BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Cikin wani irin muryar ya fara ambaton sunanta “Asma’u” Ke Asma’u!!!

Kamar a mafarki naji ana kiran sunana
Da sauri na mik’e zaune ina ja da baya ganin yanda yayi min rumfa, muryashi me taushi yace.” Tashi ki bani guri inyi sallah.” d’auke kaina nayi daka kanshi ina Ala wadai ds tur da halinshi, ya gama aikata alfasha ya ishi mutane da sallah.

A hankali na mike na koma can gefe guda gami da takure jikina, daddumar ya daga ya karkad’eta ya mayar ya shimfid’a data, ina kallonsa ya tada sallah raka’a biyu yayi ya salle me yayi addu’oin sa sannan ya mike a nutse ya futa daga dakin.

Ajiyar zuciya na sauke zuciya ta na sake-sake akansa tabbas Akwai wani al’amari nashi dake rufe

Jin ana kiran sallah ne yasa na mike da sauri na futa daga dakin tunda ya bud’e tsayawa nayi ina bin dank’areran falon da kallo ya had’u k’arshe fad’ar kyawunshi da tsaruwar shi bata lokaci ne ko ina tar haske Mimi nake lalube can na hango ta cikin kujera me cin mutum daya ta mak’ure jikinta da sauri na k’arasa inda take ina kiran sunanta.

Ta bude ido a furgice tana kallona sai kuma ta fashe da kuka sosai, sauri nayi na rufe mata bakinta na kamata ta tashi, hanyar futa muka nufa.

A bude take, abun mamaki muna dosar ta kofar sai ta fara tafiya suuuuuuuuu ta rufe kanta, Jan hannun Mimi nayi da gudu muke k’okarin ture kofar, abun nasara tuni ta rufe har tana hadawa da hannu ihu na kurma ina matse shi.

Mimi tace.” Kinga Asma’u kiran sallah ake muje muyi alwala tun daga toilet can muyi sallah mu jira gari yayi haske.”

Babu yanda na iya haka muka koma ciki Mimi ta shiga toilet ni kuma na zauna jiran futowar ta

Minti biyu da zamana sai ga Alina ta futo daga wani bedroom tana sanye da wata mutsitsiyar Riga da gajeran wando cinyoyinta duk a waje, Attachment din kanta duk ta duje. Shek’eke na kalleta naja tsaki gami da fad’in.” ‘Yar isakar k’arya da wofi.”

Da sauri ta juyo tana kallon inda nake zaune domin Sam batayi tunanin akwai mutum a gurin ba.

Cikin jin zafin abunda nace mata tace.” Wallahi Asma’u zagin da kike min ya ishe ki tun jiya kike zagina saboda tsaurin ido irin naki har kina kamani da kokawa,wallahi kinci sa’a a gaban Amjad ina tsoran fushinsa amma da sai nayi miki rashin mutumci kin San dai halina ko a skull bani da kyau bana barin ta kwana.” Tsaye na mike nayi kanta cike da masifa da neman tashin hankali nace.” Durun uwar ki Alina don Allah Ki dauki mataki kan abunda na miki ehee ni kinsan irin masifa da bala’in da kika sanya ni a ciki tsakanin jiya da yau? Kin fi kowa sanin wacece ni kin san na fiki rashin mutumci wallahi sai na rama abunda kika sa wannan Dan iskan yayi min.”

Rik’e baki tayi cike da mamaki tace.” Amjad din kike zagi Asma’u tun jiya fa naji kina aibata shi gami da zaginshi wallahi ki kuka da kanki, Dan baki San waye shi ba kuma baki San me ya taka ba bakin san d’aurin gindin da yake dashi na a kasarnan.”.

A har zuk’e nace.” An zageshi din shi waye ko a gabansa ma zan zageshi ba wani abun bane idan kin Isa ki fada masa in ya shigo, ke dashi duk ‘yayan iska, ‘yar durun uwa kawai.’

Alina ta fusata! Iya fusata jin ina zaginta lallai baza ta lamunta ba, da gudu tayo kaina muka sark’e da kokawa sosai.

Mimi ta futo taga abunda yake faruwa kanmu tayi tana k’okarin rabamu muna bugeta sai ta koma gefe tana kallon ikon Allah.

Yana bud’e kofa yaga abunda yake faruwa, duk bamu lura da shigowar sa ba Mimi ce kawai ta lura tsabar kwarjinsa yasa ta kasa fada masa abunda ya hadamu sunkuyar da kanta kurrum tayi ya wuce ta cike da karsashi ya durfafo mu fuskarsa kamar an aiko da mala’ikan mutuwa.

