BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Suna zaune sun fi su talatin masu babbar riga da masu cout masu suit da masu jampa sai zare ido suke hakan ya tabbatar masa da cewar shi kadai suke jira ganin lokacin da ya shigo suna gyara zama masu hararsa nayi da masu yi masa tsaki.

Kafin ya zauna sai da ya gaishe su jam’i kasancewar shine me k’ananun shekaru a cikinsu wasu suka amsa wasu suka yi masa shiru, cike da jarumta ya mik’a wa me girma governor hannu suka gaisa a muntuce sannan aka bude taro da addu’a.

Shugaba taro ya mike ya fara fadin “Dalilin da ya tarasu anan domin a zauna a samu maslaha da fahimtar juna a matsayin su na ‘yan kasuwa da suke kawowa kasa cigaba saboda haka an bawa kowa dama ya tashi ya fad’i ra’ayin sa a kan abunda yake faruwa.

Dukaninsu kusan bakinsu yazo daya na cewar Amjadu yana so ya rusa su ya dakatar musu da harkokin kasuwancinsu bayan bude company da yayi ya sauke farashin kaya sunyi kasa kuma yana da ma’aikata sosai suna tsaye a company ko suna kawo cigaba kayayyakin da suke yi wane na kasar waje da wata Dubai ma saboda haka bakinsu ya had’u gurin cewar gomnati ta rusa wannan company domin yana dak’ile harkokin kasuwanci su.”

Yana hakimce cikin kujera yana kallon bakin kowa Alhaji Hashimu me citta shi yafi kowa zak’ewa a gurin Akwai Alhaji Sunasi me leshi mutum da ko sati ba’ayi ba yaje masa da maganar cewa yana so su hada hannu dashi, domin faranta ran talaka da k’ananun ‘yan kasuwa Ashe duk k’arya ne lallai dam Adam mugun ice ne gashi harda shi cikin masu hada masa taro.

Bayan me girma governor duk ya gama jin k’orafe-k’orafen su sai ya kalli Amjad cikin nutsuwa yace.” Young millionaire kaji abunda suka fada, wannan metting din muna yin sa ne domin Samar da zaman lafiya gami da maslaha ga gomnati da kuma Ku ‘yan kasuwa.

Cikin nutsuwa ya dago kansa yana kallon me girma governor yace.” Ranka ya Dade duk naji abunda suke k’orafi akai, farko dai ina so su gaya min cikin su wa na tab’a shigarwa harka ko kuma na tab’a zuwa ran can kudi gurunshi, bayan nan kud’in waye company nin waye? Ko yau nace a daina futar da kaya da zumar siyarwa a daina karb’ar kud’in duk Wanda ya shigo sari a bashi kyauta ko dila nawa yake so ina ganin babu damuwar kowa a cikinsu tunda babu kwabon kowa a ciki so ina ganin wannan taron da aka hada shi an hada sh domin a bata maka lokaci Yallab’ai kai da kake aiki a gabanka.”Ya k’arashe maganar sa yana zakud’a kafad’a kamar ba a gaban governor yake ba. Zufa ce kawai take karyo wa daga jikinsu dukaninsu sunyi mutukar mamakin jin abunda ya futo daga bakin k’aramin yaro Wanda wasu daga cikinsu ma sun haife shi, wani dattijo me suna Alhaji d’an Akushi ya mik’e tsaye a zafafe! Ya daki tebur ya kalli Ajamd tare da nuna shi da ya tsa yace.” Baka isa ba Wallahi domin tunda ka bude wannan company naka shikkenan kasuwancinmu ya rushe ko mun futa waje mun d’auko kaya to babu wani k’aramin Dan kasuwa da zai zo ya Sara sai dai ya barmu da abun mu saboda haka baka isa ba, muna kiranka da babbar murya ka je ka rushe wancan mutsiyacin company naka domin tun baka San kanka ba muka san meye kasuwanci babu abunda zaka nuna mana.” Alhaji Dan Akushi ya kare maganar sa kumfa na futa daga bakinsa .

Me girma governor ya kalli Amjad yace.” Kaji kan maganar Young suna tuhumar ka da dakushe musu harkar kasuwancin su, da kayi wannan shine maganar maslaha muke nema.”

Amjad ya dago ransa ya soma b’aci ya kalli governor ido da ido yace.” Yallab’ai INA ce kaji abunda nace ko ina nan kan bakana gurin ganin na taimakawa na kasa dani.”

Cike da b’acin rai Alhaji Hashimu me citta ya mike tsaye baki na kumfa yace.” To kuwa ka kwana da sanin zamu sa a kone company domin bashi da wani amfani a gurin mu.” Wani malalacin kallo yake masa yana miskilin murmushi cike da son cusa haushi yace.” So what don kunsa an kone company Amjadu Abul Abbas nasan dai ni baku Isa Ku kona ni ba, kuma ko yau Ku ka kone company na to ina me tabbatar mu da cewar ko kwana baza’ayi ba zan fara aikin bude wani sanin kanku ne ni kudi ba matsalata bace.”

