BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL


Alhaji Hashimu me citta sai da ya san yadda yayi ya jone harkar kasuwanci sa dana Alhaji Abbas domin ya cimma wata manufa tashi, Sam Alhaji Abbas be san da wani kudiri a zuciyar mai citta ba kacokan ya mik’a masa yardarsa tare da amuncewar sa suka cigaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci, kamar babu wani k’ulli a zuciyar me citta.

Amjad na kammala scondry skull ya wuce London ya fara karatu kan harkokin kasuwanci ra’ayin sa ne haka kuma ra’ayin mahaifinsa yana mutukar so yaga ya gaji mahaifinsa kan sanar shi to shima Alhaji Abbas din nashi b’angaran haka yake. Lokacin Amjadu na da shekara ashirin da hudu inda yayi wani irin girma tsayi da fadin k’irji gami da kuzari sai kace wani Dan shekara talatin tunda ya fara zama saurayi yake da akidar turawa dakin shi duk dics din mawak’a ne na kallo dana ji ko da yaushe kunnen shi mak’ale da airphone yana jin music Amjad yana sauraren wak’okin tsohowan mawak’in nan bom marly da macaal Jackson 2pac Sisqo Joy BIG da sauransu. Cikin mawak’a mata kuma yana sauraron wakokin Cilen dion Janeepar Burandi Tony da dai sauransu, gashi dai bai zo a zamaninsu ba amma yana bala’in son wakokinsu Dan bai fiye sauraran mawakan na lokacin ba, gwara Usha da wzky yana sauraron nasu, kallon Hausa ko jin wakokin Hausa Sam bai dame shi ba, gashi dai yana jahar Kano dandalin Hausa da film din Hausa a cewar sa duk shirme suke da shashanci don in yaga Adam A zango yana Abu na nigogi Dari kwai yake masa ya wuce abun yana bashi mamaki in yaga yadda matasa suke kwaikwayonsa.

Duk sutturun shi babu namu na Hausa duka kananu ne ga wani uban gashi da yake tarawa a kanshi kunsan dai yadda bafulatanin mutum yake da kyawun gashi gami da baki to haka ma na Amjad yake saboda tsabar gyara da yake sha gami da mayuka masu tsada har wani tattatewa yake askin shi abun kallo ne har inda ya futa ba tare da mota ba ‘yan mata susucewa suke yi sai su dinga ganin kamar d’an India Wato Allu arjun DOMIN suna mutukar kama dashi, shiyasa yake wayan shiga mota ko da ko tafiyar da zaiyi ba me nisa bace , gudun kallon matan Kano Wanda yake ganin hakan tsabar k’auyanci ne da gidadanci sai kaga mace har mace ta tsaya tana kallonsa wasu ma yana cikin mota suna mota zasu dinga zuro kai suna lek’ensa tsaki kurum yake ya d’auke kansa
Maman shi me damuwa da yanayin shigar shi tayi tai masa fada watarana in taga ya sanya siririyar sark’a a wuyansa turke shi take tace dole sai ya cire domin bazai futa da ita ba, ita ko granny dake haka ya ke kiranta tace masa bata son wannan sunan domin na arna ne yak’i ya daina saboda ya lura bata so duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taki amsawa sai ya kirata da Innah sannan zata amsa. Cewa take ki kyaleshi dai ya cigaba da irinn wannan shigar Cikin kano sai ya rasa matar aure domin ‘yan Matan kano idan ba jampa da kufta kayi musu ado dashi ba babu me auran ka nu kuma ka dawo gare ni in ce a kai kasuwa. Dariya yake duk lokacin da tayi wannan maganar sai yace.” Ke an fada miki ni zan auri ‘yar kano gidadawa dasu Wanda babu abunda suka iya sai kallo da ihu! Ga Adam A zango ga Ali nuhu dama me suka sani in banda bleccing.” Granny tace.” Ranar da bakanuwa zata rike maka wuya yanan zuwa” tsaki kurum yake ya barta a gurin. Ganin ya tsaida sallolinsa biyar yasa Alhaji Abbas baya ta kura masa kan abunda yake yi domin sallahr Asubah bata wuce Amjad yana riga kowa tashi a gidan to itama Hajiya Aisha sai ta kwantar da hankalin ta.

