BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
Gyad’a kansa yake yana d’an cije lips d’insa na k’asa tunda take a rayuwa babu wata ‘ya mace da ta tab’a yi masa irin abunda yarinyar ta yi masa, ta kwance kudi ta watsa masa saboda tsabar bata da mutumci tana tashan balaga, sosai ransa ya b’aci d’azu zuciyar musulunci ne kawai tasa ya k’yaleta lura da yayi bata da wani galihu ko ga yanayin unguwar tasu ma da ya gani kuma yaji daga bakin ‘yar uwarta cewar marayu ne shine kawai ya k’yaleta a d’azu, wannan ya wuce mutukar ta kuskura ta k’ara aikata masa wani Abu makamanci Wanda take masa tabbas zata karb’i hukunci ko ina ne ta ganshi ta nuna tasan shi ta kawo masa shirmen ta to tabbas sai yaga da wanda take tak’am zaiyi mata horo me tsanani wanda zata zo tana kuka da hawayen ta tana bashi hakuri.
Da wannan tunanin ya rufe babin Asma’u a ransa domin baya saka damuwa cikin zuciyar sa ko kankani.
Mik’ewa yayi ya d’ibi wayoyinsa ya futa duka Wanda suke gurin suka mike suna masa a sauka lafiya b’aki kuma da suka shigo company suna so su gaisa dashi babu lokaci kawai ya daga musu hannu ne ya wuce. Bodyguard d’insa na take masa baya.
15/October/2009
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
Whasap numbar
07084653262
08089965176
Account numbar
1013851874
Ahamad gwadabe
UBA BANK
18
Tsakiyar dakin Mimi ta tsaya ta rik’e k’ungunta tana sauke ajiyar zuciya tace.” Wallahi ban zaci abun xai zo mana da sauk’i haka ba. Mik’ewa nayi zaune ina cire hijab din dake jikina nace.” Wallahi nima haka Mimi Allah ne kawai ya taimake mu Yaya Aminu bayan da munga tujara dan sai Yaya Musa ya tambaye shi ko Dan ya kure mu.”
Mimi tasa dariya tana bin jikina da kallo tace.” Wai a ina kika samu wannan muguwar rigar kika saka kinga yanda tayi miki mugun kyau kuwa,tun d’azu nake so in tambaye ki tashin hankalin da muke ciki ya hana. Tab’e bakina nayi nace.’ Ke a ina kike tunanin zan samu kayan gurin wancan guy ne fa, shine ya bani rigata Kin san ta yage.” Mimi tazo ta zauna kusa dani gami da zuba min ido.nace.” wannan kallon fa malama.”
“Asma’u amma dai baiyi miki komai ko.” ? Mik’ewa nayi ina shirin tub’e rigar nace.” Jeki tambaye shi sai ya baki amsa.’ Kallo tabi ni dashi tace.” Wallahi gwara kuwa ki cire rigar tun kafin Umma ta Ankara da ita.” Nace.” Nima dama tunanin da nake kenan.
Mimi ta cigaba da cewa.” Gaskiya Asma’u kinyi nisa da tsaurin ido kamar wannan kikayi wa iskanci gaskiya banji dad’i ba ko banza ya taimake mu tunda ya kaimu gidansa muka kwana kinsan da sai dai mu kwana a hanya Wallahi yanda motoci suke wahala in dare yayi.
Tsaki naja nace.” Don Allah ja can gefe guda,waye ya fada miki irin wannan mazan ana musu da sauk’i, Bari kiji kudinsa ko kyauwunsa wallahi bazai hanani in yaga shi ba, domin nima rigar mutum ci na ya keta min gaban idanun mutane ko Baki ga abunda yayi min bane.”
Mimi ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin .” na gani mana ai kece kika jawo wa kanki saboda kaifin harshen ki, don Allah ki kula Ku sake haduwa mukayi dashi babu ruwanki dashi.”
Shashan kallon na watsa mata nace.” Yo meye dama alak’ata dashi da har kike fatan sake had’u war mu dashi, rigar shi CE dai gata zan sanya cikin Leda in aje DOMIN ta gama min amfani duk inda na ganshi in bashi kayansa.”
“Lallai ma Asma Mimi tafad’a cike da mamakin abunda nace ta cigaba da cewa.” Nima fada kawai nake nasan babu a inda za mu kara ganinsa domin yayi mana nisa dalilin birthday din Alina ne ma yasa muka ganshi amma na Dade da jin sunansa na yawo a gari. Tab’e baki nayi nace.” Mimi ke kika damu dashi da har kika fahimci sunansa na yawo a gari ni kam wanka zanyi ki k’yaleni da zancan guy nan haka.”
