BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Mik’ewa nayi na shige dakinmu Mimi ta biyo ni a baya muka zauna kan katifa muna sauke a jiyar zuciya Minti biyar a tsakani tace.” Asma’u wai da gaske kike guy nan ne yayi miki siyyaya”? Nace” Mimi kin San dai ni kaifi daya ce, wallahi duk abunda na fadawa su Umma hakane, babu karya. Tace” kuma babu abunda yayi miki.” ? Kallonta nayi nace.” Kema zargin da zakiyi min kenan.” Girgiza kai tayi nace” To Allah dai guda ne, in kin yarda dashi wallahi babu abunda ya shiga tsakanina dashi.” Shiru mukayi ta mike had’e da fadin Bari in dauko miki abunci naga kamar kina jin yunwa.”

Mimi da kin barshi kawai ni bakin ciki ma bazai barni inci abunci ba duk akwai yunwa a tattare dani.” Wuce wa tayi ba tare da ce komai ba, minti biyu ta shigo dakin hannunta da plate da shinkafa da wake a ciki gami da salak da tumaturi, duk da abuncin da nake mutukar so ne, amma naji ko sha’awar sa ban yi ba, ta aje min ta futa ta d’ebo mun ruwa ta aje min. Nace”Mimi nagode K’warai Allah ya kara zumunci.” Shiru tayi kawai ta tsura min ido tace
” ki sako ki ci.” Domin kar in watsa mata kasa a ido yasa na sako na fara cin abuncin ba Dan dad’i ba.
[10/29, 9:51 A

Kai tsaye ba su wuce ko ina ba sai gidan granny, tunda al’amarin ya faru bai je ba yau kwana biyu kenan, mai gadi ya bude get din yana mik’a gaisuwarsa ga Amjadu ya amsa ta hanyar daga masa hannu. Motar ta shige ciki gami da samun gurin tayi parking, Rambow ya futo da sauri ya bude masa motar ya futo da sauri ya karb’i wayoyinsa hannunsa ya shige ciki suka rufa masa baya. Tsayuwa sukayi bakin kofar palo shi kuma ya shiga bakinsa d’auke da sallama, tana zaune kan kujera hannunta rike da carbi kana ganinta kasan tana cikin damuwa dattiijuwa me sanin ya kamata kenan. Tana ganinsa ta sauke ajiyar zuciya had’e da sakin fuska tace.” Ashe kana tafe.”? Da sauri ya k’arasa kusa da ita yw zauna had’e da Dora kansa kafadar ta, wani irin tausayi tsohuwar yake ji

Kanshi ta shafa muryar ta na rawa tace.” K’ato haka Abu ya faru ko.” Girgiza kansa yayi dake kafadar ta yace.” Waye k’ato kuma.”? Kanshi ta rank’wasa tace” ga kanan a gabana.” Gyara zama yayi yana Dan bata fuskarsa yace.” Bana son sunan fa.” Murmushi tayi tace.” Yanzu na fara fada ni kuma.” Shiru yayi mata. Minti biyu tsakani tace.” Amma mutanan sun cika azzalimai, wallahi tunda nake ban taba ganin mutum maciyin amana ba irin Alhaji Hashimu. Nasan da hadin bakinsa komai ya faru.”

Girgiza kanshi yayi cike da b’acin rai yace.” Granny ni nafi zargin me girma governor domin dashi mukayi sa’insa a ranar.” Tace.” Koma dai waye ka barshi da Allah da sannu zai saka maka.”

Murmushi me ciwo yayi yace.” Dole ne Granny Allah ba abun wasa bane amma zan basu mamaki wallahi nafi su k’ananun shekaru nafi su kuma dabaru sosai governor sai ya gagara futowa wani taro domin sai jama’ar gari sun jefe shi tunda ya nuna kansa a gurin su.”

Granny tace.” Ai naji a redio sai zaginsa akeyi Allah dai ya kyaua wasu masu mulkin su dauki alk’awari su kasa cikawa su Da Wanda ya hallice su.”

Shiru yayi yana girgiza kansa, ta mike a nutse ta nufi kicin da kanta minti biyar tsakani ta dawo hannunta rike da k’aramin tire jere da kayan abunci. Zama tayi tana k’okarin zuba masa, ya bata fuskarsa, tace.” Kome zakayi sai kaci abunci ayi mutum yayi ta rayuwa babu cikkaken abunci sai yame-yame.” B’ata fuska yayi yace.” Si kece komai naki sai kin sanya masa daddawa yayi ta wari.”

Hararasa tayi tace” karya kake ba komai nake saka mishi daddawa ba. Kallon plate din yayi yaga wata lafiyayyir wainar shinkafa fara tas da ita, wani kwano me kyau ta bud’e farfesun kayan ciki ne sai kamshi yake yaji kayan kamshi tace.” Nasan dai wannan zai yi maka dad’i ko.” Murmushi yayi yace.” Nagode granny gaskiya kina ji dani sosai, zanci wannan delicious din naki yayi min kyau a ido Allah yasa yayi min dad’i a baki.” Duka ta kai masa yasa dariya, hannunsa ya nan nade ya dauki Fork ya fara cin abunci zuciyarsa a sake duk damuwar da yake ciki mutukar yazo gurin kakarshi yana Neman kashi Hamsin ya ras.

