BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Cike da tsoro na kura masa ido fuskarsa a murtuke shima nasa idon ya samun kamar zai cinye ni danya, munfi minti uku muna kallon_ kallo kafin nace.” Sake ni inyi abunda ya kawo in tafi.” Shiru yayi min bai CE komai kuma har yanzu idonsa na kaina yana kare min kallo inda naga ya fi kalla a jikina na kalla ina dubawa, sai naga kwaurina da ya futo waje dalilin yanayin dinki bayin saurin Jan mayafi na rufe ina hararsa, hannunsa yasa ya janye gyalen ya jefar kasa ya cigaba da bin jikina da kallo kamar tsohon Maya. Cikin ikon Allah kuma time din banji wannan azabban fleengs din Dana ke ji ba in ya kusance ni.

Karfina nasa da gaske nake k’okarin ture shi. Ko motsi kirki ya kiyi . muryar shi a harhad’e yace.” Me kika dawo kimin a gida”? Ko nuffasawa ban bari yayi ba nace.” Bana munafurci na dawo d’aukar handbag dina ne.”
[10/22, 8:58 AM] BintaUmarAbbale????: Kallo yake min kamar Wanda be tab’a ganina ba, gashi ya wani had’e fuskarsa tamau!! Yace.” Karya kike da akwai dai abunda ya kawo ki,babu wata handbag da kika manta.” Fuzge jikina nayi ina galla masa harara gefe na matsa ina bin dakin da kalo ko a ina zan ga handbag din oho min… Cikin tafiyar shi ta jarumai ya nufi bed d’insa ya zauna tare da Dora kafa daya kan d’aya yace.” Zo ki duba kayan ki inda kika aje ki fuce min daga d’aki”. Kai tsaye.. Na nufi bed d’in na fara duba bayan shi da lukunanshi,aikuwa sai na hango ta, da sauri na zura hannuna na d’auko abata. Bayansa na kalla naga ki juyo bai yi sai danna waya yake. Rike da ita a hannuna na tsaya a kanshi nace.” Sai sak’on da aka bani na bak’a” ya dago kanshi tare da cewa.” Ina jin fad’a min ki fuce ki bani waje” cike da taikacin yanda yake kyarata wai in fuce!!! Sai kace wata tinkiya nace.” Kai kaga bafa komai ne yasa nazo gidan ka ba da har kake k’okarin gaya min magana dama ko baka ce na fuce ba zan fuce in bar maka d’akin ka….. Ya katse ni ta hanyar fadin ” naji ki fad’i sak’on ki, ki futa min a d’aki fitinanniya kawai wa zakiyi wa preetanding ni nasan abunda ya k’ara kawo ki gurina kuma baza ki samu ba” ya k’arashe maganar cikin sigar rashin mutumci” zuciya ta kamar ta tsage saboda zafi nace.” Ni ba shashashar mace bace kuma ni ba irin ‘yan Matan ka bane wallahi ni nafi k’arfin ka bare in kawo kaina gurin ka ko abunda kayi min baya ma Allah ya isa.”

