BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Wanka nayi na futo na tsuguna bakin rijiyar na d’aura alwala, lokacin da na shiga dakinmu Mimi ta kwanta tana lumshe idonta dama ita sarkin bacci, duguwar Riga na zura na sanya sabon hijabina na tada sallah duk sai da na rama sallolina nayi addu’a sannan na mike had’e da ninke daddumar na aje ta, ba tare da na cire hijab dina ba na nufi kicin Fula’s din da ake zuba mana abunci na dauko na dauko dugon jug na Debi ruwa a randa na wuce dakinmu ba tare da na kalli kofar dakin Ummamu ba.

A hankali nake cin abunci kamar me cin magani ko rabi ban ci ba na rufe Fula’s din, ruwa na d’auka nasha. Jin gina kaina nayi jikin katifa INA addu’a Allah yasa nannauyan bacci ya d’auke ni domin bana so tunanin guy nan ya dame ni.. Haka kurum daga na tuna shi a ko wane hali sai gabana ya yanke ya fad’i!

Allah ya amshi addu’a ta bacci naji a idona nayi saurin hayewa katifar had’e da runtse idona kafin minti biyar bacci ya kwashe ni, me nauyin gaske!


Shi kuwa Amjadu bayan tafiyar su, mamaki yake sosai yanda iyayen ta suke da kula da tsantse ni gaskiya sun burge shi sosai kuma yarinyar ta kara samun girma a cikin zuciyar sa,, kashe wayonyinsa yayi duka ya kwanta shima domin wani irin bacci yake, abunda da Wanda ya kwana ya yini a tsaye.

Asubah ta gari Young millionaire


Me girma governor hankalinsa ya kai kololuwa tashi sosai yanda jama’ar gari suke zaginsa kuma suna zargin sa, dole ne ya zauna da manya ‘yan kasuwa kamar su Mai citta, hankalinsa bai kara tashi ba sai da ya saurin Maganar Amjadu ta yau inda ‘yan jarida suke masa tambayar shin yana sha’awar shiyasa, hankalinsa ya tashi sosai da yaga jama’ar gari suna ihu tare da fadin”Muna sonka zamu Mara ka baya duk inda kake.” : Lokaci kankani yaji wata irin muguwar tsanar yaro ta kara shiga zuciyarsa yana ganin da alama yaron yana da farin jinin jama’a, kuma alumma zasu yi sauya masa ra’ayin sa ya fara sha’awar siyasa Wanda yake ganin haka kamar karshen mulkinsa ne yazo gashi yana so yayi tazarce, dole nema ya sake tsaurara matai kuma zai k’irk’iri abubuwa Wanda zasu jawo hankalin allumma su dawo kansa. Da wannan shawarar ya kira Alhaji Hashimu ya fada masa cewar gobe k’arfe goma na safe ya zo gidan gwamnati zasu tattauna magana me muhimamci.


Ko da na tashi da safe babu Wanda na kula ita kanta Umma gaisuwa ce kawai ta shiga tsakanina da ita, na koma dakinmu na kwanta zuciyata duk babu dad’i. Mimi ta shigo dakin hannunta d’auke da jug cike da koko d’ayan hannun kuma takardar k’osai CE,ta aje tare da fadin ” ki tashi mu karya duk wannan nukufurcin babu inda zai kai ki.” Ganin yanda ta damu dani ne yasa na mike zaune muka fara karya wa.

Bayan mun gama tace.” Ya Aminu yace.” Mu dauki kud’in atampar a cikin kud’in jiya.” Nace” kudina ne babu Wanda ya Isa ya tab’a min bayan sun gama ce min ‘yar iska kuma zasu ci kud’in iskan ci kenan.” Na karasa maganar raina w bace.!! Mimi tace” duk abunki dai ba a canzawa towo suna dole kiyi hakuri dasu,kuma ni banga laifin su.” Nace” ai baza ki gani ba Mimi tunda ba ke aka yi wa ba.” Mimi dai shiru tayi min ganin yanda na hayayyak’o mata da masifa.

Muryar Umma naji tana kwala min kira, amsa wa nayi na mike da sauri. Daga bakin kofa na tsaya nace” Umma gani” Sam naki kallon Ya Aminu dake tsaye yayi shirin makaranta.

