BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Tun daga bakin get din makarantar mu muka soma cin karo da k’awayenmu da ihu!! Suka zo suna rungume ni tare da taya mu murna ni da Mimi mun ci jarrabawa nima sai na saki fuska sosai na kutsa cikin jama’a domin idona ya gane min, duk mun cinye maths ne kawai muka fad’i shima ba sosai ba, wasu na murna wasu na bakin ciki nima tsabar murna tasa na manta da komai na shiga cikin k’awayenmu muka fara ihu! Da dariya wadan da suka fad’i ciki ko har da Alina tana tsaye jikin motar ta kamar ta kurma Ihu! Munnu na kalla cikin dariya na nuna mata Alina ina fad’in” Munnu dubi Alina da fuska sai kace soyayyan k’osai sai maiko take cikin rana.” Munnu ta shek’e da dariya tana fadin” shegiyar ba fuska taci bleecing ciki ko oho dama yaushe zata ci jarrabawa tana can tana yawon iskan ci.” Dariya muka shek’e da ita. Mimi tace.” Ku Wallahi kun fiye Neman fitina kuzo mu tafi tunda dai mun gama abunda ya kawo mu” hararta nayi nace.” Wallahi baza mu tafi yanzu ba sai nagama kallon ‘yan bakin ciki da masu kuka irin su Ooo” na nuna Alina da bakina . a fusace! Ta tawo inda muke tsaye ta nuni da ya tsa tare da fad’in” ke Ki shiga hankalin ki wallahi ko in sauke fushina a kanki yanzu”. Kallon banza na watsa mata nace .”da gaske kike.” ? Tace.” Zan sanya ne ayi min k’asa-k’asa dake shigeya ‘yar gidan malam Shehu sai tsabar girman kan tsaya.” Wawan mari na Kai mata ta dafe kuncin ta cike da tsoro! Ina numfar fashi nace.” Wato har kin manta dabi na dake ko? Shine kike ikirarin sawa a dake,to don durun Uwar ki ki saka ayi gunduwa-gunduwa dani shine kad’ai zai nuna min ke ‘yar gidan Bulget ce ubanki ba Santana ba ne.”

Ca kumo wuyana tayi ta hau d’ura min ashar!! Idonta yayi jazur!! Kafin ta Ankara na daki bakinta da gwiwar hannuna nace.” Dama Neman ki nake ruwa a jallo shegiya karuwa.” Ai kafin kace kwabo gurin ya soma cika da mutane Alina ta fad’i a gurin tana wani k’ifkifta ido bakinta na kumfa,dama ta saba daga zarar an fara fada da ita zata fad’i kasa tana burgima wai ita me aljanu.

Mimi da Munnu hankalin su ya tashi suka nufi offece din principal da sauri sauran ‘yan makaranta suka fara guduwa domin sun tsorata da abunda Alina take ni ko ina tsaye a kanta ko d’ar ba nayi. Malama Rakiya ce da aunt Lahira suka k’araso gurin hankali a tashe suka fara yi mata tofi, mintuna kusan ashirin sannan ta dawo dai-dai duk suka tattaramu suka tasa mu gaba zuwa offece din principal me gaba d’aya.
Fad’a sosai shugaban makaranta yayi mana tare da gargadin cewa idan mun San rigima za mu zo muyi ta zai soke mana shagalin murnar da mu tana da ranar candy sai kawai kowa yazo ya karb’i takkadun sa, ya tafi, hakuri muka bashi sosai sannan ya sallame mu muka futa daga ofis din gruop-gruop an tsaya sai gulma ake haka Alina ta futo jiki babu k’wari ta shiga motar ta ta tafi, mu kuwa sai bayan sallahr azuhur sannan mukayi sallama da k’awayenmu bayan mun tsaida ranar da zamu gudanar da murnar kammala makaranmu sati guda me zuwa, tare da futar da anko har kala uku duk ranar zamu sanya shi. Muka futo titi muna Neman abun hawa rana ta kwalle sosai gumi kawai nake ga wata irin yunwa na damuna dama ban karya ba gwara Mimi ta karya da k’yar muka samu a dai-dai sahu muka shiga, ya dauki hanya sai gida. Hira muke sosai cikin adai-dai tar kowa na fadin albarcin bakinsa, danja ta tsai damu, cike da jin haushi nace.” Na tsani ina cikin abun hawa danja ta tsaidani wallah………maganar tawa ta katse hango gefan fuskar sa da nayi kwance a cikin wata mutsiyaciyar mota silver sai shak’i take a can tsallakenmu, da sauri na d’auke kaina gabana na dukan uku-uku addu’a nake kar Allah yasa Mimi ko Munnu wata ta hango shi, a sace na k’ara kallon gefan haguna sai naga ya mak’ala airpix a kunne shi tare da gyara zaman shi ya d’ora pcap me wani irin ado a jikinta gani nayi yayi min wani bala’in kyau ban gane ko wane dressing ne a jikinshi ba, amma na tabbata k’ananun kaya ne tunda INA hango hannunshi yana latsa wayar sa, ga Rambow a gefan shi sai zare ido yake.

