BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Mimi ta kalle ni had’e da bata fuska tace”Asma’u babu kyau cin fuska don Allah ki k’yale baiwar Allah nan haka wallahi tana d’aga miki kafa” nace” me nayi mata to” Mannu tace”ki daina kiranta da me warin HAMMATA” nace” na daina shikkenan” suka cigaba da shirarsu ni kuma ina kalle kalle a dakin can na hango Wani rubutu jikin bango anyi shi da blue din maka tare da wani k’aramin hoto an manna gurin
Mik’ewa nayi na isa gurin INA fadin “Su Hafsa ‘yan gayu ken….. Magana tace ta mak’ale a mak’o gwarona sakamakon gani fuskar guy nan jikin picture din dake manne a bango gaba na fad’uwa na bi rubutun ina karantawa, abunda nagani an rubuta ya gigita ni gami da dimauta ni. _Ilov my love my sweetheart yaya na farin cikina Amjadu ina bal’in son ko zuciyata tana azabutuwa da kaunar ka zan iya kashe kaina saboda kai ina mutukar kaunar ka yayanaaaaa!
Na nemi miyau na rasa a bakina ya bushe k’amas na fara tunanin meye hadin Hasfa da guy nan to? Gashi tana kiransa da yayanta kai duk yanda akai da akwai alamar tambaya, idan Hafsa suna da alaka da guy nan me ya jawo musu talauci haka duk tsiya si zai taimaka musu.
Motsin shigowar Hafsa naji nayi saurin komawa na zauna jikina na tsiyayar da gumi, Sam su Mimi ba su ankara da komai ba suna can suna hira, Hafsa ta shigo dakin hannuta rike da ledar ruwa pure watar da Lemo cocarcolar a ciki guda uku ta aje gabanmu tunda ta shigo nake zabga mata harara ina mata wani irin kallo, ita ko sai washe baki take tana mana labari,, sai dariya take tace”Asma’u ga lemon nan” hararata nayi ita da lemon nata ta d’auke kanta kurrum tana murmushi.
Hirarasu sukeyi babu ni a ciki sai dariya suke yi Hafsa sai tsoma ni take cikin hirarar tasu ina gwaleta.
Daf da magariba nace “Ku tashi mu tafi haka ke Munnu dama a gida kike”. Mik’ewa sukayi a tare Munnu tace.” Kin manta da maganrmu ko”? Nace” ban manta ba” nayi waje na kyalesu tare suka futo har Hafsa ta raka mu har bakin titi tana godiya sune kawai suke amsa mata ni ko ko kallo bata ishe ni ba.
Har aka idar da sallahr bamu samu abun hawa ba kun San dai tadda titin k’ok’i yake a baude bayan haka kuma muna tsakiyar kasuwar kurmi. Sai muka fara tafiya a kasa, gashi gari ya soma duhu, Wani me a dai-dai sahu yazo ya tsaya gabamu tare da fadin ” INA zakuje ‘yan mata “? Nace.” Rijiyar zaki scound get Cikin Jambulo ” Mimi ta kalle ni da sauri nima na zare mata ido tare da fad’in” in zakije kawai ki shiga mota mu tafi.” Baki na rawa tace ” INA tsoron fadan Umma kina ji fa tace.” Kar mu Kai magariba ba ko.” Ko sauronta banyi ba naja hannun Munnu muka shiga Mimi ta shigo duk jikinta a sanyaye mai a dai-dai ta yaja motar muka tafi.
Tofa
My fans ko me zai faru a haduwar Asma’u da Amjad a karo na biyu
Ku muje zuwa dai
21/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO
mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.
