BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Bayan mun gama cin abunci ne a na zaune ana hira nace”Umma ki bani dubu goma sha biyu a cikin kud’in I’n siyi waya.”

Tace” INA taki take.”? Nace” Umma wayar nan dama lallab’a ta nake wallahi jiya ma ta fad’i gurin chaji ya lalace.” Tace” kuma sai a kace Dole sai mai tsada zaki siya ko ina zaki kai wayar dubu goma.”? Marairaice fuska nayi nace” Lallai Umma Don baki ga wayoyin ‘yan ajinmu bane rafka rafka ko Mimi.”? Nafada INA kallon Ta. Tace” hakane Umma dom Allah ki bata kin ga sai muje da karfinmu babu raini.” Hararata Umma tayi tace.” Saboda rashin kishin kai ke Kin yarda ita ta rike waya ke baki da ita.” Dariya Mimi tayi tace.”Ummanmu kenan a wayar ta kamar tawa CE.” Tace” duk da haka dai baza ta siya ita kadai ba ga dubu goma sha hudu kuje Ku siyi ‘yar dubu bakwai bakwai ta ishe ku.”

Bata fuska nayi nace”Umma wayar dubu bakwai ai me madannai ce ni da nake son toching.” Aunt dake k’okarin shigowa dakin bayan futowar ta DAGA band’aki tace” sai ki siyi Vivo kawai in dole ne sai Kin rike babbar waya wannan ragowar kud’in da kika sakawa ido zamuyi amfani dasu ne gurin kara jari ki cire idonki daga Kansu, ” ta karasa maganar ta tana shirin ta da sallah. Nace”aunty ko Vivo zamu siya tafi dubu bakwai indai sabuwa CE.” Umma tace” sai Ku siyi ta hannu ai duk waya CE.” Shiru nayi kurrum domin bana kaunar yin jayayya da Umma.

Sai daf da marigaba aunt Hauwa tabar gidan.Mimi ce kawai ta karata hanya ni ko kwanciya ta nayi ina jin haushin yanda take k’ara zuga Umma akan komai,wani lokacin ko Umma bata yi niyyar yin abuna to aunt Hauwa da Ya Aminu sai su sanya ta.


Yaya Aminu ne ya shiga kasuwar ‘yan jagwal ya siyo mana Vivo ko wacce da ta ta, dake namiji ne sai suka bashi me kyau DUK bata wani sha jiki ba, yau saura kwana biyu Party mu duk mun tashi hankalin mu ni da Mimi mun fara gyaran jiki kamar wasu amare dilka da halawa kullum sai munyi aikuwa fatarmu ta goge mussaman ni da nake da chocolate din fata sai take wani irin k’yalli abun gwani sha’awa

Munnu muke jira tazo domin yau ne mukayi niyyar zuwa kunshi ja da baki can kabuga zamu je wata ‘yar kawar Ummansu Munnu ce take yi, duk mun shirya Munnu kawai muke jira tazo

Goma da minti goma ta shigo ko zama ban Bari tayi ba na azazzale ta, a tsaitsaye suka gaisa da Umma muka kama hanya.a dai- adai ta sahu guda muka d’auka har kabuga muka sauka da kafa muka shiga lokon su Bahijja me kunshi.

Babu jama’a a gidan Dan dama mun sanar mata da cewar in mun zo baza mu bi layi ba, aikuwa dama lallanta a had’e yake kawai ta fara aikinta. Ja ta farayi mana, bayan shi dai d’aura mana baki a kai, wai!!! Kafin kace kwabo mun fito Tass!damu gaskiya Bahijja ba dai Iya kunshi ba, dunu uku na mik’a mata tace baza ta karb’a. Ummansu tace” akan Me zata karb’a kuje fa kud’in ku ai Ku na gidane.” Aikuwa zura kud’in nayi a jakata dama a titi da muna tafiya naga wani gurin kwalliya gami da gyara gira. Muna futa nace dasu Mimi mu tsalla titi muje shagon kwalliyar can.” Munnu tace”wane irin kwalliya kuma. ? Nace “ke dai muje.” Suka biyo ni a baya cike da mamaki.
Duk kab’ilu ne a gurin, suna ta aikinsu ga wasu had’addun ‘yan mata anayi musu kitso irin na gashin doki.. Sai hira suke gami da taunar cingam. Cikin turanci nace da wata in ya mura muna so a gyara mana gira ne kuma za mu siyi gashin ido muna son su nuna Mana yanda zamuyi amfani dashi.

Aikuwa sunga costomas tuni suka bamu gurin zama muka zauna. Mimi ake wa ina kallonta naga tayi kyau sosai, murmushi nayi nace”Mimi kin ganki kuwa.”? Fuskarta ta shafa a hankali tayi dariya. ‘Yan Matan nan ne naji sun kwashe da dariya nayi saurin kallonsu cike da zargi, kawai idona yayi min tozali da budurwar nan da mukayi fada da ita shekaran jiya a Mudannsir&brots, shan kunu nayi sosai tare da tsare gira

Naji tana fad’awa kawarta duk abunda ya faru.kawar tata tace.” Kawai ki karawo su Salmanu a waya suzo su sab’a mata kammani.” Na fuskanci ni suke nufi. Mimi da Munnu Sam basu gane komai na sun fi tunanin cewar ‘yan Matan hirarasu kawai sukeyi irin ta kawaye.