Ko da yaje London sai Abu ya kara k’aimi saboda haduwa da yayi da turawa masu irin ra’ayin shi harda bakaken fata ma “ya gari daban-daban, sai ya saje dasu kawai ya koma tamkar wani bature har ta kai ta kawo yana zuwa barbing saloon Wanda ya amsa sunansa ya zube kudi masu kyau! Ayi masa kitso Wanda muke kira zane manya ake masa guda shida ko biyar, ya futo abunsa babu Wanda zai kalleshi tace. Mahaifitarsa bakar fata ce KUMA ya hada jib’i da Hausa Fulani saboda yadda ya saje ya koma tamkar d’an sarauniyar Ingila.
Shekararsa biyu a can, wata rana Dady dinshi yayi masa waya cewar zasu je Chadi ziyara, yaji ina ma yananan aje dashi yayi musu fatan dawo wa lafiya tare da cewa a mik’a masa gaisuwa gurin ‘yan uwa, aikuwa haka a kayi suka shirya tsaf suka bi jirgi 1:00 pm tare da guzurinsu ga ‘yan uwa Innah sai murna take da farin ciki zata ga ‘yan uwanta, daf da zasu sauka daga jirgi Allah ya saukar da al’amarinsa i n jirgi daga sama ya samu tangard’a nan take ma’aikatan hankalinsu ya tashi suka fara kai kawao drabobin jirgin suka gigice domin son su shawo kan matsalar inahh! Duk abunda Allah ya hukunta zai faru sai ya faru duk k’okarin su na son su sauka kasa Allah bai nufa ba daga sama jirgin ya tawo a gicceye a sauka cikin wani daji take ya fara hayak’i kafin kace kwabo ya fara wuta jika Tass tass mutane suka fara k’okarin ceton ransu kofa ta rufe ga shi wuta ce kawai take ci mutane Abu a cikin daji nan take Alhaji Abbas ya turo mahaifiyar sa ta fado kasa can gefe kanta ya bugu da bishiya suna yunk’urin futowa jirgin yayi bundiga inda wuta ta tashi gaba dayansa cikinsu babu Wanda yayi rai sai Wanda suka futo daga ciki suma duk da haka sun kone gami da daddaujewa ga abu a daji.

Hayakin da gurin yake ne yasa hankalin jama’ar gari tashi domin hayak’i har cikin dakunansu nan take kowa ya furfuto masu tsaron lafiyar mutane suka fuskamci daga inda hayakin yake suka nufi gurin cikin shiri

Tashin hankalin da suka gani ya dimauta su jama’ar gari sai kuka suke duk Wanda yake cikin jirgin na n ya kone kurmusu DOMIN wasu har sun zama gawayi saboda konewa take ma’akata suka fara aikin gaggawa.

Wa’yanda suka rayu aka wuce da hospital domin a dubasu sukuwa Wanda suka mutu nan aka tattarasu guri guda tare yayyafa musu ruwa aka sallace su kana aka haka rami aka bune su duka.

Sai dai muce Allah ya jikan muslmai

Wannan al’amari da ya faru ya zagawa ko wace kasa a fadin duniyar nan domun ‘yan jarida ma daga kasashen waje sai da suka zo d’aukar rahoto inda abun ya faru. Suka je Hospital suka hira da Wanda suka rayu a ciki, kuwa harda Innah Wanda akayi hira da ita tana kuka ta fad’i duk yanda Abu ya faru tare da addu’a ga danta da matarsa kuka sosai take tana kiran Amjadu
Yana can yana ta kiran wayoyin iyayen nasa a kashe tuni jikinsa ya bashi akwai matsala domin a ranar kwana yayi yana mugayyan mafarkai akansu, suna tare da abokanshi Rafiq da Irfan Larabawa ne karatu ya hadasu sai wani bature Dan America me suna Sony kallo suke ana american film amma na nigas kwata-kwata Amjad baya jin dadin kallon yayi shiru kawai Linda ta shigo tana sanye da dogon wando tare da Riga me madauri a baya bayanta da cibiyarta duk a waje. Da turanci tace . Su kamo tashar larabai suka abun tausayi jirgi ya fad’i a Chadi gaban shi ya fad’i ya fuzge romt din a hannun Irfan ya fara k’okarin kama tasha, idonsa ne ya sauka kan Granny zaune a gadon asibiti kanta nan nade da bandeji sai kuka take tana kiran sunansa. Su Irfan hankalin su ya tashi ganin yanda ya mike tsaye a zabure yake fadin .” innallahi wainnalihi raji’un.” Suka mike suma , tare da kurawa TV ido ga gawawwaki nan ana bunne su ga jirgi a kone. Zubewa yayi kan kujera yana zubar da hawaye tare da cewa Allah ya jikanku Iyayena duk cikin turanci yake maganar Linda tq zube a gabansa tana kuka tana k’okarin rungume shi, tana bashi hakuri to suma su Tariq zama sukayi suna rarrashin sa tare da bashi hakuri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button