BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
Muka gaisa da ita Sosai tare da fada mata sak’on Umma tace.” Tana amsawa tare da cewa “ai duk laifin Ku ne da bakwa zuwa akai akai sai Ku d’ebo wattani ba kuzo ba ke Mimi haka dangi zasu yi ta cigiyar ki.” Mimi ta sunkyar da kanta cike da kunya nace.” Mamansa Munnu Kawu Ba yanan ne.” Tace.” Bai jima da futa wallahi” nace Munnu fa.” Tace” yanzu ta shiga ban daki tana Wanka ” muka mike muka shiga dakin Munnu kan katifar ta muka zube ni da Mimi Munnu ta baza hotona kan katifarta tana kallo duk irin tsaffin hotanan ne na makaranta da wasu lokacin muna yara. Wani hoto Mimi ta mik’o min tace.” Asma’u kin ganki a nan”? Karb’a nayi ina dubawa Mimi tq fashe da dariya, da sauri na yi yunk’urin yaga hoton cike da takaici hoton anyi mana shine farko fara zuwa makarantar mu lokacin muna kwailaye muna sanye da sabbi unporm ko wanne da k’atuwar jakarsa sai murna muke mun shiga secondary skull Mimi ta fuzge hoton tana dariya tare da fadin” kin San Allah Asma kina kama da ‘yar film din nan Nafisa Abdullahi” hararata nayi nace.” Kin cuce ni Mimi”. Tace. OK kina nufin kin fi Nafisa kyau kenan.”? Nace” nesa ba kusa ba wallahi . Mimi tace “bari Munnu ta futo ta fada miki gaskiya.” Aikuwa sai ga Munnu ta shigo dakin tana goge kanta da k’aramin towol tace.” Ku kuma ‘yan iska yaushe kuka zo” nace.” Babynaaaaaa!!! Cike da tsoka na fad’i maganar Munnu ta kawo min duka tana warce hoton dake hannuna dariya na fashe da ita ina nuna ta da hannu. Ita ko Mimi dake mayyar dariya ce kwanciya tayi kan katifa tana sheka dariyarta. Munnu ta wuce mu cike da takaici take fadin “banza ye kawai wad’anda basa manta Abu.” Ina dariya nace.” Ya za’ayi mu manta Munnu ta Shamsu kenan baki da aiki sai kallon hoton Shamsu ki ishi mutane a skull da Baby na yayi kaza babyna yace zai siya min kaza hummmm! Shamsu ya San takan sace zuciyar ‘yan mata gashi ya sace taki ya gudu ya barki da ciwon sonsa”
Mimi tace” wallahi kuwa kin San ko a skul aka zagi Shamsu sau kunyi fada da ita ko ta d’aura gaba dakai, ummm! Ni kaina sau nawa Munnu tana gaba dani duk akan ina mata magana ta rabu da Shamsu Dan yaudara ne.” Nace.” Nifa WALLAHI duk son da nakewa Namiji bai Isa na nuna masa ba sai dai ya gani a aikace.” Munnu tace.” Ni Ku k’yaleni don Allah kuyi min addu’a kawai Allah ya cire min son Shamsu daga zuciyata” nace.” Munnu kina so ki rabu da soyayyar Shamsu a zuciyar ki amma kike kallon hotan sa.” Shiru tamin nace.” Kinga to” juyowa tayi tana kallona na daga hoton Shamsu dake hannuna na zaga shi gida uku na watsar nace” wannan shi yafi dacewa dake amma kullum kina kallon hoton sa ta Yaya zaki mance dashi.” Mimi tace kinyi min dai-dai da kika yaga wallahi” Munnu ta juya ba tare da tace mana komai ba ta cigaba da kintsa jikinta mu kuma muka cigaba da caccakar Shamsu gami da tsine masa sabo yaudarar da yayiwa Munnu wacce ta saki jiki dashi sosai ya gudu ya barta.Bayan ta gama shirya ta juyo tana fuskantar mu tare da fadin ” INA kukaje ne kula biyo tanan domin nasan dai ba takanas kuka zo nan ba” Mimi tace” aikuwa kin fad’i ba dai-dai ba takanas muka zo nan domin mu wuni amma za muje gidansu Hafsa me warin Ham!! Munnu ta fashe da dariya tana nuna Asma’u dariya muka kwashe da ita dukan mu sai kace wasu tab’abb’u.
B’angaran Hibbah kuwa tana zaune har wajan goma na dare tana jiran dawowar Amjadu shiru bai dawo ba kamar ta fasa kuka haka take ji gashi bata da numbar sa ga wata sha’awrsa na damunta tunda ya d’and’ana mata zumarsa a baki shikkenan taji tana son kara kasan cewa dashi, jiki babu k’wari ta futo daga dakin tana sakkowa kasa taga haske tar mutane sai kai kawo suke tamkar rana domin wasu ma a lokacin suke shigowa gurin cikin motocinsu wasu da ‘yan matansu wasu da abokan su gasu nan dai. Duk tarin mazan da suke Binta da kallon sha’awa Sam basa gabanta domin yanzu ita babu Wanda take gani a gabanta sai Sadauki Amjadu shi kadai ne burin ta. Motar ta bude ta shiga ta futa daga hotal din.