Yana cin abuncin tana kara tausar zuciyarsa gami da nasiha na cewar kar ya dauki fansa akan duk Wanda yayi masa haka ya barshi kawai da Allah zai saka masa cikin kan kanin lokaci.

Robar ruwa ya d’auka ya bude ya kafa kanshi Yana sha Sam bai tsaya tsiyayawa a cup ba, sai da ya kusa sanye rabinsa ya aje robar ya aje Fork din had’e da jin gina jikinsa jikin kujera yana lumshe idonsa, shi kadai yasan tunanin da yake. Ta kalle shi had’e da fadin kaga da kana da aure sai kawai ka mik’e matarka tayi maka tausa yanzu ko sai dai ka zare ido.” Bude idonshi yayi yana Dan kallonta tace” K’warai kuwa ai gaskiya na fada” zama gyara yana fuskantar ta sosai yace.” Kina son inyi aure ne.”? Tace” sosai ma kuwa ai ka kai munzali Dan baka da auran ne ma yasa wasu suke samun dama akan ka, kasan shi aure yana karawa mutum Martaba. “

Yace.” Nifa ko budurwa bani da ita Granny.” Da sauri tace.” Ai me sauk’i ne wannan ni idan ka yarda sai in nemo maka matar aure.” Murmushi yayi yana Sosa kanshi yace.’ A’ina”? Gyara zama tayi cike da murna tace. ” ko d’azu mun Dade da Innah ka Suwaiba tazo yi maka jaje shine muka yanke shawarar kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar da ka gani ranan a gidan nan.”

Bude idonsa yayi sosai yana kallonta Yace.” Granny nine zanje in nemi ta ko ita ce zata zo.”? Tace.” Ka tab’a ganin inda mace tazo Neman aure K’ato.” ? Sosa kansa yayi yace.” Um!Um kawai ki bar wannan maganar Sam! Yarinyar batai min ba, inan zan kawo miki budurwa ta ki ganta.” bata fuska tayi tace”Ai ka saba fad’ar haka, ni dai nace Hafsa nake so ka aura saboda na Yaba da halayen ta.”

Kallonta yayi cike da mamaki yace.” Granny ni ba tayi min ba in kuma kina so na maida musu da yarinya k’aramar bazawara shikkenan.” Jin abunda ya fada ne yasa granny dawo wa nutsuwar ta tace” shikkenan ai yaushe zaka kawo min budurawar taka.” Yace.” Kar ki damu zan kawo miki ita da ko wane lokaci.”


Muna idar da sallahr magariba aunty hauwa ta shigo dakin namu tace.” Sai Ku futo mu tafi ai naga alama bakin Ku d’aya. ” hibaj dina na d’azu na zura fuskata kojale kojale muka futo duk nayi wani zuru-zuru dani. Yaya Aminu na tsaye a bakin kofar futa sai zare ido yake kamar wani dogari , harara ya bimu dashi muka futa simi-simiā€¦. Suka biyo bayanmu bayan sun yiwa Umma sallama.

A dai-dai muka samu muka shiga aunt ta kalli Aminu tare da fadin ” yanzu kwatancan gidan zamu nema.” Yace.” Ai gidansa ba b’oyayye bane a jambolo baza mu sha wahala ba.” Su kadai suke hirarsu munyi shiru. Sai da muka zo second get muka sauka muka tsallaka titi da kafa muka fara tafiya, har muka Isa Estate din da muka gani a kulle ga wasu iyayen karnuka a ciki a kwankwance masu tsarin gurin suna zazzaune a gurin zaman su da, ya tsayawa mukayi jikin get din muna shawarwarin yadda za’ayi.

29/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

34

Yaya Aminu ne yake d’agawa masu dadin hannu. Daya daga cikinsu ya taso da sauri yana zare ido! Hannu Ya Aminu ya mik’a masa yak’i karb’a, fuska a had’e yace.” Gurin wa kuka zo.”? Shi kansa Aminu a lokacin daburce wa yayi kafin yace.” Gurin Amjadu Young millionaire” wani irin kallo me gadin yayi masa yace.” Bayin Allah yanzu duk irin kyauta da bawan Allah nan yake muku bai muka ba sai kun biyo shi har gidansa.” Ya Aminu yace.” Ba abunda kake tunani bane ya kawo mu, wata Matsalar CE,idan da hali muna so ka sada mu dashi.” Cike da nazari me gadin yake binmu da kallo kafin yace.” Bai shigo gida ba.” Shiru mukayi dukaninmu. Me gadi ya koma gurin zaman sa yana fadawa ‘yan uwa tare da nuno mu da hannunsa suna dariya. Duk sai naji na kaskanta Ashe haka Ya Aminu ya juyo gare ni a zafafe kamar zai kurma min mari yace.” Kin kyauta Asma’u kinga wulakacin da kika jawo mana ko.” ?
Kasa nayi da kaina cike da tsoro domin kar ya dake ni.aunt tace.” Yanzu meye abinyi.” Ranshi a bace yace.” Tafiya zamuyi domin tsayuwarmu a gurin bata da amfani domin bamu San sanda zai dawo ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button