Mimi ta kwanta kan katifa tana lumshe idonta tare da tunano sifar Amjad kyawunsa yana burgeta haka kurrum take jin wani abu a zuciyarta a game dashi. Soso da sabulu na d’auka na nufi band’akin mu dake tsakar gida domin inyi Wanka, ina jawo ruwa cikin rijiya Aunty Hauwa tayi sallama ta shigo hannuta rike da yarinyar ta Islam daya hannun kuma wata katuwar Leda ce ta shigo da kallonta nayi naga tana cikin farin ciki. Gefan tabarma ta zauna kusa da Umma wacce take d’aurin gishiri,suka fara gaisawa nace.” Aunty Hauwa wai ke don Allah bakya gajiya da tafiya ne, sai kace ma’aikaciya yau in baki zo ba gobe sai kin zo hana don Allah.”!!! A harzuk’e tace.” Wallahi zan zo in ci ubanki Anan gurin ni sa’ar ki ce na shigo gida babu sannu bare gaisuwa kin zo kina min shirmen banza da wofi.” Dariya nayi nace.”Allah ya baki hakuri bari nayi Wanka sai inzo mu gaisa a tsanake .” k’wafa tayi kawai ta juwa suka cigaba da magana da Umma wacce take cewa.” Kece kika biye mata ma Asma’u Wanda be San halinta ba sai ta sashi hawan jini.” Aunty Hauwa tace.” K’yaleni da ita Umma wallahi ta jawo wa kanta bazan bata mayafin ba Mimi ce zata dauki daya kema ki d’auka nima na d’auka ita ko ta jawowa kanta tunda tana ganin Neman kud’in da nake yawo ne, ko mijina be hanani ba sai ita me bakin magana.”
Cike da farin ciki Umma ta jawo ledar tana zazzage kayan ciki. Mayafai ne da dogayan riguna sabbin shigowa sunyi bala’in haduwa sai walwali suke ko ina stones a jiki anyi musu ado wasu shipom wasu kashka ne masu taushi.
Umma tace.” Wannan mayafan sabibin zuwa ne da alama.”?
“Wallahi kuwa Umma yanzu daga kasuwa nake naje d’aya daga cikin kantinan Mudansir And brothrs kawai naga suna sauke kaya, kasancewar mun saba dasu saboda INA zuwa sari yasa suka bani kaya akan yanda suka sauke Wallahi naji d’adi yanzu zan cire abunda yayi saura a account dina in basu in yaso in nagama had’a kud’in sai in cika musu sauran.” Umma tace.” Aikuwa haka yayi wallahi kice yanzu zamu fara kasuwan ci da karfin gwiwa ko.” Cike da farin ciki Aunty Hauwa tace.” K’warai kuwa Umma ai naji dadin abunda sukayi min wallahi. Kinga ko bani da ko kwabo zasu bani kaya in juya in kawo musu kud’in.” Umma tace.” Allah yayi musu albarka ubangiji Allah ya daukaka Mudansir a duk inda yake.” Aunty Hauwa tace.” Ameen ya rabbi ammafa Umma bashi kadai zamuyi wa addu’a ba.” Umma tace.” Auwo!! Dawa kuma.”? Dariya tayi tace.” Akwai mutumin da naji suna zancan sa wai sunanshi Amjad ya bude sabon company a wajan gidan governor can wajan magwan, ya zuba ma’aikata sosai fararan fata da bakake fata, can suka samo kaya masu kyau da arha suna ta murna sun huta futa Dubai da sauran kasashe kawo kaya,DOMIN kayan da company suke har yafi na wata wata kasar wajen ma kyau da karko.”
Umma tace.” Kai wannan kuwa Allah yayi masa albarka wallahi yanzu ‘yan kasuwa zasu fara walwala da NISHAD’I.”
Aunty Hauwa tace.” Wallahi nima haka nace sunan company Amjadu Abul Abbas Matireals.”! dai-dai lokacin da aunty hauwa take fad’ar wannan ni kuma lokacin na futa daga ban daki kenan , abun sabulun dake hannuna ya kusa fad’uwa nayi saurin rike shi gabana na fad’uwa jin sunan da aunty Hauwa take fada……….kallon bakin ta kawai nake lokacin da take zayyanowa Umma mutumci da karamcin Amjadu me company sai da naji tana cewa kuma ance yaro ne karami ko matar aure bashi dashi nan na kara tabbatar wa da cewar guy nan ne domin dai ni tunda nake ban tab’a jin suna irin nasa ba Amjadu Hararata aunty Hauwa take nazo na wuce ina kunshe dariya don nasan abunda nayi mata d’azu take wa, nace.” Bari inzo in karb’i nawa mayafin.” Ko kallona ba tayi ba ta cigaba da maganar ta. Mimi na samu kwance har yanzu idanunta a lumshe. Nace.”Mimi ki tashi ga aunt can tazo ta kawo mana mayafai.” A hankali ta bude idonta na kalle ta cike da mamaki nace.” Badai bacci zakiyi ba.”? Tace.” Wallahi shi zanyi jiya fa banyi wani baccin kirki ba.”