BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

“Humm ai ba k’aramin cin zalinmu guy nan yayi ba ni kaina baccin nake ji.’ Na fada INA k’okarin ciro kaya cikin akwatuna.

Mimi ta mike ta futa ni kuma na sanya riga da siket na atamfa nicham na saka kudusdusar wayata a chaji na bi bayan Mimi. Zama nayi kusa da aunty Hauwa na jawo ledar ta janye abarta tana hararata nace.” Haba big aunt meye duniyar kiyi hakuri wallahi wancan purple din mayafin yamin kyau ki bani shi.” Tace.” Ai kinyi wa kanki sai dai kiga ana yi.” Marairaicewa nayi na jawo Isilam nace.” Babyna cewa momyn ki tayi hakuri ta bani gyale guda d’aya.” Aikuwa Islam ta jawo mayafin da Mamanta ta kwace a hannuna ta mik’o min na mike da sauri zan gudu aunty ta rike min kafafuna wai Dole sai bata mayafin ni kuma naki saki.

Yaya Musa ne yayi sallama ya shigi gidan ganin abunda yake faruwa ne yasa yace.” Ke Hauwa anyi babbar kwabo sakar mata k’afafu kar ki k’arya ta na wane kud’in mayafin naki sai a sai mata.” Dake sun saba wasa a tsakanisu tace.” E a sai mata mana don ni nayi rantsuwar bazan bata ba.” Yaya Musa ya zauna Tar da zura hannunsa cikin aljuhu ya futo da kudi yana fadin .” am ce miki ki sake ta ki fad’i kud’in gyalan naki.” Hannu ta mika masa tana fad’in.” Kud’in gyale dubu hudu ne da Dari biyar.” Da sauri nace.” Yaya Musa kar ka bata Dari biyar din kai ka nemi ragi ita ta Dora akan dubu hudin ribar ta CE.”
Dariya Yaya Musa yayi yace.” Kina hannu amma kina surutu ko ki bari in fanshe ki a hannunta. ” aunt tace.” Rabu da ita dai.” Dubu biyar ya mik’a mata ta karb’a sannan ta sake ni, babu kunya ta zura kud’in cikin purse dinta.

Yaya Musa yace.” Ke kam son kudin ki yayi miki yawa Wallahi. ” dariya aunt tasa tace.” Yo waye yak’i kudi ko dangote kullum cikin nema yake bare ni gallafiri me naiman na koko.” Dariya kawai Musa yake, sai da yayi me isar sa sannan ya juya yana gaida Umma cikin girmamawa suka gaisa tana tambayar sa mutan gidan yace.” Kowa lafiya. Kusa dashi na zauna gabana na fad’uwa domin ina jin tsoro kar ya fadawa cewar ba a gudansu muka kwana ba Gashi munyi wa Umma k’arya.Ashe Mimi ma tunanin da take kenan muka kalli juna gabanmu na fad’uwa

Umma tace.” Yau kazo gaishe mu kenan.” Sunkuyar da kansa kasa yayi yana murmushi yace.” Nazo gurin Asamau ne,.” Umma da aunt sun gane munufar sa, oho!! Ni San ban fahimci wai sona yake ba. Jin abunda yace ne yasa Umma ta tashi ta shige kuryar daki cike fa kunya, aunty ma ta mik’e ta bita tana murmushi. Muka kadai ne mukayi shaura, INA kallon Mimi ta sauke ajiyar zuciya nasan ko ta mecece nasa dariya ina fadin. ” kura sarkin tsoro kenan. ” hararata tayi ta mike tana niyar fucewa tare da fadin “Masoya asha soyayya lafiya ” kallo na bita dashi cike da mamakin abunda tace.” Naji muryar Yaya Musa yana cewa. ” ke Asma’u akwai Wanda ya kaiki tsoro kuwa.”? Juyowa nayi ina kallonsa na gyara yanayin fuskata sosai cikin zuciyata nace kardai abunda Mimi tafad’a gaskiya Musa sona yake lallai ma kuwa. Nace.” Ya Musa ni nan da ka ganni kafin kaga abunda ya furgita ni zaka jima.” Ya kyalkyale da dariya kamar wani soko yana gyara zama yace.” Allah tawan.”. ? Allah tawan.” Na maimaita a abunda ya fada a zuciya lallai wannan bashi da hankali yo ko maza sun kare a duniya ni me zanci dashi tabd’ijam ! Ya wani gyara zama yana kashe min ido tare da fad’in.” Asma’u zauna sosai zamuyi magana dake ta fahimta. ” nace.” Ai a zaune nake Yaya Musa.” Murmushi yayi min yace.” Hak’ika Asma’u zuciya ta kamu da so da kaunar ki tun kina ‘yar k’arama nake sonki ina fatan zaki amunce mun muyi auran zumunci domin raya sinnar Annabi MUHAMMADU .” nace slw.” Yace.” To kinji abunda yake tafe dani gurin ki.Murmushi nayi me kunshe da abubuwa da dama nace.” Yaya Musa kenan,a gaskiya bazan munafurce ka ba, bani da ra’ayin auran zumunci a rayuwata kawai dai zan cigaba da yi maka fatan samun mace wacce ta fini na gode da so da kauna.” Jiki a sanyaye yake kallona bakinsa na rawa na lura magana yake so yayi amma ya kasa. Mik’ewa nayi nace.” Kar kace na wukalanta ka ni na shiga ciki.” Kallo ya bini dashi cike da mamaki har na futa. Ya Dade zaune a gurin yana tunanin Asma’u yanzu shi ta kalli tsabar idonsa tace bata sonsa lallai ko taso ko taki sai ya aure ta zai gwada mata iko tabbas ruwa ba sa’an kwando bane.” Haka ya mike ya bar gidan ba tare da yayiwa kowa sallama ba.

