BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Yana kwance ya bayan mota da karan sigari a hannunsa ya kusa shanye kwali guda kana kallonsa kasan ransa ya bace yake saboda yadda jijiyar kansa tayi rad’ad’a busa sigari kawai yake yana shawarwari a zuciyarsa ta yanda zai bulluwa magautansa, Ciki da ladabi Doh-doh yace.” Sir ina muka nufa.”? Shuru yayi masa sai da ya kara maimaitawa sannan yace.” Gyad’igyad’i gidan Granny”. Rambow yace” Sir yau ka tuna da ita kenan.”? Shiru yayi masa kawai ya lumshe idonsa.
Suna shiga get din gidan masu gadi gami da masu aiki suka dinga zuwa suna kawo gaisuwarsu ya futo daga mota a tsanake ya na amsa musu ya wuce ciki gidan cikin kakkarfan takunsa.
Wata lafiyayyir dattijuwa na gani zaune a wani kayattacan falo da ya gaji da haduwa komai na more rayuwa akwai kwata-kwata farlon baiyi kama dana tsohuwa ba tana zaune cikin kujera me cin mutum guda sanye take da Riga da zani na atamfa ammata dinki irin na tsoffafi idanunta sakaye da farin glashi na kara k’arfin gani carbi na gani a hannunta tana ja ta zubawa tv ido tana kallon tashar sunnah tv malam jafar mahamud Adam na tambihi Allah ya jaddada rahama a gareka malam
Granny kenan kakar Amjad ta gurin ubah sunanta na asali Saratu bafulatana ce usul duk da ta tsufa amma har yanzu da hasken ta tamkar tsada k’afar nan kamar ka matsa jini yayi sartuwa, sai ince muku duk kamaninta Amjad ya kwaso sosai suke da kyau kamar ka sace ka gudu.
Tana zaune ta dinga n k’amshin turaransa da sauri ta kalli kofar shigowa aikuwa shi ta gani sunkuye yana k’okarin cire takalman sa, d’auke kanta tayi da sauri ta dauki goranta ta b’antara k’asa-k’asa tace.” Bazan kula ka nima tunda sai ka ga dama zaka zo gareni kallonta ta cigaba da yi kamar bata San ya shigo farlo ba, abun mamaki sai taga ya nufi inda wasu tangama-tangama hutuna suke jingine yana zuwa gurin ya tsunguna tare da sanya hannunsa yana shafa jikin hotan, gabanta ya fad’i tace.” Yau a n tab’o zuciyarsa kenan.” Mik’ewa tayi ta biyo bayansa shi kuma ya rungume hotonan a k’irjinsa yana kukan zuciya wasu zafafan hawaye suka biyo kucinsa. Granny ta dafa kafadarta muryarta a tausashe tace.” Tashi muje ka fada min wanene ya tab’oka dama tunda na ganka nasan akwai dalili ka aje hotan an Wanda ya mutu ya Riga ya mutu addu’a ce kawai tsakanin mu dasu.” Da k’yar granny ta shawo kansa ya aje hoton a inda ya mike ta kama hannunsa suka bar gurin ni kuma da sauri na kalli hoton wasu mutane nagani mace da namiji jikin hotan da alama mata da miji ne namiji yana tsananin kama da granny macan kuwa kana ganinta kaga a salin bahaushiya domin bak’a ce amma kuma me kyau hanci har baka. Tausayi Amjad ya bani sosai ganin yana tsiyayar da hawaye da alama yana da alak’a da mutanan dake jikin hotan. Farlo na bisu domin jiyo muku me suke tattaunawa.
Wanene Amjadu?
Zamu had’u daku a pege na gaba.
