BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Zarya na fara a dakin ina kaiwa ina kawo wa, da sauri naje na daki kofar! Da kafata kamar wata wacce ta samu tab’in hankali da k’arfi nace Idan baka bude min kofar nan ba kai ba d’an halak bane wallahi!!!Abunka da dare shiru ko INA yasa magana ta ta cika parlor murmushi ya saki a hankali yace.” Yarinya inan zuwa gurin ki,zaki fada min wace irin alk’ace a tsakanin dake da har kika samu dama a kaina….

22/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

22

Sama-sama Asma’u take jin Mimi tana magana wani irin sarawa kanta yakeyi ga wani sanyi me ratsa jiki tana ji a jikinta,dishi-dishi ta ke kallon Mimi tana sallah lumshe idonta tayi tana kara takure jikinta.Mimi ta idar sallahr ko addu’a bata yi ta mike tana ninke abun sallah ta futa waje da sauri.Umma na kicin tana k’okarin raba abinci tace.” Umma In Kin zuba mana namu bani in je muci domin muje chamis din kinsan dole su taimabaya ko ta ci abunci nasan dai allura ce za ayi mata.” Umma ta mik’o mata Fula’s MA dai-dai ci cike da shinkafa da faduka da kifi d’anya abunci dai-dai na talaka tace.” Aikuwa domin Kin San wannam zazzab’in na maleria dole sai da allura.” Su duk a tunaninsu maleria ce take damun Asma’u. Mimi ta wuce da sauri tana shiga ta hau kiran sunanta “Asma’u tashi muci abunci muje a dubaki.” Bude idona nayi a hankali nace.”Mimi k’yaleni da chamis din nan don Allah.” Sakin baki tayi tana kallona naja bargo na rufe kaina gaba daya ina takure wa.” Tace “Dole fa ki tashi WALLAHI ke taurin kanki ne matsala.” A hasale nace.” Dallah ki kyale ni wai jikin ki ko nawa da zaki dame ni.” K’arar!a kunnen Umma ta daga labule ta shigo rai a bace tace.” Gwara ma ki tashi tun kafin ranki ya b’aci ita meye laifin ta kawai Dan ta damu da lafiyarki shine kike mata tsawa.” Nace.” Umma nifa lafiya ta lao”. Tsaki taja tace.” Kin saba karya dama duk abunda ya same ki ke kika jawowa kanki wanka da magariba saboda haka ki tashi tun kafin raina ya b’aci.” Tana gama maganar ta ta fuce daga dakin.
Cike da jin haushin Mimi na tashi zaune ina hararta had’e cinyoyina nayi ina ya mutse fuska tace.” Ki sauk’o kasa mana.” A hasale nace.” Anki a sauko ki d’auko Fula’s din abunci ki dawo dashi kusa dani in kin damu.”Mimi tace.” Banza masifaffiya.” Shiru nayi mata ina hararata gefe guda ina matse cinyata Dan karta gane halin da nake ciki. Ta kalle ni cike da nazari tace.” Wai meye tun d’azu kike matse cinjyar ki kamar wacce taji ciwo.” “Ban sani ba.” Abunda nace da ita kenan na sha kunu. Tab’e bakinta tayi tace.” Mutum babu lafiya ma sai masifar tsiya.” Share ta nayi kawai na fara cin abunci a ya tsine.Kad’an na iya ci na mike a daddafe na futa waje domin wanke hannuna, sauri sauri Mimi ta gama ci itama ta futo hannuta rike da hijabai ta mik’a min na sanya itama tasa ta wanke hannunta muka tafi. Ko da Anas me chamis ya gama duba ni sam bai ga wata maleria ba maganin zazzab’i kawai ya bani muka dawo gida, nace.” Ki damu sai munje to munje muguwa kawai allurar dai da kike min fata bata samu ba.” Dariya Mimi ta sanya tana zolaya ta ni ko na sha kunu.muna shiga gida na dauki buta na d’aura alwala can dakin Umma na shiga nayi sallahr mariba da Isha’i na kwanta kan daddumar ina addua’a Allah yasa bacci ya d’auke ni. Aikuwa Allah ya taimaka ni bacci me nauyi ya kwashe ni, Umma tace.”tunda na samu bacci shikkinen Mimi ma ta dawo dakin a takaice nan muka kwana.


Granny ce take ta fama dashi ya fad’a mata abunda ta faru tunda ya shigo gidan take aikin rarrashin sa yana jin ta yak’i tanka mata sai kallon guri guda yake.cike da takaici tace.” Wannan a cikin musklan ma k’arshe ne kazo ka zauna kana min dacin rai nayi tambar duniya kamin shiru shikkenan.” Ta k’arashe maganar cike da takaici.”