Tace.” Idan anjima aunt Ku zata zo sai kuje Ku siyo shaddar da atamfar ga dubu ashirin a cikin kud’in dole a fada miki tunda hakkin ki ne.”
“To” kawai nace na kama hanya zan koma daki. Ya Aminu yace.” Dawo Dan ubanki ba,a gama magana ba zaki tafi.” Rai abace nace” nifa na tsani wannan abunda kake min haka kawai sai ka dinga yi min tsawa kana hantara haka jiya a gaban mutane ka tsinkani ni gaskiya ka daina min irin haka bana so.”Hannu ya kawo zai dake ni na kauce da sauri ina zumb’ura baki! Yace.” Idan na kara me zaki min? kaji min Mara kunyar yarinya ko.” Umma tace”kai tsiyata da kai saurin duka ka daina don Allah.” Yace” Umma wannan yarinyar ai duka ne maganin ta.” Nace”wallahi Umma baga yanda jiya ya dinga min masifa ba a gaban mutumin nan. ” Umma tace.” To ke meye damuwar ki.? Shiru nayi kawai. Ya Aminu ya wuce Yana mata sallama ita kuma sai fatan alkairi take masa, kallona tayi tace” kuyi sauri Ku gama aikin Ku kafin tazo domin kun santa da azazzala.” Nace” toum Umma” Mimi na kwalawa kira ta futo muka fara aikin gida.


Yana zaune a gefen bed jikinsa daure da wani faffad’an towol da alama daga Wanka ya futo Loptop dinsa ce a cinyar sa, suna magana da babban abokin shi Anthony dake can Chana. Dama duk yana da labarin abunda ya faru da abokin nasa shine suke shawarwarin abunda za’ayi.Anthony yace.” Company uku ya kamata a bude Wanda zai dinga kawo ko wane irin kaya daga na hausawa har na turawa, daya a Chana d’aya a America d’aya a nan kano din, saboda haka k’wararraun ma’akata zai zo dasu cikin wannan satin a fara aikin gurin.” Amjad yaji dadin wannan shawara da abokisa ya bashi gashi dai arne ne amma yafi wani musulimin kishin musulunci, nan ya amunce da shawarar abokin nasa.sun tsaida rana Monday Anthony zai shigo najeria tare da ma’aikata domin a fara gudanan da aikin sabon company me zaman kansa.


Me girma governor ya kalli Mai citta murya a cunkushe yace.” Ina fatan jiya ka saurarin maganar wannan yaron ko.”? Mai citta yayi kamar bai fahimci wa yake nufi ba.
Yace.” Ranka shi Dade wane yaro ne.”? Me girma governor ya daki! Tebur din da yake gabansa ransa a bace yace.” Young millionaire ne zaka ce baka fahimta ba, ko wace kafar sadarwa tana watsa muryarsa jama’ar gari suna ihu! A kansa tare da bashi goyon baya ko ta Ina, wannan nasarar da ya samu ina me tattabar maka da cewa, ni asara ce a gare ni, domin mutukar mutanan gari sukayi mubayi’a dashi to babu shakka kashina ya bushe 4+4 din da nake so nayi bazan samu ba.”
[10/30, 10:50 AM] Binta U Abbale????: Mai citta hau inda-inda! Cike da takaici da jin haushi governor ya kunna wayarshi had’e da bude rocouding na muryar Amjadu ya mika masa.

Shima sai da jikinsa yayi sanyi, jin hayaniyar jama’ar gari da ihu duk a kam Amjad. Gyad’a kai yayi yace.” Yanzu meye abinyi.”? Governor yace.” Dole ne ku ne mi maslaha dashi, ko kuma Ku zauna kuyi shawarwari a tsakanin ku, Ku manyan yan kasuwa abunda zai fishhe Ku, saboda duk abunda nasa aka yi wannan yaron DOMIN in faranta muku ne, nima sai kuyi kokari kuga na zauna kan kujerarar mulki shekara takwas.” Share gumi! Me citta yayi cikin zuciyarsa yake cewa” lallai ubangiji me kyauta a kan bawan sa wani lokacin akan yi wa mutum mugun Abu sai ya zama alkairi a gareshi, mutukar ubangiji ya so bawa da rahamarsa ta babu shakka babu wani d’an Adam d’in da ya isa ya hana faruwar haka…. Yace.” Ranka ya dad’e ina ganin zamu fara bin malamai da ‘yan tsubbu kan yaron nan domin naga kansa da tauri! Ina ganin idan aka nakasa masa wani b’angare na jikinsa tou sai ya nemi guri ya zauna, kaga kenan babu shi babu wani mulki.”

Governor yace.” Ni dai babu ruwana duk abunda zakuyi kuje kuyi kujera ta kawai na sani idan ba haka ba, kafin na sauka daga kan mulki wallahi duk sai na ruguza Ku.” Mai citta yace.” Duk baza’ayi haka ba ranka ya Dade zamu San abun yi, insha Allahu.”.
Sallama sukayi ko wanne ransa babu dad’i.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button