Ina shiga dakin mu na tadda Mimi na ninke kayanta ta dago ta kalle ni tare da fadin.” Har kun gama soyayyar.” Duka na kai mata ta goce tana Dariya . kan katifa na zube ina Jan tsaki nace.” Wallahi wannan musan ya ma rainawa kansa hankali duk ‘yan matan dake cikin birnin Kano ya rasa wacce zai ce yana so sai ni,wallahi ji nayi kamar in mangare shi Dan haushi.” Mimi ta dinga dariya tace.”To shi ke ya hango saboda haka ki bashi hadin kai kawai musha buki.” Wani dukan na kaima ta raina a bace, yanzu na samu nasarar samunta a kafad’a ta rike gurin tana kallona da baki a bude, ta bude baki kenan zatayi magana na katseta ta hanyar cewa.” Sallah!rufe min baki,sai dai idan kece zaki aure shi wallahi ni me zanyi DASHI yana tafiya salo-salo da kafad’u a sauke hummmm! Wannan auran sa ai takaici ne wallahi.”

Mimi ta kwanta tana sheka Dariya fad’i take.” Asma’u baki da kirki wallahi gaskiya kin yanki Yaya Musa santalelen saurayi haka mijin mata hudu kikewa wannan cin mutum cin.” Nace.” Wallahi da gaske nake wannan ya kuskura yayi mata hudu guduwa zasuyi su barshi wai baki ga yanayin sa bane babu wani kuzari da karsashi komai salo salo.”

Mimi ta gyara zama tana kallona tace.” Nifa ban fahimci inda kika dosa ba.”? Nace.” Yaya Musa bazai yi wani k’arfin kirki ba gurin sex.” Mimi ta saka salati tana kallona a tsorace tace.” Ke yaya akai kika sani ke ba bazawara balle kice kin San namiji.”

Tsaka naja tare da fadin ” ke k’yaleni don Allah DUK da nake budurwa ina gane maza wallahi masu jarumta da ragwaye Bari in miki misali da guy nan na jiya wannan shi kana ganinshi kaga jarumi a komai ma, misali kawai namiki dashi shi kuwa Yaya Musa ai sai a slow daka gani.
Lumshe ido naga Mimi nayi nace.” Ke meye haka kikayi.”? Bude idonta tayi tace.” Wallahi Asama ban san me yasa ba idan na tuna wannan guy some times sai inji gabana yana fad’uwa ina jin tsigar jikina na tashi wallahi yanzu ma da kika ambace shi haka naji.” Wata irin faduwar ga bace ta rikito min tuni naji miyau din bakina ya tsinke bakina ya zama lami babu tes ko na kwabo dake ina da b’oye abu sai nayi saurin aro jarumta na aza a raina na kalli Mimi murya a dage nace.” Ko sonshi kike ne.?”

Cike da rashin madafa Mimi tace.” Ban sani ba Asma.” Tab’e bakina nayi nace.” Wannan dai duk alamar so ce da kika fada.” Kwanciya tayi kan katifa tana lumshe ido naji kamar in make ta don haushi!! Nace.” Ki daina wahalar da kanki kuma kar ki saka abunda kika san baza ki samu ba cikin ranki kin San dai wannan guy yayi miki nisa nesa ba kusa ba, kudi kyau mulki bayan wannan kuma duk wata mace tana so ta samarwa ‘yayanta uba nagari kin San wannan kuwa mugun d’an iska ne gwara ki cire shi a ranki.”

Tashi zaune tayi na kalli fuskarta naga ta sauya lokaci guda nima na sauya tawa tace.” Haba Asma’u ki daina CE masa Dan iska, ita shiriya ta Allah ce wallahi bakiji yanda naji a zuciya ta ba da kika kirashi haka insha Allahu Zai dawo hanya madaidaiciya.” Nace.” Ke dai so ya rufe miki ido kawai kin kasa gano abunda ake so ki gano irin wad’annan ‘yan barikin basa tab’a daina halinsu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button