Alina na mukure jikin bango tana kifta ido saboda shak’ar da nayi mata, sai kakari take tana k’okarin k’watar kanta ni kuma ina kara matseta tare da fadin.” Nace miki ki kwaci kanki a hannuna, ni zaki yaudara ki sa muzo birthday din ki, ki jefa mu halin masifa eheeee! Kin San irin jarfar da kika sanya ni a ciki tsakanin jiya da yau, bayan wannan ma me kike so muce idan mun koma gida. Alina sai na dauki fansar abunda kika mun dake d’an Iska Amjad da kike damuna da shi.”

Hannunsa guda ya sanya ya funcike ni daga jikin Alina ya yarfar dani guri guda, yana wani irin huci!! Da mugun gudu na mike na kara komawa kan Alina, yayi saurin tare ni da gangar jikinsa, ya matse a bango!! Muka fara kallon kallo, lumsassun idonsa ya zuba min sunyi ja saboda b’acin rai. babu walwala ko ta kwabo a tare dashi.

Kirjina ya matse da nawa kirjin sosai ya zura hannunsa ta bayana yana shafo mazaunai na cikin wani irin dan iskan salo.

Numfashina ya dunga futa sama-sama lokaci kankani na susuce yayi lakwas duk kuzarin da nake ji dashi ya gudu, sai naji gwiwa ta tayi sanyi k’alau ina nema in zube a gurin.
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

15

Saki na yayi na zube a gurin, ya tsaya kaina yana sakin wani muskilin murmushi tare da shafa kwantaccan gashin dake fuskar shi.

Saurin kauda kaina nayi da kansa leb’ena sai rawa yake ni kadai nasan halin da nake ciki a lokacin.

Murza hannunsa yayi kamar yarda ya saba ya kauce da kaina, a hankali ya tsugana kusa da Alina dake nishin wahala ya dagota tare da rungume kungunta suka nufi bedroom d’insa.

Kallo na bisu dashi yayin da naji wani irin k’aton Abu yazo ya tokare min a mak’ogaro ganin yanda hannunshi yake tab’a mazaunai Alina.

Mimi ta k’araso inda nake takure tace.” Asma’u ina hadaki da girman Allah da Annabi ki iya bakin ki kibari mu rabu da guy nan lafiya duk wannan abun da kikeyi bakya nasara akansa, wahalar da kanki kike.”

Cikin jin zafin Abunda tace.” Nace.” Ni kiyi min shiru don Allah don dai ke ba ke akaiwa abunda akaimin ba shiyasa kike fadin haka.”

Rike baki Mimi tayi tace.” Wallahi abunda ya faru dake ji nake tamkar ni akayi wa dadin da naji kawai yanda naga kin futo daga dakin k’alau dake wannan yana nuna min cewar baiyi raping din ki ba.”

Kaina na sunkuyar kasa cikin zuciyata nace.” Ke kike maganar raping Mimi ni kadai nasan halin da ya sanya ni tsakanin jiya da yau.

Mimi ta zauna tana rarrashina cewar don Allah ko ya futo kar in kara tanka masa kawai muyi kokari mu rabu lafiya dashi.

To nima na yarda da shawararta domin ina ganin idan ba haka ba mutumin nan zai iya sakawa na mutu saboda abunda nake ji in ya rabe ni.

Awarsu hud’u a cikin dakin sannan suka futo. Muna zaune ni da Mimi kujera guda lokacin Fleengs din da nake ji a game dashi ya rago sai abunda baza’a rasaba.

Da sauri na kauda kaina ganin yanda yayi min wani mugun kyau Sosai ya dauki wanka dress din ya mutukar yi masa kyau, yana sanye da wani bleu jinsh wanda yake gwiwoyinsa duk a fashe wanda be san tsadar shi ba sai yace yasa wando lallatace.

Tare da wata shart me k’aramin hannu itama pink color rigar ta matse shi mussaman daga gurin hannunwansa kayan sunyi masa cif a jiki kasan cewar sa mutum me kyawun jiki Sam babu rama a jikinsa ko ina a jiki take,da alama yana yawan motsa jikinsa.

Kasa hak’ura nayi a fakaice na kara kallon inda suke shida Alina itama tayi Wanka ta sanja sabbin kaya. Wuyanshi na kallah naga wata siriryar sark’e kamar daimond sai shek’i take hannunshi tsaddadan agogo ne Rolex sai walwali yake, hular shi hana sallah ya juya ta ma’ana gaba ya koma baya- baya ya koma gaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button