BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Wani helf cover naga yana sanya wa a k’afar shi fara Tass! Da ita kafa kamar bata namiji ba, ga wani ya tsunsa gashi sun bi sun kwanta abun sha’awa takalimn blue ne amma sky ya d’aura agogon shi Rolex mai mugun tsada. Cike da karsashi da jarumta ya futo , suna tsaye bakin kofa suka rufa masa baya. Rbow ya bude masa mota ya shiga suka futa daga gidan.


Take tashar express redio ta saki muryar Amjadu a gari, gari ya d’auka dattawa wadanda sukan sa meye duniya suke fadin “Yaron nan mai hankali ne da sanin ya kamata gashi dai karami ne me k’ananun shekaru amma yana aiki irin na manya ya iya lafuza masu kyau abunda ya kamata ace gomnati ita zata tsawayar ta kasayi shi ya futo yanayi tabbas wannan yaron zai dace da zama shugan kasa kuma shugaban al’umma domin irinsu ake so masu sanin ya kamata”!!!!…….. Tofaaa!! Muna zaune muna zancan Yaya Aminu ya shigo da sauri hannunsa rike da wayarsa yana fad’in Umma kinji kalaman Young millionaire ko kai!!!! Gaskiya guy nan Dan aljanna ne wallahi.” Umma ta karb’i wayar tana sauraron muryar Amjadu fuskar ta cike da farin ciki. bayan ta gama saurara tace.” Allah yayi masa albarka kuma ya bashi mace ta gari wannan yaron sai naji ya shiga raina sosai.” Yaya Aminu ya futa da sauri yana fad’in “Bari in mai da wa Garba wayarsa . Jiki a mutukar sanyaye na mike salau-salau na shige kuryan dakin Umammu na haye gado tare da rintse idona gabana na fad’uwa tun da Naji muryarsa na rasa kuzarina narasa wace irin masifa ce wannan.

**
Babu inda suka yi wa tsinke sai Company nan ya tarar da Aiki yayi sauki domin duk abun futo da matattatun kayan da suke ciki gami da na’urorin da suka samu matsala matasa majiya k’arfi suna ta aiki, gaskiya ya yabawa korarin su da kuma kaunar da suke masa, tsaye yayi a harabar gurin hannunshi goye a baya yana nazari, abun mamaki sai ga ‘yan jarida sun yi masa caaaaa! A ka dama shi suke jira ya zo.

A nutse ya kalle su. Shi dariya masa suke bashi yace.” To yanzu me kuke so nace wai.” ? Daya daga cikinsu yace.” Ranka ya Dade kace mutane su janye zanga-zanga da sukeyi shine muke Neman Karin baya ni.”
Sosa kansa yayi ya saki wani killer smile wanda shi kadai ne tasan ma’anar sa yace.”duk wani bayani da zan muku yanzu bazai gamshe Ku b, so yanzu dai abunda zance shine, duk wani mubukaci yana iya zuwa wannan company ya dauki duk abunda ya ke so na abunda akayi asara saboda ina so in fara aiki a gurin.” Daga haka yaja bakinsa yayi shiru . aikuwa sun samu abun ya ya tawa atake suka fara sanarwa kafin kace kwabo zance ya baza gari mutane suka fara tururuwar tafiya domin su kwashi garab’asa

27/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

31

Muna shirin cin abunci na rana sai ga aunt Hauwa ta shigo da sallama a bakinta. Muka amsa tare da yi mata sannu da zuwa, Umma na kicin tana rabon abunci tace” ke kuma daga ina kike ana rigima a gari kika futo.”? Aunt hauwa na dariya tace. “Wallahi Umma daga gida nake ina gidana ina nan si babu nisa.” Umma tayi shiru bata ce komai ba. Nace “aunt Hauwa ina Islam take.”?
” Tana gidan Maman fa’iza na barta, saboda cikin jama’a zamu shiga.” Nace.” Aunt Hauwa ina zakije gari babu lafiya. ” tace.” Bonanza zan je in kwasa a kyauta kuyi maza Ku gama ci mu tafi don Allah kar a kwashe kayan.” Umma tace.” Wai ina zaku ne.”? Aunt tace” Umma duk abunda ke faruwa baku sani ba.”? Umma tace” sai kin fada mana yanzu.”

