BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Me citta na cika shekara biyu Amjad ya karb’o shi daga gidan kaso tare da saka hannun alkali me makon me citta ya gane mecece duniya bayan ya futo sai ya sake d’aura damarar ganin bayan Amjad ko ta halin k’aka ne

Wannan shine mussababin abunda ya tsananta gaba a tsakanin sa da Alhaji Hashimu me citta.

Zamu dawo ainihin labari a pege na gaba

19/October/2009
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

23

Kallo Umma ta bini dashi har na shige d’akinta simi-simi ina addu’ar Allah yasa kar ta tuheme ni da wata magana. Aikuwa ina cikin kuryar d’akinta bayan na idar da sallah ina Jan carbi Ta kwala min kira tana daga parlor gabana ya fad’i sosai na mike na futa lokacin gari ya soma haske Mimi na kwance a kan abun sallah a gefan ta da alama ta idar da sallah ne, tace.” Zauna in yi mini tsaye aka.” Zama nayi kusa da ita ta aje carbin hannunta tana kallona cikin nazari daga bisani ta ambaci sunana da “Asma’u” na d’ago kaina tare da amsawa cike da tuhuma tace “wankan me kikayi da asubar fari” shiru nayi saboda bani da amsar da zan bata domin dai tunda nake ban taba Wanka da asubah ko da ko wankan tsarki ne na alada tace “ba dake nake magana bane.” Zuciyata ta saka min wani Abu da sauri nace.” Umma kin San jiya na Sha magugguna to shine na tashi naji jikina ya jike da gumi ina jin zafi sosai shine na watsa ruwa.” Na kare maganar bakina na rawa. Shiru tayi tana nazarin magana ta minti biyar tace.” Ban yarda da maganar ki ba Asma’u. ” na dago kaina ina kallonta nace.” To Umma ke wane Wanka kike tunani zanyi da asubah.? Umma tace.” Na sani ko kin fara mafarki aure kike so.” K’irjina na dafe ina zaro ido nace.” Wallahi a’a Umma.’ Tace” bana son munafurci wallahi idan aure kike so sai kicewa Musa ya futo kawai ni ba yarinya bace duk abunda kike ciki kamar a tafin hannuna kike.” Ina kallon Mimi tana kunshe dariya, hararata nayi cike da takaici nace.” Umma ki bar maganar nan don Allah ni kam Musa bai min ba wallahi.” Na fada ina zumb’ura baki tace.” To sai ki nemo wani domin naga aure ki kike so sai ai miki. ” kafin ince komai sai ga Yaya Aminu ya futo Cikin shirin makaranta ya watsa mugun kallo tare da fadin.” Wallahi Umma yarinyar bata da mutumci d’azu ina mata magana ta wuce tana k’okarin zagina.” Yafad’a yana k’okarin zama, Umma tace.” Nima fad’in da nake Mata kenan ai Yaya Aminu yace.” Idan jarrabawar su ta futo Zan musu kokari su samu su je legal ko FCE ko dufoloma su samu kafin suyi aure. Umma tace.” Da ko ka kyauta wallahi amma ina ganin ai ba karatun suke so ba aure su ke so.” Mimi ta mike zaune da sauri tace.” A’a Umma muna so wallahi ko baba Nafi’u ma yace.” Zai nema mana makaranta idan jarrabawar mu ta futo mu cigaba.” Umma tace.” Ai fa ke da kike da me uwa a gidin murhu.” Aminu yace.” Wallahi na manta dashi Bari in daina wahalar da kaina kawai tunda yana da ra’ayin Ku cigaba sai Ku cigaba kawai.
Umma tace.” Amma idan miji yazo dole a ajiye karatu ayi aure. Mimi ta sunkuyar da kanta wai ita kunya, nace”a’a Umma aure sinna ce haka ma karatu yana da mutukar muhimanci garemu idan mun fara sai ayi yarjejeniya da Wanda zai auremu.” Yaya Aminu ya kawo hannu zai buge min bakina na kauce da sauri yace.” Shegiya me bakin magana ke ko kunya bakiji ba gaban Umma kike wannan maganar cikin kukuni nace.” Ai gaskiya ce”
[10/21, 8:00 AM] ????: Mik’ewa yayi da niyar futa na zabura! Da sauri na b’uya bayan Umma hararata yayi kurrum yace.” Umma zan tafi.” Umma tace.” Bazaka tsaya ka karya ba.” Girgiza Kai yayi yace.” Muna da darasi k’arfe bakwai bana so na makara” Umma tace
” To Allah ya bada sa’a” ameen yace ya futa kafad’arsa rataye da jaka ta makaranta, murmushi nayi a fili nace “Yaya Aminu Dan makaranta” Umma tace ” da kikaga ya futa ko.” ? Dariya muka sa ni da Mimi Umma ta mik’e da nufi zuwa kicin tace.” Ai ya kamata Ku shirya kuje gidan Kawun NAKU Nafi’u kun kwana biyu baku je ba.” Nace wallahi kuwa Umma zamuje yau insha Allah” kicin ta nufa muka bita domin kama mata ayyuka yau Umma awara tayi mana da kunun tsamiya wai haka na dinga dabkar yaji duk da attaruhun da aka saka cikin awarar hummm ni kam ina son yajin barkono a rayuwata. Muna gama karyawa muka fara aikin gida ita kuma Umma tana harkar cinikin ta da yara har da Matan aure ma masu shigowa. Bayan mun gama mukayi wanka.

