BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Alwala na dauro Nazo na tada sallah ta, bayan na idar zama nayi ina karatun alkur’ani a zuciyata har gari ya soma haske sao danayi izu biyar sannan nayi addu’a na shafa, agogo na kalla bakwai da rabi na safe, tunda ya futa ban kara jin motsin sa ba, na mike raina a cunkushe na futa dama kofar a bude ya barta, yana kwance kan 3sitar duk tsayin kujerar tayi masa kad’an saboda k’afafun shi ma kan hannunta suka sauka, idonsa a lumshe yake hannunshi da carbi me bala’in kyau yana ja ,tsayuwa nayi a kanshi a cushe nace “sai ka tashi ka mai dani gidanmu ko kuma ka sanya a mai dani.”
Bud’e idonsa yayi masu d’auke da son yin bacci ya zuba mata su. Kauda kaina nayi daga kansa domin Sam bana son in kara jin sha’awar sa cikin zuciyata so nake ma in ji zuciyata na masa muguwar tsana na har abada, zaune ya mike yana kallon a gogon dake daure a hannunsa, minti biyu ya dago kanshi yana kallona da idonsa Wanda babu digon kunya ya ciki muryar sa k’asa-k’asa yace.” Ki Bari 9:00 tayi yanzu Safiya ce bana futa irin wannan lokacin idan na muhimin abune zai futa dani ba.” Hannu na daga masa da sauri! Nace.” Wannan ba hujja bace, ni yanzu bana neman wata doguwar magana da kai abunda kayi min na barka da Wanda ya hallice mu.” Kansa ya sunkuyar k’asa yana dan murmushi ni kuma nayi masa tsaye a ka had’e da rik’e k’ugu d’ago kansa yayi yana kallona a karo na uku yace.” Shikkenan kije yanzu zan zo sai in Kai ki da kaina.” Nace.” Babu inda zan matsa daga gurin nan.” Sai ka tashi tunda na futo daga wancan dakin bazan kara komawa ba.” Hannunsa ya d’aga min duk biyun yace.” Ok ok naji. Kina min hayaniya aka yanzu zan tashi.” Nace ya fi maka.” Minti biyar ya kara a zaune ya mike da sassarafa ya shiga d’akinsa, tsaki naja ina watsa masa muguwar harara. Ba tare da sanja kaya ba ya bude kofar ya futo tare da fadin” muje kar ki cinye ni.” Yafad’a yana nuna min hanya, wuce wa nayi fuskata a murtuke, ina futa naga ya ranshi tsaye a bakin kofa wani mugun haushin su ya kamani na dinga watsa musu mugun kallo nayi wuce wata, INA kallonsa ya tsaya dasu suna magana, sannan naga ya tawo in da nake yana taka k’asa kamar zai tsaga ta. Wata mulmulalliyar mota naga ya bude ya shiga yace.” Shigo. ” kofar baya na bude na zauna bai ce min komai ba yaja motar me gadi ya bude masa muka futa daga gidan.sai sannan na sauke ajiyar zuciya. Tafiya muke babu Wanda ya kula Dan uwansa sai dai mu hada ido ta mirror dashi hararace take rabumu dashi, Sam! Fuskarsa bata nuna b’acin rai ko kadai. Gani yayi ya dauki hanyar Gidanmu nace.” Banan zani ba.” Ta mirror ya kalle ni a nutse yace.” Banan zaki fa kamar yaya.”? Nace.” E haka nace k’oki zaka kaini gidan ‘yan uwanmu in kasan ni.” Yace.” Ni ko nasan koki unguwar kakannina CE, abun da na kasa fahimta shine kince ba gida zakije ba INA so ki fada min inda zakije ko kuma yanzu in juya dake in da kike futo. Fuskarsa na kalla naga yanda ya had’e ta tamau! Tsoro ya kamani nace.” Gidan su Mimi ne tana can tana jirana.” Cike da zargi yace.” Ok kina nufi dama ba gidan Ku daya da ita ba.” Nace” wannan duk ba abunda ya shafeka bane kawai ka kaini inda nace.” Yace. ” idan nak’ifa”? Shiru nayi masa, gyada kansa naga yayi yace. ” sam ban yarda dake ba wallahi amma muje gidan in da kaina kuma sai kin kirawo min Mimi sannan zan barki ki futa daga motar nan.” Share shi nayi kawai. Ya kunna motar mu dauki hanyar zuwa koki.