Murmushin gefan baki yayi ya d’an sosa sumar shi kad’an da Jan ido ya kalle ni still da murmushi a fuskarsa yace.” Ok naji ba abunda ya kawo bane kin tsaya kina Jan magana fad’a min sak’on ko in sa yanzu ayi waje dake domin bana bukatar ganin wannan mummunar fuskar ta ki bak’akirin!!!!!!!!!! Asamau da tsani ace mata mummuna lokaci guda hankalin ta ya tashi taji wani irin hawaye me zafi na k’okarin zubo mata da sauri! Ta aro jarumta da dauriya ta aza a ranta, wani kallon Tara saura kwata ta mai tace.” Wa kake da suna Amjad ko me?? Kai dai ka sani, bari kaji wani Abu da baka sani ba, kyau ba shi bane kyawun hali da nasaba me kyau da shi a ke tunk’aho Allah Ubangiji ya raba mu da kyau irin naku babu kyawun hali da nasaba me kyau Wanda nasan ni nafi ka nasaba da tarbiyya me kyau duk wannan iskancin da kake rashin tarbiya ne da rashin samun iyaye jajirtattu saboda haka tun wuri gwara ka koma islamiyya ka samo ilimin addini domin kasan meye banbanci kyau da muni.” Ina karasa maganar na nufi kofar futa ina da na sanin zuwa gidan. Kofar nake k’okarin budewa taki nayi-nayi na juyo a fusace! tare da kaurara murya ta nace” zo ka bude min kofa in futa daga wannan annobar” ina kallonsa ya mik’e ya nufo inda nake, fuskarsa na tsurawa ido kamar mala’ikan mutuwa take naji tsoro ya shiga raina na kauce daga bakin kofar, cike da k’arfin hali na dinga watsa masa kallo ko kallona bai ba ya bude kofar zai futa na biyo bayansa, da sauri hannunsa guda ya sanya ya ingiza ni ciki dakin na fad’i kasa, ko juyo wa bai ba ya rufe kofar tare da murza key! Na mike a zafafe! Na daki! Kofar dak’afata ina janta tun karfina ko motsi tak’iyi ihu!!!!! Na kurma sosai ina fad’in “Idan baka bud’e mun kofar nan na futa ba kai ba d’an hakan bane, d’an iska asharari”!! Duk yana jin haukan da take wai shi take zagi harda su d’an iska asharari wai ma meye alk’ar shi da yarinyar ne da har ta samu dama akan shi shine Mara tarbiyya Wanda iyayensa suka lalata shi, ya zama dole yarinyar ta karb’i hukunci a gurin shi, fuskarsa ya kara hadewa ya Isa tsakiyar parlor inda ya hango su Mimi tsaye bakin kofa suna zare ido dama yasan dasu tunda ya gansu cikin CCTV Camera, Cikin jarumta ya durfafe su,sai ga Munnu tana rawar k’afa ganin wani ingarmar namiji na kusan to su, cike da tsoro ta zube bakin kofar. Ita ko Mimi suma ne kawai bata yi ba daga ninsa tunda ya futo ta tsora mishi ido tana kallonsa wata muguwar soyayyar sa na kara nunkuwa a cikin zuciyarta. Kallonsu yayi a nutse yace.” Ku ne ‘yan rakiyar ta”? Munnu ta gyad’a kanta alamar “Eh bakinta na rawa tace” ina wuni” ko kallonta baiyi ba ya bud’e kofar parlor ya futa, minti biyar ya dawo yana kallonsu tare da fad’in” Ku tashi a mai daku gida”. Cikin dauriya Mimi tace” Asma’u fa”. Da gefan ido ya kalleta ya d’auke kansa tare da fadin.” Nace tazo a kai ku gida tace baza ta tafi ba so kuyi tafiyar Ku kawai Ku k’yaleta duk sanda ta ga damar tafiya sai ta tafi.” Jikinsu ya soma b’ari Mimi tace” kayi hakuri don Allah kaji”” miskilin murmushi yayi ya Dan Sosa kansa Wanda hakan ya zame masa jiki yace.” Ke ba laifina bane fa nata ne, kunga ni ita ta kawo kanta har gidana ta bude min daki ta shiga ta zage ni ta fad’a min duk maganar da tazo bakinta to babu laifi na” hanya ya nuna musu da hannu a karo na biyu yace.” Doh-doh na jiran Ku a mota a sauka lafiya.” Simi-simi suka wuce suna waiwaye gefe guda kuma suna mamakin abunda Asma’u ta aikata domin sun gazgata maganar sa saboda sanin halin kaifin harshe na Asma’u. Zama yayi a parlor ya rik’e kansa zuciyarsa na masa zafi sosai yake tunanin hukunci da ya kamata yayi wa yarinyar, murmushin mugunta ya saki da ya tuno wani abu kawai ya mike ya isa gaban TV ya kunna ya zauna cikin kujera yana kallonshi wani american film yake kallo ya manta da wata Asma’u dake d’akinsa a kulle sosai film din ya d’auke masa hankali.

Gajiya nayi da dukan kofar na zube bakin kofar ina mai da nuffashi wani abu me nauyi yazo ya tokare min a mak’ogwaro na a fili nace “wai me guy nan yake nufi ne da nine? Babu me bani amsa Mik’ewa nayi da sauri na Isa window na yaye labule INA lek’en waje tunani nake ko zan samu hanyar futa, ko alama babu wata hanya, nafi minti goma a tsaye a gurin gabana na fad’uwa, na juyo na kalli a gogo dake manne a dakin 9:53 na dare goma shaura minti bakwai kenan. Sai naji kafafuna baza su iya daukata ba, na duba wayata da sauri nake lalubar numbar Mimi na kira babu kudi a cikin wayar, da sauri na tafi cin bashi, da k’yar suka bani naira Hamsin dama suna bina bashi, Mimi na daga wayar nace.” Kuna ina ne”? Tace.” Muna gidan su Munnu yaushe zan koma gida ni kadai in cewa Umma me? Murya na rawa nace Mimi guy nan bai da mutumci wallahi ya kulle ni a d’akinsa” Mimi tace” Yace ke ce kika ce baza ki tafi gida ba”. Cike da mamaki nace” Mimi sharri yayi min kawai kyaleshi” tace” nasan kin masa rashin mutumci shiyasa yayi miki haka” ga yanayin yadda Mimi tayi magana na gane ranta a bace yake nace.” Mimi nayi masa din in zaki rama masa bisimillah” na katse wayar cike da taikacin ta wato ita bata jin ciwon kulle ni da yayi shi take k’okarin karewa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button