Mimi ta Ciro mana wani les baki da ratsin ja a jikinsa na waccan sallahr ne. Wai shi zamu sa nace “sai dai in ke kika saka wallahi kin San na tsani les din shine zaki wani Ciro mana shi.” Mimi tace” naga mun Dade bamu saka shi ba.” Nace.” Ki saka ke ban hanaki ba.” Kallo na take ina birkito kayan cikin akwatuna na futo da wata atampa haitaget anyi min doguwar Riga me madauri daga baya hannun rigar dogone amma an tsaga shi sosai duk kasan galalin hannuna in nasa rigar ana gani blue and orange ne na amma blue yafi yawa a jikinta saboda haka na d’auko mayafi orange na aje. Mimi tace” kin Mayan cewa atampar nan WALLAHI .” nace “tanayi min kyau ne Mimi.” Tab’e baki tayi tace.” Dinkin yana nuna tsaracin ciki kina daga hannu hammta a waje.” Duka na Kai mata ta kauce da sauri tana dariya nace.” K’aryar ki kice HAMMATA ta na wari ko kiga gashi ko daya kullum Cikin aski nake ke zaki fadawa wani saboda kin San na tsani warin hammata.” Mimi ta kyalkyale da dariya tana fadin “wallahi har kin tuna min da Hafsat me warin.” Dariya na sa nace.” Ni na manta da ita wallahi.” Mimi tace.” Asma’u baki da mutumci WALLAHI haka kika tasa Hafsa a gaba a skull duk kika tsagwame ta da ta matso daks dimmu zaki fara tsokanrta Me warin ham Allah sarki Hafsa tun bata ganewa ta gane cewar da ita kike dole dai kika saka ta ta daina zuwa gurimu dimu Nace.” Wallahi Mimi na tsani inga mace tana kazanta shiyasa na takurawa Hafsa in ta fahimta sai ta gyara haba!tasan zata shigo cikin makaranta cikin mutane baza ta tsaftace jikinta ba nifa wallahi mijina zai ga tsafta domin shi kanshi kullum cikin kyalkyale masa ji nake.” Mimi tace.” Ga manyan mata hummm mijin da bai zo ba ana masa tanadi lallai wannan me sa’a ne.” Nace fad’i ki kara Mimi duk namijin da ya same ni ya tsinci dami akala domin sai na sanja masa rayuwa ummm! Mimi kenan ni nasan wacece ni.” Mimi tace “maganar Umma ta futo lallai Asma’u aure kike so.” Hararata nayi nace “don Allah tashi ki saka kayan ki , e aure nake so Mimi waye zaiki sinnar Annabi muhammadu.” Mimi ta mike tana saka kaya tace.” Babu gaskiya kam Allah dai ya zab’a mana nagari.” Nace ameen ya rabbi.

Mun futo a kintse Sosai mu kayi kyau Mimi tasha kwalliyar fuska ni ko hoda kawai na saka sai kwalli Dana zirara ko man leb’e ban saka ba, Umma ta kalleni tare da fadin ” Asma’u ban ce ki daina saka atampar nan ba haka kurum kinje an miki lalataccan dinki ko.”? Nace Umma duba fa ki gani atampar da kyaunta kuma ni duk cikin kayana nafi sonta wallahi.” Umma tace.” Ke kika sani ai ba kyawun atampar ne abun dubawa dinkin ne.” Nace Umma na kai wa Ummi makociya ta gyara min hannu” shiru kawai Umma tayi min domin tasan duk tsarina ne, tace.” Kar Ku kai magariba baku dawo gidan nan ba.” Muka ce to Umma” tace Ku daina min da Kawun NAKU da Mamansu Munubiya” muka je zata ji insha Allah. Nan muka futa muna taku dai-dai mussaman ni sau kace wata ‘yar gidan shugaban kasa. Da kafa muka k’arasa bakin titi muka tsaya domin jiran abun hawa. Wasu ‘yan mata suka zo wucewa ta gefenmu nace ” Mimi kinga irin handbag dina ko ajikin waccan” Mimi ta kallesu tare da fadin “aikuwa irinta CE.” Nace.” Anya ko Mimi bazan je in d’auko kayata ba” tace” kin dai ji abunda Umma tace don Allah kar ki jawo mana wata Matsalar ” shiru nayi mata kawai ina sak’e-sak’e. A dai-dai ta sahu ta tsayar mana tayi ciniki dashi tare da fada mana inda zai kaimu, muka shiga, mun Dan yi nisa Mimi tace.” Idan mun futo daga gidan Kawu Nafi’u mu biya gudansu Hafsa mana tunda kusa ne.” Nace “muje mana ai babu komai. ” Mimi hira take min ni ko ina can tunanin yadda za’ayi in d’auko handbag dina gidan guy nan . mu ka sauka Titin wajan gidan marigayi Ummaru ta’ambu da kafa muka dinga shiga lungunan kafin mu Isa gidan Kawu Nafi’u muna shiga yaran gidan suka rungume Mimi suna ihu!! Kallonsu nake INA dariya nace” nu baku sann ba kenan” su dawo kaina nan Mamansa Munnu ta futo tana mana maraba tace Ku shigo ciki yara sun hanaku shigowa . nan muka shiga parlor me d’auke da kujeru biyar da kafet malale a tsakiyar gefe friji ne sai kayan kallo lavuleye kewaye a parlor ka hotunan shuwagabbanin kasa a manne a bango kana ganin tsarin gidan kasan na ‘yan boko ne

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button