Bayan munci abunci munyi sallah azuhur ne sannan muka sake kintse jikinmu domin zuwa gudansu Hafsa muka futo mu ka sanarwa da Mamasu Munnu tace” to daga can zaku wuce kenan.”? Nace “Eh daga can zamu wuce gida” d’akinta ta shiga tana fadin “Bari in zo to” mu kowa ni da Mimi hanyar futa muka nufa saboda mun San halinta kullum in muka zo sai tace zata bamu kudi.” Aikuwa sai gata ta futo hannunta da gudar Dari biyar tare da wata Leda me Zane Zane. Ta mik’o mana tana fadin Ku karb’a Ku kara kud’in mota” nokewa mukayi cike da kunya Mimi ta karb’i ledar tana fad’in “zamu karb’i wannan amma ki bar kud’in naki” Munnu ta karb’i kud’in tana fadin” Umma kyalesu suna so wallahi munafurci ne” kawai na basu in mun futa” Ummansu Munnu tace” to Ku gaida gida Ku gaishe min da Umman taku ” mukace “zataji sosai wallahi.
Muna futa na warce Dari biyar din hannun Munnu nace.” Bani to salon mu manta mu tafi ki rike ko ai na gano ki” Munnu tace” to mayyar kudi kar ki jimin ciwo a banza” Mimi tace “Munnu har kij tuna min da wani Abu da ya faru shekaran jiya” Nan Mimi ta kwashe haduwar mu da guy nan ta fada mata harda watsa masa kud’in da nayi
Munnu ta dinga min masifa kamar wata uwata take “fadin WALLAHI kin cuce mu na rantse da ina gurin sai nayi miki duka kuma na tsinka ki a gurinsa ke wacece da zakiyi watsa da kudi masu yawa a daure a kyauwa ‘yar bura uba kina fama da kod’add’iyar atampar ki haitaget sai shegen girman kan tsiya malam” ta k’arashe maganar cike da takaicin abunda na aikata, Mimi dariya take kamar Cikin zai ciwo ni ko sakin baki kawai nayi INA kallon Munnu tana zuba min masifa kamar ta ari baki, dariya ta kufce min na fada soron wani gida na zauna inayi biyo ni sukayi duk da haka Munnu bata daina surutai ba, nace.” Munnu WALLAHI ban tab’a ganin me mugun son kudi ba irinki tabd’ijam!!! Munnu!! Na fada ina dariya. Tace” wallahi da ina gurin sai naje na tsince kudin na bashi hakuri, Um!!!! A wannan zamani yanda kudi suke wahala ana bahariyar tsiya” na mike tsaye tare da fadin”in kina so sai in raka ki idan zaki same shi ki bashi hakuri dama na manta handbag dina a gidan shi” Munnu tace”wallahi muje zan bashi hakuri sai dai Allah yasa ya bamu kudi” bani kadai ba har Mimi dariya take, nace” Munnu ya ishe ki WALLAHI kar ki mai damu mahaukata a hanya sai faman dariya kike saka mu. Tace” Ku muje na daina” muka futa daga soran gidan muka cigaba da tafiya babu Wanda ya sake cewa komai. Daf da zamu shiga gidansu Hafsa ne Munnu tace”Asama da gaske fa nake muje gidan guy nan don Allah” nace” zamu je in dare bai yi ba”. Mimi dai shiru tayi mana muka shiga gidansu Hafsa da sallama. Tana zaune kan kujera ‘yar tsungo tana gyara wake ta mike da sauri saura kad’an ta zubar da waken nace” hankali dai ki zubar ki daku wallahi” da ihu!! Tayo kanmu tana murna nayi saurin gocewa don kar ta rungume ni inji tsaminta, duk sun gane dalilina nayin hakan har ita Hafsa din, dake ta san halina bata damu ba, ta rike hannunsu Mimi muka shiga d’akinta, nace.” Ke Hafsa INA mamanku” kamar me jin tsorona tace”ta tafi unguwa” nace”sai kije ki siyo mana ruwa da Lemo mai sanyi”
Tace” Ke fa kin fiye Abu kinga ban kawo muku bane.” Nace “si hali na sani ne rowa da……… Na ki karasawa ina b’oye dariya Hafsa ta d’auke kanta cike da jin haushina ta cigaba da hira dasu Mimi ni kuma na dinga bin dakin Hafsa da kallo ina kunshe dariya. Ta mike da sauri tare da fadin” ai yau ina da manyan baki bari in sanya yaro ya siyo muku ruwa da lemo ta futa da saurin ta.