BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

A zuciya ta nace kyau babu kyawun hali Allah ya sawake dube shi kamar ba shine ya gama sallah da addu’oi ba amma dubi yanda yayi wata shiga sai kace arne wanda ya futo daga kudu.

Mimi ya kalla fuskar shi babu walwala yace.” Ku tashi ku muje.” Mimi ta mike Zumbur . yayi gaba be ko kalli inda nake ba. Nima harara na bishi da ita na mike ina gyara zaman hijab dina,gefe guda kuma ina tunanin k’aryar da zamu sharara a gida, domin ina sane na kashe wayata saboda nasan za’ayi ta damuna da kira bani da amsar bayarwa.

Muna futa bodyguard d’insa na tsaye bakin kofa duk suna sanye da bakaken kaya hannunwan su da safa bak’a kana kallon fuskarsu zaka San babu wasa.

Suka fara kawo gaisuwa gurin ogansu, kallon banza nayi musu nayi gaba Mimi ta biyo bayana Simi-simi.

Doh!-doh ne naga yazo ya wuce ni da sauri yaje ya bud’e wata arniyar mota ba irin ta jiya ba, wannan daga ni ma sabuwa ce kalar ta ruwan zuma ne gaskiya motar ta burge ni.

Tun kafin ya k’araso saboda k’arfin hali irin nawa naje na kama murfin baya zan bude in shiga.

Wata azabbabiyar tsawa doh-doh ya buga mun fa sauri na saki murfin na m ma gefe ina zare ido.

Cike da karsashi ya k’araso ya shiga Alina ta shiga ta zauna kusa dashi, harararta nayi ina jin wani mugun haushin ta. Doh-doh ya maida murfin ya rufe ya zaga da sauri ya shiga Mazaunin sa.

Rambow ne ya zauna kusa dashi sai Alina sai ni Mimi ce ta k’arshe shiga.

Cike da ladabi Doh- doh yace.” Boss ina muka nufa ne.”?

Mimi ya d’an kalla da gefen ido yace.” Wace unguwa ne.”? Baki na rawa tace.” Badawa ne wajan giginyu.”

Yace.” To kaji ko”.?

“Yes sir.” Doh-doh ya fada yana k’okarin futa daga gidan.

Shiru motar babu wanda ya ce ci kanka gudu kawai take kan kwalta. Ina kallonshi a fakaice, ya makala airphone a kunnenshi sai gyad’a kai yake yana bin wak’ar da yake ji, ba daina najin muryar mawak’iyar daga bakinshi na fahimci janeefar Lopez ce.cikin wak’ar me taken a into mamah.

Kalle kalle nake domin in tantace wace anguwa ne muke ciki, Jambulo sai yanzu na gane unguwar akwai wata friend dinmu dake unguwar mun tab’a zuwa duba mahaifin wani lokaci da yayi hatsari. Muzo dai-dai kan kwana inda wasu gungun almajirai suke zaune da ‘yayansu maza da mata.

A hankali naji yace.” Tsaya anan.”

Doh-doh ya samu guri yayi parking. Da sauri shadow ya futo ya bude masa kofa ya futa. Ido na bishi dashi cike da mamaki ganin yana zuwa gurin almajiran nan. Aikuwa suma suna ganinshi suka fara gyarawa

D’aya bayan d’aya ya dinga binsu yana saka musu kudi Wanda ban San adadin su nasan dai ‘yan dubu-dubu ne. Duk yawansu sai da suka samu.

Cikin sauri ya dawo motar Shadow ya maida murfin ya rufe muka bar gurin.

Gaskiya ni da Mimi munyi mamaki sosai da sosai da lamarinsa daga k’arshe muka cigaba da tunanin yadda zata bulle mana a gida.

Kallon shi nake so nayi zuciyata tana hana ni, a sace na d’ago kaina muka had’a ido dashi ta mirror wani miskilin murmushi ya Sakar min yana sosa sumar shi. Na kauda kaina INA jan k’aramin tsaki, har yanzu da akwai k’ulli a kaina dangane da Alina.

Kwanar gidanmu Mimi ta nunawa Doh-doh nayi saurin dago kaina tare da fad’in.” Kai sauke mu nan ma k’arasa da k’afafun mu.”

Ina da manufa ta tafad’ar haka.

A hankali motar tayi parking gefen hanya. Na kama murfin motar da sauri zan bude na kasa sai da Shadow ya futo ya bude mana, na futa ina gallah masa harara.

Ido yayi wa Shadow magana naga ya zura kansa ta window motar wani abu ya mik’o masa, yana dagowa naga kud’i daure da kyuare ‘yan dubu-dubu.