Bayan an gama wa Mimi sai Munnu nice ta k’arshe sosai nace su gyara min saboda ina da yawan gashin gira sosai…aikuwa suka shiga fed’e min had’e da red’e ta sai da ta dawo sirirya sosai tayi wani irin kwana sannan suka bar ta, mudubi na kalla naga nayi kyau sosai, handbag dita na bude zan Ciro kudi kawai naji an wafce da sauri na d’ago kaina ina kallon su, wasu matasan samari ne sun sha askin ‘yan iska leb’ansu bakikkirin dashi. Wannan vudurwar suka kalla tare da fadin “ita ce ko.”? Gyda kanta tayi Tare da mik’ewa da niyar tafiya dama an gama musu kitson su….d’aya daga cikin masu aiki a shagon ta k’araso da sauri cikin turanci tace” me yake faruwa ne.? Safiyya ta mik’a mata kud’in aikin su ba tare da tace da ita komai ba taja hannun kawarta suka futa daga gurin
Kaina suka yo suna jamin mayafi cikin sigar rashin mutumci! Da sauri na Mik’e tsaye ina gudun kar su cire min mayafi gani a kan hanya kuma a bakin titi domin daga inda muke muna ganin shige da fuce na jama’a gami da zurga zurgar ababen hawa.Mimi da Munnu suka mike hankali a tashe suna basu hakuri . ni ko cewa nake.” Ku rabu dasu suyi min abunda aka sanya su Mimi sai ta fara kuka ganin har sun cire min mayafi. Duk ma’aikatan gurin suka rufe mu suna basu hakuri d’aya daga cikinsu ce ta dauki wayarta domin ta kira aunty su wato wacce ta bude gurin, ita kuma d’aya ta futa waje da sauri domin kiran jami’an tsaro.saboda wani lokacin suna zama bakin hanya kasancewar titin kabuga babban Titi ne bayan haka akwai many an masu kudi sosai a nahiyar saboda haka dole sai Da tsaro. Mimi ma futa tayi da gudu ta tsaya bakin titi ta diririce sai zare ido take……Fuuuuuuuuuu!!! Motar tazo ta wuce, yana kwance ciki ya hango Mimi da sauri ya mik’e zaune gami da bawa dravar sa umarni ya koma baya….doh-doh ya bi umarnin da aka bashi. Dai-dai santar shagon motar ta tsaya, ya hango duk abunda yake faruwa a ciki. Asma’u ce tsaye babu mayafi babu d’ankwali ga wasu maza tsaye a kanta. Sai mata uku suna kare ta.. Dake motar me tintac ce babu Wanda ya ganshi a ciki cikin tsantsar b’acin rai gami da bak’in ciki da takaici ya kwatsawa rambow tsawa tare da fadin yayi maza ya bud’e motar nan yaje ya kawo masa ‘yan iskan samarin nan, har da ita kan ta Asma’u.

Rambow ya bude motar da sauri ya nufi shagon, tunda nesa ta hango rambow sai gabanta ya fad’i tana mamakin me ya kawo shi gurin? Fad’uwar gabanta ne ya tsananta da ta tuna nan hanyar gidan shi ce tsakanin kabuga da jambolo ko da kafa mutum ya karasa, taji dadin zuwan rambow tasan zai taimake ta daga hannun ‘yan iskan samarin nan. Wanda suke k’okarin yi mata tsirara, daya daga cikin ma’aikatan gurin ce ta rike rambow tana fadin” please oga zo ka taimake mu ka futar Mana da wad’ancan ‘yan iskan samarn.” Rambo ya shiga ciki sosai take ‘yan iskan suka shiga hankalin su, domin sun yi wa rbow kyakyawan sani, yace.” Me ya hada Ku da ita.”? D’aya daga cikinsu yace.” Oga sunyi sa’insa da wata ne kwanaki shine ta kira mu muzo muyi mata tsirara.” Shi kanshi rambow da yaji abunda suka ce sai da ya tsorata, mayafin ya d’auka ya mik’a mata da sauri yana waiwayen bayansa, yace.” Ku muje mota dama akwai aikin da zakuyi mana a company .” aikuwa suka wuce da sauri suka tsaya jikin motar su duk a tunansu babu kowa ciki rambow ne kurrum, To shima Amjad din yana sane yaki futowa saboda gudun idanun jama’a DUK da haka yana kallon yanda mutane suke zurga-zurga a gurin motar tunda duk inda motocinsa suka shiga dole a gane saboda sunanshi dake mak’ale a bayan motar wato AA AbulAbbas Mai nasara.shiyasa yak’i futowa amma dukanin abunda yake faruwa yana hangowa, rambow ya kalli Asma’u yace.” Ku muje in kai Ku gida, don Allah Ku daina kula irin wannan ‘yan iskan samari marasa kamun kai.”
Fushina na sauke a kansa na watsa masa harara tare da fadin” kaga munyi kama da ‘yan iskane da zaka fad’i wannan maganar, mtssss.” Su Mimi da ma’aikatan gurin suka Bini da kallo cike da mamaki! D’ankwalina na d’aura sosai na ya fa mayafina kudinsu na mik’a musu,nace” Ku mu tafi.” Su ka biyo ni abaya , Rbow ko dake yasan halin rashin kunyar yarinyar bai damu ba, kuma yaga ogonshi yana ji da ita, shiyasa yake kaffa-kaffa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button