Kallon gefan ido yayi mata yaji ta bashi tausayi Sam bata son damuwar sa ko kankanuwa yace.” Granny kin san Alhaji Hashimu abokin Dadyna ko.” ? Tace.” Ni ko nasan Hashimu me citta.” Yace.” To zan mai dashi prison wallahi.” !! “K’ull!! Tafad’a tana kallonsa ta cigaba da cewa.” Me yayi maka mutum magidanci me iyali zaka dauki hakkin su.” Murya a sama yace.” Yau ya assasa taro DOMIN a ci ma Dadyna mutumchi.” Shiru tayi saboda tasan da kiyayar dake tsakaninsu ba tun yau ba, amma dake tsohuwa ce me hangen nesa tace.” Sai ka kyaleshi ai da me rai ake ba da Wanda ya mutu ba. Mik’ewa yayi a zabure! Ya kai ya kawo a parlor yace.” Impossible ina Raye a duniya granny babu mahalukin da ya Isa ya taba min dadyna ban ta kurawa rayuwrsa ba.” Granny ta mike cike da tsoro tace.” To me zakayi masa? Ka k’yale shi mana ba sa’anka bane.” Ta k’arashe maganar tana kamo damtsen sa wai ita dole sai ta zaunar dashi kan kujera kamar tana Jan dutse yak’i motsa wa. Tace.” Dube ka sai wani huci kake jiki a murde kamar dan danne”zama yayi cikin kujera yana huci yace.” Granny yau me citta ya hada min taro har dasu governor da jama’a kan lallai sai na rushe company na na Magwan.” Tace.” Abunda bazai yiwu ba kenan lallai me citta Ashe yanan nan da bak’ar zuciyarsa. “
Granny ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin. ” Allah wannan bawa naka kai ka hallice shi kanai ka dora masa nauyin wannan dukiyar da ta hau kansa ina rik’on ka ka dafa masa cikin al’amuranshi ka tsare shi daga sharrin mahassada.”
Ta k’arashe maganar tana shafa kansa cike da tsantsar soyayya. Gyara kwanciyarsa yayi cikin kujerar ya lumshe idonsa yaji dadin addu’ar da kakarsa tayi masa a yanzu bashi da wacce ta fita a duniyar nan sai dangin mahaifiyar sa da ba wani sha kuwa yayi dasu ba, granny tace.” Ina Neman alfarma daya a gurinka.” Bude idonsa yayi amma be kalleta ba, tace.” Abunda ka kudurta kan Alhaji Hashimu ka hanye shi in ya kara sai ka dauki mataki.” Kallonta yayi da jajayen idonsa yace.” Kin samu amma da bakin ki kika ce idan ya k’aramin wani Abu in dauki mataki ko.”? Granny ta daga kanta tana murmushi yace.” Shikkenan ya wuce.” Dariya tayi tace.” Ho!! Dan nema kai dama soja ka zama da wannan halin naka.” Tab’e baki yayi kawai ya koma ya kwanta bai ce mata komai ba. Tace.” Bari in sa A kawo maka abunci ko.” Girgiza kai yayi kawai har yanzu idonsa na lumshe. Tace “me yasa to.”? ” b’acin rai ba zai barni ba.” Granny ta mike tsaye tana fadin.” Dole ko kaci abunci towo ne miyar kuka.” Bude idonsa yayi da sauri yana kallonta yace.” Sai dai kici abunki ko kin sa an kawo min bazan ci ba.” Granny ta wuce kicin tana fadin.” Dama si tsokanar ka nake Abunda nasan ba cinsa kake ba, aikuwa ka bar dad’i.” K’aramin tsaki yaja afili yace .” wai towo fad’ar sunansa ma a baki babu dadin ji malam Bahaushe kenan.

Wata lafiyyaye jolop rice wacce taji kayan lambu gami da kifi bushashe granny ta kawo masa cikin plate ta aje masa gabansa kamshi da take ne yasa ya bude idonsa tare da Dan tsurawa abuncin ido kad’an yace.” Wannan.”? Granny tace idon MA tambayi ne.” Murmushi yayi kawai ya d’auko cokali yana juya ya abunci yayi bisimillah ya fara ci a nutse.
Granny ta gyara zaman ta sosai tana yi masa labari duk Dan ta d’auke hankali sa ya ci abuncin sosai DOMIN San Amjad cin abunci bai dame shi ba.”
Cokali biyar yaci ya aje ya ya go tissue yana goge bakinsa . B’ata fuska granny tayi tace.” Ka koshi ne.”? Gyad’a kansa yayi yana k’okarin Mik’ewa tsaye. Tace.” Kai kam matarka zata sha fama da kai wallahi abunci ma sai kayi masa felek’e kace wancan kace wannan. Yana tafiya yake fadin.” To ke granny wa ya fada miki ni zanyi aure ke kadai kin ishe ni zaman duniya.”
Wani tayi masa tana hararsa tace. ” sai kayi kuma aure kamar kayi ka gama domin da kaina zan nemo maka matar cikin ‘yan uwa da abokan arziki.” Murmushi ya saki yana k’okarin futa dafa parlor yace.” Ki nemo wa ni dai amma bani ba kamar ni zaki nemo wa mace kuma wai ‘yar kano never. ” tace.” Sai kayi ni wannan turanci ba jinsa nake ba.” Dariya yasa yace.” Ni na tafi sai kin sake gani kuma Nazo kika kara min maganar aure to na bar zuwa gidan ki.” Granny tace.” ahaf!! Sai dai ko in baza ka zo ba WALLAHI na ma gano maka matar aure yarinyar kyakkyawa mai hankali nan makotanmu.” Fucewarsa yayi yana mamakin granny wai shi zatayi wa aure lallai ta d’auko da zafi. Yana futa su Rambow suka rufa masa baya dama duk suna tsaye bakin kofar parlor.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button