Sai ince kusan a tare suka mike suna caccakar sa gami da nunashi da Dan ya tsa har da masu son su tsune masa ido zaginsa kawai suke gami fa cin alwashi a kansa.
Governor da yaga abun yana so ya shige gona da iri sai ya tsawatar amma duk da waha wasu basu bari ba sai da suka gama fad’ar abunda yake bakinsu sannan suka koma suka zauna suna huci!! Yana zaune yana kallonsu fuskarsa d’auke da kwantaccan murmushi, da alama abunda sukayi din bai dame shi ba, shiyasa dukaninsu yake musu kallon mahaukata wadanda basu San me suke ba kuma masu son Kansu da iyalinsu. Hakan da yayi musu ya mutukar tun zura zucuyarsu sun so ya tanka musu su ci masa mutum ci sosai sai yayi aiki da iliminsa ya kyalesu a matsayinsa na me k’ananun shekaru akan su sai ya dauki girman kawai, shi kanshi governor yasan shi yake da gaskiya, tun farko da suka kai masa maganar to amma don kar suce ya goyi bayansa yasa ya amunce da zuwa taron gashi sun zo suna hauka.
Yace.”Young ina ganin abu d’aya zamuyi Wanda zai kawo maslaha a tsakaninmu.” Duk sukayi shiru suna sauraron sa me girma governor ya cigaba da cewa.” Zaka k’ara farashin kayanka akan yanda ka sauke a da sukayi raga-raga Wanda hakan yasa sauran ‘yan kasuwa kasuwar su ta tsaya saboda duk wani me Neman sauk’i sai ya gudu company ka domin ya d’auko kaya ina Neman wannan alfarmar a gurin ka ka d’aga ‘yan ?uwanka kafa suma su samu nasu kason.” A lalace Amjad yake kallon me girma governor ranshi in yayi dubu ya b’aci a matsayinsa na shugaban aluma talaka da me kudi har wani da bashi da mukami a gomnati ya iya sadaukar da kudunshi duk dan a kan talaka yaji dad’i amma shi yana maganar ya tsawwala farashin kayansa domun a kuntatawa talaka abunda bazai yi wu bane. Da karsashi yace.” Yallab’ai wannan magana da kake fada Sam baza ta samu ba ka sanja wata domin ni nan daka ganni dukiya ta ta talakawa ce so ina ganin babu Wanda zai nuna min ga yanda zanyi da ita.” Sosai sukayi mamakin abunda ya fadawa governor shi kansa yayi mamaki lallai yaron yana da tsaurin ido a matsayinsa na shugaba yace ga abunda za’ayi amma yace bazai yi ba ran governor ya mutukar b’aci sosai da sosai. Alhaji Hashimu me citta yace.” Ranka ya Dade kaga kaima ya nuna maka halinsa ko ai da ni na tun yau ba nasan yaron nan DOMIN tun ubanshi na yawon haya da bin kasuwanni karb’o kaya nasan bashi da mutumci ubanshi Abbas mugun Dan taurin bashi ne a wancan lokacin kafin 6a mutu da k’yar na samu ya biya ni kud’ina duk da haka da wasu a kansa ya tafi kuma baya fe masa zanyi ba, Alhaji Sunasi me leshi yace.” Gashi ya mutu ya bar baya da kura zakuwa mu dauki mataki.” Kafin ya k’arasa Amjad ya mike tsaye a zafafe! Ya daki k’aton tebur din dake tsakiyar su robobin ruwa da Lemo suka dinga tsalle suna fadowa kasa, muryarsa a sama! Alhaji Hashime kake kome ? To ka kiyaye ni wallahi bani da kyau, na fuskanci kai baka san ka girma ba idan baka sani ba ina so in sanar da Kai ku in kara tuna maka kana magana ne da Amjadu d’an Asali Amjadu Dan Abul Abbas ko a wannacan lokacin da muka gwabza da kai ba samu riba ballanta na yanzu saboda haka ina kasanar daku dukkaninku Ku rike girmanku kar Wanda ya shigo gonata zamu sanya k’afar wando guda dashi.!!! Yana gama maganar shi ya d’ibi wayoyinsa ya fuce, da zafin zuciya tafiyar da yake tamkar zai dasa tayal din gurin.
Tsit!!!!!! Gurin yayi kowa yana mamaki abunda Amjadu ya aikata tabbas yaron ya cika tak’adiri kuma mara tsoro. Me girma governor ya sauke ajiyar zuciya ransa a bace yace.” Yaron nan bashi da kunya ko kad’an kuma dole gomnati ta dauki mataki a kansa za mu nuna masa mulki da izzarsa zai da k’arfin mulki zamu nuna masa shi ba kowa bane tun fmda har yak’i ya bamu hadin kai mun zauna domin a samu sulotion mu samu mafita ya karya doka ya nuna ma bashi da lokacin mu to duk Ku kwantar da hankalin Ku zaku ga abunda gomnati zata aiwatar akansa.” Dukaninsu fara mik’a godiyarsu ga governor, ya rufe taro da addu’a kowa ya watse zuciyoyi babu dad’i!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button