BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Ko kwana ba ayi ba ya fara shirye-shiryen tafiya domin dubo granny yana ganin yanzu ita kadai ce tayi masa saura hukumar makaranta ya sanarwa sosai suka jajanta masa. Yayi sallama da abokan shi Linda tana ji kamar ta bishi domin ta mugun sonsa a rayuwarta, haka dai suka rakashi har filin jirgi ya hau suna daga masa hannu.


Lokacin da Innah ta ganshi kukanta sai ya dawo sabo ta rungume shi tana kuka sosai tare da yiwa iyayanshi addu’a daurewa kawai yake domun baya so yayi hawaye a gabanta, ya nemi sallama daga hukumar asubitin domun yana so suka Isa can mahaifar tasu kamar yanda granny ta bukata cewar ya kaita ta gaisa da ‘yan uwanta tunda Allah yasa tana da rabo ganawa dasu.

Da suka Isa “yan uwa sun koka sosai da mutuwar Alhaji Abbas DOMIN shine jigonsu ta dalilinsa matane da dama sun far fado daga kangi na talauci, sukayi tayi masa addu’a shi da matar shi tare da fatan samun rahama gurin Ubangiji.

Satin uku suka dawo najeria inda labarin mutuwar Alhaji Abbas ya karad’e ko ina mussaman cikin kasuwanni Alhaji Hashim me citta duniya sabuwa a fili yayi ta nuna jajansa da mutuwar amma a zuciyarsa fal take da farin ciki yana gani duk wata duniyar Alhaji Abbas zata zama mallakinsa domin sun hada kasuwanci banking su daya duk wasu shagunanan Alhaji Abbas ya kane yanzu shi yake bada ido duk ciniki da akai yana lissafi Alhaji Dan Akushi na kara tunzurasa kullum suna mak’ale da juna suna kus-kus.

Kwanaki arba’in da faruwar al’amarin Amjadu ya fara bunkice kan dukiyar mahaifinsa duk wasu kadarori gami da shagunansa sai da ya bunkito da takkadun baking da yake ajiyar sun kai goma kowanne yana ajiya ga share iri-iri yana dasu a wannan lokaci in ka kalle shi sai ya baka tsoro saboda yadda ya koma hero saboda rashin fara’a kullum fuskarsa a murtuke take, har gida labari yq same shi cewar gasu Alhaji citta can suna facaka da dukiyar mahaifinsa yaji haka daga bakin mutum kusan biyar, kawai ya shirya zuwa kasuwar cikin shigar k’ananun kaya yaje vest ne da wando 3Qutar wuyanshi da siriryar sark’ haka kunnenshi da barma sai shek’i take ga uban kitsonshi wando ya nannade a bayanshi duk Wanda ya kalleshi a lokacin sai yace ba musulmi bane, ya dura cikin kasuwa jama’a suka dinga kallonsa wasu gani suke bature ne ko Dan India saboda Sam bai kama da baushen mutum ba, sai da sukaji Hausa a bakinsu suka tsinke da lamarinsa, d’aya daga cikin shagunan mahaifinsa ya zauna yasa aka kira masa me citta yana can sauran shagunan yana mulki da kallon yanda ake sauka kaya. Jin kira daga sama ya taso domin ya d’auka masu d’aukar kaya ne, ya zuwa idonsa yayi masa tozali da Amjadu gabansa ya fad’i cikin zuciyarsa yace me kuma ya dawo da yaron nan domin sun taba maganar da Alh Abbas cewa ba yanzu Amjad zai dawo ba sai yayi shekara hud’u daya zuciyar tace masa ki’la ya dawo ne kan mutuwar mahaifinsa, sai ya nufe shi yana da fara”a yana fadin’ Yaro na ka dawo Ashe.”?
Amjadu ya mik’e tsaye da sauri tare da daga masa hannu fuska a murtuke yace.” Duk wani Abu da kasan mallakin mahaifina ne ina bukatar ka hado ka kawo min har gida, nasan iya adadin dukiyar mahaifina dake hannunka saboda haka mutukar kana son zaman lafiya ka zare dukiyar ka domin bana bukatar ta a cikin tawa ina fatan ga gane.” Mai citta ya saki baki yana kallonsa cike da mamaki tabd’ijam ai abunda bazai yiwu bane ya fada a zuciyarsa, kwantar da muryarsa yayi zai rarrashe shi Amjad ya daka masa tsawa tare da fad’in ” INA da labarin b’arnar da kake kan dukiyar saboda haka babu abunda zaka CE min na baka daga nan zuwa dare ka hado takkadu ka kawo min ko in sanya a rufe shagunan kowa ya huta.”

Yana gama maganar sa ya fuce cikin zafin nama!