Shadow ya mik’o min tare da fad’in”.Gashi oga yace a baki.”

Kud’in na kalla shekeke ina sauri mubar gurin domin nasan halin ‘yan unguwar mu abun magana baya yi musu wahala.

Mimi sarki ‘yan san kudi ta dinga zungurin kafad’a ta wai in karb’a

Tuni zuciya ta tafara min wasiwasi kan wannan uban kud’in da yace a bani,wato yana nufin ya biya ni kud’in iskancin da yayi min kome oho,me yasa bai bawa Mimi ba.

A tunzure na karb’i kud’in kai tsaye gurin shi na nufa, na zura kaina ta window na motar na cire kyauran dake daure da kud’in.

Kallon juna muke ni dashi, fuskarta babu fara’a na fara zuba masa kud’in a jikinsa tare da fad’in.” Wannan kud’in da ka bani basu isa su siye ni ba, baka da abunda zaka yaudare ni dashi, kasani inanan sai nayi maka illah a rayuwar ka tunda ka sake ka shiga rayuwata sai kayi daka sani wallahi.”

Da mugun gudu Shadow ya kawo min duka na kifa kaina cikin motar har ina buge goshina. Da sauri na dago Shadow ya daga hannu zai kwada min mari!!!!!!!

“Shadow!!! “.
Ya fad’a cikin wata irin murya wacce ban san shi da ita ba, muryar dai tafi kama da ta Wanda yake cikin tsantsar b’acin rai.”!

Shadow!! Ya sauke hannunsa yana wani irin huci!! Jikinsa sai tsuma! Yake.

Ni kuma duk na furgice so nake kawai Shadow ya bani hanya in wuce kar wani Wanda muka sani ya futo daga cikin layin mu.”

K’asa-k’asa naji yace.” Shigo mota mu tafi.” Shadow yayi min wani irin kallo me nuna zamu had’e dake ne watarana ya bude mota ya shiga.

Ina Kallon Alina tana kwashe masa kud’in da na baza a jikinsa sai harararmu take.

Tsaki naja na matsa gefe ina taufar da yawu.

Hannun Mimi na kama muka fara tafiya Mimi bina take simi-simi jikinta DUK yayi sanyi da abunda nake aikata wa.

Ajiyar zuciya! kawai yake saukewa zuciyarsa tana masa sak’e-sak’e akan yarinyar tunda yake a rayuwa babu macan da ta tab’a yi masa Abu irin Wanda yarinyar tayi masa.

Sam baya so ya nuna mata hakikanin waye shi baya so ya nuna mata mugunta saboda shi mutum ne me tausayin talaka a duk inda yake ya lura kuma takalawa ne sosai babban abunda ya kashe masa jiki dasu jin abunda d’ayar take fada masa jiya cewar su marayu ne babu uba ya tabbata mahaifiyar su tana fama dasu, amma ya lura sai ya saita yarinyar domin abun nata yayi yawa, yanzu dai tayi na farko tayi na k’arshe kuma sun rabu domin babu ita a rayuwarsa a yanzu amma mutukar ta shigo gonar sa ko Allah zai sake had’a su a wani guri to tabbas zai nuna mata true colour d’insa sai ya gigita mata rayuwa, da wannan tunanin ya cire abunda tayi masa a ransa ya bawa Doh-doh umarnin tafiya.

Cike da tsoro muka lab’e soran wani gida nida Mimi muna shawarar wace irin k’arya zamu girbawa Umammu in muka je gida.

Meye Asalinsu ne?

Asalin su shine………….

Zamu had’u dake a pege nagaba
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

16

Malam Sulaiman mai madara shine mahaifin Asma’u d’an Asalin garin kano unguwar k’oki a ka haife shi, su goma sha shida ne gurin iyayensu maza goma mata shida maihaifinsu da mahaifiyar su duk sun rasu ba dadaewa ba, lokacin ma an haifi Asama’u kasancewar dama ba wani arziki ne dasu ba yasa babu wani gado da suka bar musu ‘yan uwansu mata duk sunyi aure suna gidajan mazajansu suna sana’oinsu da zaman aure to suma haka take a garesu duk suna da aure da yara ko wanne na buge bugen sa na kasuwanci da aiki yanda zai rufawa kansa asiri, kwata-kwata basu da zumumci ga junansu kowa kansa ya sani da ‘yayansa idan ba wani taro ake ba babu me ziyartar d’an uwansa daga matan har mazan duk da cewa ‘yayan mutu d’aya ne kowa harkar gabansa yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button