kulle kanshi a daki shi kad’ai duk irin mutanan dake zuwa gurin shi ya hana a shigo dasu.” Tv ya k’ura ido yana kallon labarai na k’arfe goma dai-dai tashan NTA sosai ya girgiza ganin yanda matasa suke tashin hankali a gari tare da kona tayoyi had’e da rigima da ‘yan daba mutanan me girma Governor jama’ar gari sai gudu suke, wannan al’amari da ya faru ba iya kacin najeria ya tsaya har kasashen waje suma sai da suka nuno Company tare da rigimar da ake yi a kano din cikin labarai su na safe.

Mik’ewa yayi da sauri ya futa waje. Suna ganin futowar sa suka k’araso dukkanin su. Ya kalli Doh-doh tare da umartar sa da maza yaje gidan redio na express ya d’auko masa d’an jarida daya yana so zai yi magana.

Doh-doh ya wuce ya tafi cikin sauri. Nan harabar gurin ya zauna gurin hutawa yana sauraran dawowar sa, minti talatin a tsakani sai gasu sun shigo, ba tare da b’ata lokaci na Dan jarida ya gyara na’urarasa domin d’aukar muryar Amjadu

A nutse yayi bisimillah ya bude da addu’a sannan ya fara magana kamar haka.

*Ni Amjadu Abul Abbas ina kira ga jama’ar gari da duk wani d’an kasuwa matasa majiya k’arfi da duk wani me kishin kasa da duk wani me kishin kansa ina kira da babbar murya cewa in dai akaina kuke wannan zanga-zanga da ta hankalin Wanda basu ji ba basu gani ba, to maza Ku janye bana buk’atar haka ni Amjadu!! Nafi bukatar zaman lafiya a garin kano, saboda haka ina kira a gare Ku Ku aje makaman ku mu fuskanci abunda yake ga banmu ina me tabbatar muku da cewa ko yanzu kun tauna tsakuwa domin aya taji tsoro, shi Wanda kuke yin abun dominsa na tabbatar yanzu yana can hankalin sa a tashe, hausawa suka ce ruwa cikin cokali ya ishi me hankali yayi wanka tsalla d’aya tak!!! Za kayi ka fad’a rijiya amma sai kayi dubu baka futo ba…….Daga k’arshe nake muku albishiri da cewar duk wani Dan kasuwa da yake jin takaicin abunda ya faru to Ku kwantar da hankalin Ku sati guda yayi yawa gurin kara k’irkirar muku sabon Company me zan kansa wannan karon abunda company na na baya baya kawo muku to wannan sabon zai kawo muku samfura kaya kan farashi me sauk’i……..Ni ne naku *Amjadu Abul Abbas Mai nasara!!!!!!!!*

!Yana gama maganar shi ya mik’e da sauri! Ya bar gurin d’an jarida yayi saurin nad’e kayansa yana k’okarin tafiya. Nan doh-doh ya umareshi da ya tsaya kar ya tafi. Amjadu ya futo da kud’in cikin wata farar takarda ya mik’a masa, ya karb’a yana godiya sosai da sosai sannan ya tafi.

Cikin gidan ya koma a gurguje yayi ya wanka ya futo yana goge jikinsa wani mutsiya cin yadi ya dauko piltex me mugun kyau da tsada gashi cotton bashi da nauyi ko kad’an kamar net haka yake kalar shi darkblue!! Sai yayi amfani da singilet fara tas!! Ya dora rigar akai kana ganin hasken singilet din, shi kansa d’inki abun kallo ne, ya gaji da had’uwa sosai ya tsaya gaban mirror yana gyra links din hannun rigar ya taje sumar sa tare da sanya mata maya mayai sai shek’i take. Mugun turaran shi ya d’auka ya feshe jikinshi, hula irin ta hausawa sam! Bata dame shi shiyasa bashi da ita ko guda d’aya suma kayan hausawa din yana d’inka su ne domin amfanin wata rana kamar zuwa d’aurin aure gaisuwar mutuwa ko shiga cikin wani babban taro amma Sam! A tsarin sa babu manyan kaya. *Ni ko nace *Amjadu da kasan yanda kayan hausawa suke maka kyau da ka dinga sakawa oh! Dama dai zaka sanya hula damanga nasan ba k’aramin kyau zaka yi ba, hummm!! Kuna ina ne mutanan Amjadu ya kuka hasko mutumin NAKU cikin manyan kaya???????????? nima na dan gwala masa domin na k’yasa????????????‍♀????????‍♀*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button