Dai-dai kwanar gidan nace a sauke ni ya gyara parking tare da juyo wa yana kallona yace.” Kira ta a wayarki ta futo mugani.” Nace “bani da kudi a wayata.” Dube-dube ya fara cikin motar wayarshi yake nema tana gida, dafe kansa yayi na minti biyu ya dago kansa tare da kallona, handbag dina na rike da kyau domin nan wayata take, ganin yanda nake dama- dama da ita ne ya sa ya fuzge ta daga hannuna ya fara zazzage min kayan dake ciki. Akwalar wayata ta fad’o k’asa batir din ya yayi nasa guri dama baya zama sosai jikin wayar sai nayi masa ciko sunkuyawa yayi ya dauki wayar yana dubawa ina kallonshi yana sakin wani munafikin murmushi, sauri kauda kaina nayi cike da kunya da takaicin sa, batir ya sanya ciki da dubara ya kunna wayar INA kallonsa ya fara laluben ma’adanar aje numbobo har yazo kan sunan Mimi inda nayi serving numbar da Mimina ya danna kira minti biyu ta shiga har ta katse Mimi bata d’aga ba ya k’ara kira a karo na biyu tana shiga ta d’auka Muryar ta radau naji tana fad’in ” Asma’u kiyi kokari ki futo daga gidanan Wallahi hankalin ummansu Munnu ya tashi jiya Umma tayi mata waya wai anan zamu kwana tace.” Mata eh shine take tambaya ta ina kike.” Wayar ya mik’omin ba tare da yacewa Mimi komai ba,na karb’a da sauri hannun mu na haduwa da nashi ko a jikina nace.” Mimi ki futo bakin titi ganin nan kinjiiii.” Tace.” To ganinan zuwa.” Kashe wayar nayi nasa a jikin jakata naki kallonsa, Wanda INA kallonsa tunda nafara magana da Mimi cikin waya yake kallona ta mirror.

Mintuna goma na hango su Mimi ita da Munnu suna sanye da hijabi har k’asa, Sam hankalinsa basu cewar ina cikin motar nan ba tunda motar me tintac ce.
Kalle-kalle kawai suke suna Neman inda nake, kallonshi nayi nace.” Bude min kofa ga sunan suna nema na.” Kamar da dutse nayi maganar ya shareni murya a sama nace.” Kaji. “!!!!! Juyo wa yayi a hankali yana kallona naga ya Sosa kansa kad’an wani munafukin murmushi a fuskar sa, kauda kaina nayi Ina jijjiga murfin motar naji muryar sa a k’asa yana fad’in” Baby zanyi missing din wannan tsiwar ta ki sosai hummmm!! Asma’u mata masu darajah.!!! nayi saurin kallon shi jin ya ambaci sunana kamar shine ya rad’a min hararasa nayi kawai tare da d’auke kansa, ya b’ata fuskarsa yana kallona yace.” Na tsani tsaki! A rayuwata na lura dab’iar ki ce hakan kan mu rabu dake kar in k’ara ji kinyi min tsaki.” Cike da taikaci nake kallonsa nace.” Me zakayi min in na k’ara, ka tsaya kana neman magana dani kawai ka bud’e min k’ofa na futa.” Tsurawa mata ido yayi yana kallon tare da lumshe ido. Takaicin sa yasa nakasa cewa komai na tsani wannan d’an iskan kallon da yake min.

Shiko nashi b’angaran yaso ta k’ara masa tsak’in saboda ya samu yayi kissing d’inta na k’arshe sai ya ga takiyi masa, shine dalilin da yasa kawai ya zuba mata idonsa yana tunanin ya zaiyi sa ita. Kwantar da kujerar motar yayi ya hauro kusa dani. Da sauri na takure jikina jikin kujera ina kallonsa a tsorace gabana ya fara dukan uku-uku. Fuskarsa yake matsowa da ita dab da tawa na rintse idona da k’arfi tare da fad’in.” Kar kayi!!!! Ka bude min kofa na futa wayyo!!! Nace kar Kay……………..maganar tawa ta katse lokacin da naji saukar bakin shi ana wa. Ya fara tsotsar harshe ne cikin zafin nama!! Ajiyar zuciya na sauke tare da sakin jikina kan kujerar ina lumshe ido hannusa yasa cikin nawa ya rintse da k’arfi daya hannun nasa ya tallafo kaina dashi sosai yake kissing dina kamar wani mayunwacin zaki!! Mintuna kusan biyar muka kwashe cikin wannan halin kafin dmya sake ni ya koma gurin zaman shi, ido jazur na ke kallon k’eyar shi na marasa me zanyi, da sauri na fara dube-duben can na hango su Mimi suna k’okarin juya gida domin sun duba ni basu ganni ba. Kuka nasa sosai nace ” nace maka ka bude min ka bude min kak’i bud’ewa gasu can suna tafiya gida.” Hannunshi ya zura ya bud’e motar ya d’ora min kudi dauri biyu a jikina ya gyara zamanshi tare da fad’in .” A sauka lafiya.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button