18/October/2009
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
21
Abul Abbas mutumin Chadi ne inda nema ya kawo shi garin Kano bayan rasuwar mahaifinsa sai ya d’auko mahaifiyar sa, Saratu sukayi kaura daga mahaifarsu suka dawo Kano gaba d’aya. Suka bar ‘yan uwansu da abokanan arziki a can sai dai suna zuwa duk shekara su duba su, tunda Abbas ya dura a garin na Kano bai zauna ba duk wata kasuwa da ta shahara a garin yana shigarta ya nemi kudi a cikinta yayi Hulda da mutane sosai da sosai hakanan kuma ya karb’i kayayyakin mutane ya juya har Allah ya sa ya samu nasa jarin inda ya kafa tebur a bakin titi kafin kashiga ai nihin kasuwar. Babu laifi yana samun kudi sosai saboda duk Wanda ya kwana ya tashi cikin garin Kano ya San da zaman kasuwar k’wari yara da manya kasuwa CE me albarka da d’umbun tarihi cikin ikon Allah ya siyi gida maidaidaci can rijiyar zaki sai suka tashi daga hayar da ya kama musu. Nan mahaifiyar sa ta matsanta masa da dole yayi aure, lokacin Neman kudinsa ne kawai a gabansa yace kawai ta nema masa mata,aikuwa batayi sanya ba ta nema masa Aishatu ‘yar kusa da d’akinta dake gidan da suke hayar basu kadai bane, Aisha yarinya kntsatsaya me hankali gami da ilimin addini, nan take iyayenta suka yadda, to shima Abbas da mahaifiyar sa ta fada masa bai musa ba domin dama yana yaba kamala da nutsuwar yarinyar, lokaci guda aka sanya rana Abbas ya hada lefe abunka da Dan kasuwa komai yayi na bajinta lokacin buki yayi akayi cikin aminci da yardar juna amarya ta tare gidan mijinta dake rijiyar zaki. Daki da rumfa manya sai k’aton tsakar gida,dakin Inna na gefe guda can wajan kofar futa.rayuwa suke ta fahimtar juna dake Inna bata da sa’ ido kan suruki shiyasa suke zaune lafiya cikin ikon Allah Aisha ta samu ciki, to tundga samuwar cikin nan arziki yayi musu sallama Abbas ya bude k’aton shago can cikin kasuwa ya fara harkokinsa da manyan yan kasuwa, makotansa na kasuwa cikinsu akwai Alhaji Hashimu mai citta sai Alhaji d’an Akushi, sai suka Dora masa ido sosai da sosai kyashi gami da haddasa duk suka dame su gashi dai suma suna ciniki suna samun rabonsu amma sun d’ora ido kan abunda Abbas yake samu a cewar su shi na Dan gari ba yazo yana cin albarkar gari.nan suka farayi yi masa bita da k’ulli,hakan da suke sai ya zame masa alkairi domin kofofin samun sa ne suka kara budewa, Dama Annabi ya fada cewa a yayin da kake wa mutum hassada to a lokacin Ubangiji zai cigaba da d’aga shi a duniya idan kun faya kun ta sauka a kan bawa to babu wani mahalukin da ya Isa yace ba haka ba Allah ta tsare mu da ciwon hassada domin babban bala’ine
Lokacin da Aisha ta haifi Amjadu sai da talakawa sukayi farin ciki dama lokacin cikin azimi ne dab da sallah Abbas ya sauke farashin kaya ko na ko wane shagunan shi a lokacin sun kai bakwai cikin kasuwar k’wari uku na takalma ne uku na kayan sawa daya na mayafai ne, haka ya dinga bonanza mutane suka dinga zuwa suna siyarwa iyalinsu kaya DOMIN suyi bukin sallah, sosai WANNAN abu da Abbas yayi ya dugun zuma rayukan ‘yan kasuwa bari ma su Alhaji. Hashimu take suka fara shirya masa sharri Wanda suke so ya tattara ya bar k’asar gaba daya ya koma tasu k’asar.
Amjad yaro kyakyawa bafulatani usual tun yana yaro yake da miskilanci gami da rashin son magana, kakar shi tayi ta tsokanar shi da suna k’ato uban ‘yan muskilanci lokacin yayi ta jin haushinta ko d’akinta baya shiga ita kuwa ba ta fasa kiransa da k’ato uban ‘yan musklaci dake Amjad irin masu GAF!GAF din jiki ne yayi mutukar saurin girma sosai shekararsa shida sai kace shekara goma saboda girma ga Abu yanayi irin na manya a lokacin Alhaji Abbas ya gina gida k’aton gaske cikin Jambulo suka koma da iyalinsa lokacin arzkinsa ya kai ya kawo duk sati biyu suka zuwa umara shi da iyalinsa aikin hajji kuwa baya wuce su KUMA duk shekara yana d’iban mutane goma cikin ‘yan uwa da abokan arziki ya biya musu su sauke farali. Amjad tun yana yaro yake da zuciya kwata-kwata ba ayi masa Abu ya k’yale sai ya rama babu ruwan shi da shiga sabgar da bata shi ba, in ya ga dama ko Maman shi baya yiwa magana sai ya ga dama hakama a skull ba kowa yake kulawa ba Sam bai yarda da abokai ba, yawanci ma abokan shi mata ne Wanda sune suke nace masa gami da zuwa inda yake wai ya duba musu jarrabawa dake akwai brain sosai nan zai karb’a ya nuna musu inda basu gane ba.