D’auke kaina nayi jin miyan bakina ya daskare ban tab’a tsayuwa na kare masa kallo ba sai yau, a zuciyata Nace “Ashe haka yake da bal’in kyau!!!!!

25/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

29

Ban sake kallon gefan da yake ba har aka bamu hannu, muka wuce Munnu ta kalle ni tare da fad’in”wai ya kikayi shiru sarkin kaud’i.” Ya mutse fuska ta tanayi nace.” Yunwa nake ji Wallahi.” Tace.” Ba Dole ba wannan uban ihu da kika sha, shiru kawai nayi mata zuciyata nacan ga tunanin guy nan, cikin zuciyata nace sai kyau amma babu kyawun hali. Munnu aka fara saukewa ta kalli ni tare da fad’i wa kika ce zamu bawa dinkimu “? Nace.” Kinsan dai ba zamu bawa Ummi ba ta lalata mana yadi maza zamu bawa dinkimu.” Tace.” Shikkenan yaushe zamu gidan aunty Hauwa ko kuma da kanmu zamu shiga kwari.” Nace.” Ki rabu da aunty Hauwa kawai muje da kanmu.”tace.” To shikkenan sai goben” muka ce “Allah ya kaimu ni da Mimi .me a dai-dai ya ja mu muka tafi ita kuma Munnu ta tsallaka titi ta shige layinsh.

A hankali motar ta silala ta shiga cikin harabar gidan. Rambow ya futo da sauri ya bud’e masa kofar motar tare da k’okarin karb’ar wayoyin hannunsa.
Girgiza masa kai kurrum yayi ya wuce shi cikin sassarafa, suka rufa masa baya.

Dattijiwa kamillaliya na zaune cikin kujera tana sanye da atampah Ghana kamar ko da yaushe sai kamshi parlor yake tana zaune tana kallon tv tashar sunnah tv suna wa’azi, gefan ta wata matashiyar budurwa ce a zaune tana kallo ita.

Ya shiga da Sallama a bakinsa. Da sauri Hafsa ta kalli kofar shigowa jin muryarsa taji wani sanyi na kwarara a cikin zuciyarta. Cike da kunya ta d’auke kanta.

Granny tace.” Dan halak kaki jinin ambato dama yanzu nake fada miki zai shigo tunda yau juma’a.”

Hafsa ta yi k’asa da kanta tana murmushi . cikin yanayin tafiyar sa ya k’araso kusa da kakar tasa ya zauna gefan ta, tare da gaishe ta. Ta amsa cike da walwala da farin ciki tace.” Ga k’anwar ka nan tana zaman jiran kazo Ku gaisa.” Cikin rashin fahimta yake kallon Hafsa dake sine kai yace.” Granny wacece wannan.”? Cike da takaici tace.” Hafsa zaka ce baka sani ba kai kuwa.” Sosa kansa yayi tare da fad’in” banda abunki to a ina zan santa na dai ga tana kama da Innah Suwaiba.” Granny tace.” To ‘yar autar ta ce ai.” Sosa kansa yayi a karo na biyu yace.” Ayya! Ai kin San ni ba sanin ‘yayan ta nayi ba sosai wallahi in banda Musbahu da Zaraddini suka kadai zan sheda a cikinsu.”

Granny tace.” Ai dole kai da ba ziyara kake ba dole ka kasa saninta , sunanta Hafsatu.” Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya kalli Hafsa a nutse yace.” Hafsa ya gida ya makaranta.” Ba kinta na rawa tace.” Lafiya Lou alhamdullahi. ” yace.” Ina Ina Suwaibah tana lafiya.”? “Lafiyan ta lau tace ma a gaishe ka tunda ka daina zuwa.” Murmushi yayi kawai be komai ba.” Granny tace. “Ai ka saba dama da anyi magana ka sosa kai ya kamata dai cikin wannan satin kaje.” Yace.” Insha Allah zanje ayyuka ne suka min yawa ke kanki kin sani.” Tace” na sani amma ai ana barin halak da kunya.” Shiru kawai yayi mata tana surutai wayarsa yake dannawa yayin da Hafsa take ta satar kallonsa tana ji kamar ta had’iye shi ta huta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button