Aunt hauwa tace.” Garab’asa ga me rabo Umma kinsan anyi gobara a wannan company Dana ke baki labari ko.” Umma tace”eh mana ai tun dazu muke cikin jimami da alhini.” Aunt Hauwa ta cigaba da cewa”yanzu ya bada damar duk wasu kaya na ciki aje a kwashe su zai fara aikin gurin shine fa na wanko kafata in je in kwaso garab’asa.” Girgiza kai Umma tayi tace.” Ke kam ban San inda zaki kai kudi ba wallahi!” Dariya mukayi ni da Mimi aunt ta hau zaginmu tare da fadin ” in baku zuwa inayi tafiya ta wallahi kuma duk wacce taga Abu a gurina tace tana so ubanta zanci” cikin dariya nace” zamu je Wallahi ko Dan mu bawa idonmu abunci, ko Mimi”? Daga kai tayi tana dariya aunt tace.” To maza Ku tashi mu ganshi omin ban yarda ma Ku tsaya wani Wanka da kwalliya ba.” Zare ido nayi nace.” Gaskiya sai nayi Wanka dube ni fa, sai maiko nake. ” mik’ewa tayi da sauri tana kallon Mimi tace “tashi mu tafi Mimi” ta mike da saurin ta! Nima na mike dakinmu muka shiga muka d’auka zurma-zurman hijabai muka futo, Umma tace”tafiya zakuyi baza bari Ku ci abunci ba” aunt tace” Umma in mun dawo maci” tayi gaba da sauri!

Tsayawa nayi bakin kicin din nace.” Umma bamu kud’in ankon sai mu biya kasuwar kinga mun huta ma.” Mik’ewa tayi ta shiga daki minti biyu ta futo da kudi a hannunta tana lissafawa dubu goma sha bakwai ne tace.” Akwai kudi hannun auntnku ta cika muku.” Na karb’a da sauri ina fadin” sai mun dawo Umma” tace”Allah ya kiyaye kar kuyi dare kun jiko” nace” insha Allahu Umma.

Can nesa na hango Aunt Hauwa da Mimi suna tafiya kafin in karasa hat sun tarar mana me a dai-dai muka shiga da sauri aunty cewa take” yayi sauri sauri” aikuwa ya fafari mashin kamar zai tashi damu sama.

Wai!!!!!!!!! Cunkus!! Kenan tunda muka sauka daga babur nake hango dandazon mutane bakin wangameman gete din suna turereniyar shiga gurin sai buge-buge ake maza da mata.
Aunty Hauwa nake kallo dake k’okarin tsalla titi nace.” Aunt Hauwa tana ina zamu kutsa mu shiga cikin jama’ar nan.”? Hararata tayi tace.” Ta inda kowa yake shiga muma tanan zamu shiga.” Kallonta nayi cike da mamaki nace.” Ni kam wallahi bazan shiga a dauje ni a banza ba bayan haka kuma guri duk ya cika da garada maza daga ganin su za suyi tsamun hammata! Takaicina bai bar aunt tace komai ba ta kama hannun Mimi suka tsallaka titi suka barni tsaye a gurin. Ina kallonsu suna ta kutsawa cikin mutane har na daina han go su. Mintuna ashirin ina tsaye a bakin titi rana sai dukan fuskata take ga uwar yunwa dake sasakar cikina, tuni goshina ya soma tsatstsafo da gumi na fara jin jiri. K’okarin tsallaka titi nake in samu wani guri in zauna in jira su domin ni kam bazan shiga cikin wannan wahalar ba.” Gefen wata bishi na zauna ina kallon yanda jama’a suke futo da kaya a daure wasu na shiga wasu na futowa. Da sauri na mike tsaye ganin wata budurwa ta futo hannunta rike da wani dogon abu tana ja da k’arfi k’ura idona nayi sosai sai naga irin material dinmu ne sak!! Na anko har kalar bandir guda ta samo a ciki ‘yan uwanta sun biyo ta yuuuuuuuu! Da sauri na k’arasa gurinsu ina mik’a kaina domin in gani sai naga Sam! Bai samu matsala ba illah jik’ewa da yayi da kuma bak’in da ya fara kama jikinsa Dan ma kalarshi me haske ne, amma Sam bai kone ba.” Sai murna sukeyi suna kasafi tun basu je gida ba, sai naji kamar in ce musu su yan karmana domin komai abunsu yayi musu yawa Dole su bawa wani.
Zuciyata tace min kema ki shiga ki gani ko Allah zai sa ki samu kin ga kud’in Umma sun huta, kun samu kud’in siyan takalma da haka, aikuwa ban tsaya tunani ba na durfafi kofar shiga,INA addu’ar Allah yasa na samu nima ko Mimi ta samo mana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button