24
Dai-dai jaction muka sauka nace “Mimi bashi kudinsa” nan take ta ciro Dari biyar ta bashi ya dauki Dari uku ya bamu canjin Dari biyu, muka tsalla a nutse. Estate din shiru kamar babu wani mahalukin da take rayuwa a cike sai dai haske dal-dal a ko ina duk da cewar gidaje uku ne kawai a ciki,muna shiga karnukan da suke ciki suka fa ihu!! Tare da yowa kanmu duk suka tsorata ni ko na dake yare da cewa”idan kuna nuna razanar Ku a fili sai su zata b’arayi ne.” Munnu tace.” Wallahi asma’u na fara da na sanin zuwa fa” gaba nayi ban saurare ta ba, suka biyo ni a baya. Daga can nesa na hango shi ya futo daga massalacin dake jikin gidansa, zai shiga gida yana sanye da doguwar jallabiya fara tas!! Irin ta Larabawa kwata-kwata su Mimi basu ganshi ba nice na ganshi, nima kuma da suffar shi na gane shine. Muna zuwa bakin get din me gadi ya bimu da kallo irin na tuhuma nayi saurin cewa” munzo gurin me gidan ne.” Kallonmu yake cikin nazari yace.” Kunyi b’atan kai ‘yan mata banan bane” nace” kaga malam wai ba nan bane gidan Amjad ba” yace” nan ne ‘yan mata” cike da bada umarni nace” to sai ka bude mana malam” yace.” Me gidan bai bada izini ba domin da yasan da zuwan Ku zai fada min a bude muku get Ku shiga” haushin sa ya kamani na masa wani banzan kallo tare da cewa” kai malam kalle mu da kyau ka gani ba tsiyace ta kawo mu nan ba arziki ne, kuma mu ‘yan uwan me gidan ne idan kana tamtama kaje ka tambayo shi kaji” kallona yayi naga yayi saurin risinar da kansa, dama ni haka nake da mugun kwarjinin tsiya in na zuba ma mutum idona baya iya ketare hukuncina to haka ce ta faru da me gadi bakinsa na rawa yace” bazan barku Ku shiga ba domun bansan da me kuke tafe ba, amma bari inje in Sanar da masu tsaron kofar shi halin da ake ciki.” Ya ya bud’e karamar kofar ya shiga yana k’okarin kullewa babu zato yaji an buge hannunsa yayi saurin cirewa na fada cikin gidan INA kiran su Mimi suka shiga da sauri, nace” tunda mun shigo si munyi me wuyar kuma.
Duk abunda yake faruwa yana kallonsu ta CCTV Camara d’inshi ya cire rigar jikinsa daga shi sai shout nickar da kwalin Lemo a hannunsa yana sha, murmushi ne kwance a fuskarsa yana mutukar mamakin taurin kai irin na yarinyar mamaki yake sosai yanda akai har suka samu nasarar shigowa bayan sun baza karnuka a gurin saboda tsabar kokari da k’arfin hali har tana buge get man d’insa tana shigowa ko ubanta ta aje masa a gida ihu! A fili yace.” Kome ta zo tayi min a gida oho cike da mamaki yake kallonsu ita dasu rambow tana fada suna fad’a kamar zata tsokane musu ido Wayarshi ya d’auka dake aje a gefansa ya nemo numbar Rambow yana d’auka yace.” Barsu su shigo” ya kashe wayar ba tare da ya tsaya yaji me rembow zai ce ba.
Rambow yace.” Kun fi sa’a Boss yace” Ku shiga amma da badan haka ba wallahi ba zaku shiga ba” hararsa nayi nace” shima ogon naku nakusa karya alkadarinsa” cike da mamaki Rambow ya bita da kallo jin abunda take cewa, hannun munnu naja muka shige DOMIN naga Mimi sai wani ja baya take.
Muna wucewa Doh-doh yace”wallahi ina jin tausayin yarinyar nan duk ranar da zata shiga hannun Oga sai ta gane shayi ruwa ne” Rambow yayi k’wafa tare da fadin” k’aryar rashin kunya ta dama.
A hankali muka tura kofar parlor muka shiga, sanyi kamshi ne ya buge mu mu dukan mu sai muka fara zare ido sosai nake karewa parlor kallo DOMIN zuwana na farko ban kalle shi ba, wow gaskiya na yaba da tsarin parlor gami da k’yatuwar sa, komai na parlor orange color ne ina mutukar son Abu orange Munnu tace.”Asama mun banu kizo mu koma kawai na fasa” nace ke dallah can tsorone daku wallahi Ku zauna ni inje dakin shi si na sani mybe ma baya ciki.
Mimi ta rik’o hannuna tana girigiza mun kai wai kar inje fuzge hannuna nayi nai gaba ba tare da na wai wayo su ba.”
Ganin tana nufo kofar shigowa ne yasa ya mike da sauri haske dakin ya kashe ya tsaya jikin bango yana sauraron shi gowarta. Ina bude kofa naga duhu d’un d’um!! Na gane inda makkuni yake aikuwa nafara lalube zab kunna”. Wani abu naji ina tab’awa shi ba gashi ba shi ba fatar jikin mutum ba gashi dai yafi yawa a jiki, gabana ya fara fad’uwa jin kamar hucin nuffashin mutum, hannuna na daga da niyyar in kunna futular domin na fara tsorata, da k’arfi! Amjad ya jawo ta kirjinta ya daki nasa ya zura hannunsa kasanta ya rik’o kwankwanso ta sosai inda baza ta iya guduwa ba, sannan ya mik’a d’aya hannunsa sama ya kunna futula, haske ya gauraye dakin.