Me citta ya bishi da kallo gumi na tsiyaya a jikinsa yaran kanti suka fara murna domin zalintarsu kawai yakeyi zama yayi kan kujerar da Amjad din ya tashi yana jan numfashi, Zumbur!!! Ya mike ya futa kamar mahaukaci ya motarsa ya shige ya zauna tare da d’auko wayarsa wasu ‘yan daba ya kira da suke wata unguwa da tashahara a birnin kano sun kware gurin daba da sare kan mutane take ya fada musu abunda zasuyi masa,ya basu address din gidan Alhaji Abbas Wanda yanzu ya zama mallakin Amjadu.

Dari misalin sha biyu yana zaune harabar gidan shi kadai da karan sigari a hannunshi yana zuka zuciyarsa na saka masa yanda zaiyi da Mai citta kawai yaga suna haurowa daga sama DUK da security da aka keyawe gurin dashi.Mik’ewa yayi a nutse Amjad Jarumi ne sosai babu abunda yake furgita shi can yaga sun nufa bayan window din dakunansu suna zazzaga fetur, cikin zafin nama ya tafi da gudu ya sanya gwiwar hannusa guda ya daki kan d’aya tare da tad’o k’afar d’ayan suka zube a gurin suna nishi! Da hannu daya ya dunga Kansu har ya kaisu aininhin main parlor ya zauna kan kujera fuskarsa a murtuke yace.” Waye ya aiko Ku.”?

Ganin yanda muscle d’insa suke motsi sai abun ya basu tsoro suka nemi jarumantar su suka rasa baki na rawa daya daga cikinsu yace.” Me citta!!!!! Ne ya aiko mu mu kone gidan gaba daya yayi mana alk’awarin kudi har miliyan biyar biyar.”!

Murmushi yayi murya a sama yace”. Gud”!! Alhaji Hashimu me citta!!!!? D’ayan yace.” Yes sir.” Gyad’a kai yayi ya mike a zafafe! Ya daki bango ! Yakai ya kawo Cikin razananniyar tsawa yace.” Meye sunayen Ku.”?

Hada baki suka yi

Ma’aruf Amma ana kirana da “Rambow”

D’ayan yace.” Ni kuma Nasiru amma ana kirana da Doh-doh”. Gyad’a kai yayi yace.” Meye Matsalar Ku a rayuwa.”?

Sukayi shiru yace.” Baku da aiki sai kisan kai wato an turo Ku Ku kashe ni ko.”?

Sukayi shiru. Tsawa ya buga musu tare da sake fadin.” Meye Matsalar Ku a rayuwa ina tambayarku.” Suka hada baki gurin fadin.” KUDI ne sir.”

“Very Gud”!! Yafad’a da k’arfi. Mik’ewa yayi ya durfafi d’akinsa sai gashi ya futo da d’aurin KUDI da yawa a hannusa ya watsa musu a jiki gami da fadin ” gasu nan.
Cike da tsoro suke bin kud’in da ya watse a kasa kunya ta rufe su
suka sunkyar da Kansu kasa suna bashi hakuri zama yayi cikin kujera yana kallonsu mazaje sosai amma babu Sanar yi yace .” Ku bani takaitaccan tarihin Ku.”

A takaice suka gabatar masa da Kansu yace.” Zan d’auke Ku aiki zaku zama yarana INA fatan babu matsala, Har kusan kuka sukayi saboda farin ciki Ashe alheri ne ya shigo dasu gidan,lallai idan Allah yaso ka da alkairi babu mahalukin da ya iyasa ya hana, a takaice dai nan suka kwana. Da safe Amjad yasa suka kimtsa sosai suka shiga mota kai tsaye babu inda suka nufa sai court nan Amjad ya shigar da kara a ka karbo sammaci su ya sanya suka kai ma me citta har cikin kasuwa Wanda yake zaune yana jiran tsammani yaji labarin daga su Rambow kawai yaga sun mik’a masa takkada daga hair court kiran gaggawa. Ya dinga kallonsu bakinsa na rawa,ko saurarensa basuyi ba suka barshi a gurin yana zufa!!

Alkali yayiwa me citta fata-fata tare da tonan asiri gaban bainar jama’a da iyalansa me citta kuka ne kawai bai yi alkali yace dole kuma sai ya bawa Amjad tara ta miliyan biyar ko ya zauna gidan yari tsawon shekara biyar. A lokacin me citta ya dinga share hawaye tabbas idan ya bada miliyan biyar aka biyar na dukiyarsa ta yi kasa dama yaudarar su Rambow yake da yace zai basu miliyan biyan. Kawai sai ya zab’i zaman gidan yarin domin shi mutum ne me mugun San kud’in tsiya, aikuwa nan take Alkali yasa aka tasa keyarsa zuwa gidan kaso iyalinsa na kuka.
Ganin kukan da iyalinsa suke ne yasa Amjad ya kuduri niyar futo dashi amma ba yanzu ba sai yayi shekara biyu tukkuna ya San mecece duniya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button