BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
Da sauri na bud’e murfin motar na futa tare da watsa masa kudinsa kan kujera kamar zan kifa nabi bayan su Mimi.
24/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO
Mallakar_BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. _
What’s App number
08089965176
07084653262
Account numbar
1013851874
Ahamad Gwadabe
UBA BANK
Duk Wanda yake da buk’atar cigaba da karanta littafin nan naira Dari uku ne kacal sai ka tuntub’i numbobin waya ta gasu can a sama domin in fada maka yanda zaka biya
27
Kallo ya bita dashi yana daga cikin motar ya d’an ciji lips d’insa na k’asa had’e da gyad’a kansa motar ya kunna a hankali ya bar gurin. Sai da nazo dab da su sannan na kira sunan Mimi da sauri suka juyu jin murya ta duk suka bini da kallo cike da mamaki, tambaye-tambaye suka tsaya zasuyi min nace .” Ku muje gida.” Shiru sukayi da bakinsu muka kama hanyar gida babu me cewa komai. Sai da muka shiga gidan ne sannan gabana ya fad’i na fara tunanin wace irin k’arya zanyi wa Ummansu Munnu, tana kicin tana raba abun kari ta kalli a tsanake tace.” Asma’u Ku futa tare da ‘yan uwanki su dawo su barki ko da yake Mimi tace.” Gidan Kawu Yunusa kika wuce ko.” Da sauri nace. ” Eh wallahi can na kwana kuma da naje suka hana ni dawo wa wai sai na kwana.” Dariya Ummansu Munnu tayi tace.” Ai sun kyauta domin kuwa kema irin ‘yar Uwar ki ce ba kya Kai musu ziyara shiyasa, nayi dariya cikin wayan cewa nace ‘aikuwa suma haka suka CE.” Tace.” Sai Ku shiga ciki yanzu zan sanya a kawo muku kayan kari.”
D’akin Munnu muka shiga duka muka zube kan kujera hijab din wuyana na fuzge na aje shi gefe ina numfarfashi Mimi da Munnu sun ka zuba min ido kawai bakin su da alamar tambaya nace.” Wai meye kuke ta kallona ne kamar wacce kuka kama da kwarto.” Mimi tace.” Ba Dole mu kalle ki Asma’u Allah ya baki nasarar d’auko jakar ki amma ga dukkan alamu an sha artabu da guy nan ko.” ? Kafin in bata amsa Munnu tace.” Ni rigar jikin ki ma nake kallo tayi min mugun kyau lallai Ashe soyayya kuke dashi tunda gashi har da yi miki siyayya.” Nace.” Kinga Munnu inda kina son rigar zan cire in baki ne kawai a yanzu bana bukatar wani Abu da ya shafi guy nan domin bashi da mutumci ko kad’an.” Mimi tace.” Allah yasa dai bai miki komai ba.” Cike da takaici nace.” Mimi jiya naga masifa a rayuwa domin ban yi tunanin zan dawo gida da budurci na ba wallahi jiya guy nan sai da yayi min sintir kamar matarsa haka ya dinga mu’amula dani.” Dafe k’irjinsa sukayi baki na rawa Munnu tace.” Laifin ki ne tunda yace kizo ki tafi kika k’i.” Nace.” Munnu guy nan sharrin sa yafi k’arfin sa kawai ki barshi a inda kika ganshi.” Mimi tace.” Lallai Allah ya tsare ki amma nima nafi ganin laifin ki Asma’u.” Nace.” Dole kice haka mana tunda kina sonsa.”
Munnu ta kalli Mimi cike da mamaki! Nace hakane Munnu Mimi sonsa take tun ranar da muka fara ganinshi har da gudumawar ta ma naje gidan shi domin in fada masa.” Dariya Munnu tayi k’asa-k’asa tace.” Ki kai kanki dai ita me yasa Mimi dake tafi ki wayo bata je sai ke sarkin kankanba, tab!!! Gaskiya kin tsalle ke rijiya da baya.” Nace.” Ke dai bari Munnu dake d’an iska ne kuma wai sai ya zube min kud’i sai kace ce masa nayi su nake so.” Tace. ” suna ina kud’in”? “Na bar mishi abunsa cikin mota.” Tsaki tayi tace.” Kin kwafsa banza da kin d’auko abunki tunda jikin ki ya mora.” Hararata nayi nace “in d’auka yace dama su nake so hummm sharrin guy nan fa sai ya baki tsoro ni kam jiya si na dauki darasi na rayuwa.” Dariya kawai Munnu take sosai tace.” Meyasa bamu ganki ba da muka futa bakin titi.” ? Nace.” Ni ina ganin Ku ai.”. Ta ina kike ganinmu.”? Nace.” Ba kiga wata bak’ar mota ba a gefe.”? Munnu tace.” Au!!! dama kina cikin wannan azababbiyar motar.”? Nace. ” Eh mana ina ciki nayi-nayi ya bud’e yak’i sai da yaga kun tafi sannan ya bud’e min nan ma sai da nayi kuka.” Munnu ta kwanta tana ta dariya tace.” Lallai yau Asma’u kin had’u da Wanda ya fiki rashin mutumci tab!! Ammafa gaskiya guy nan ya burge ni ya kashe bakin rashin kunya.” Nace.” Munnu ke dai bari! Wallahi duk iskamcin ka akwai Wanda ya fika a duniyar nan.” Mukayi dariya ni da ita, duk wannan hirar da muke Mimi na kwance taki tanka mana na kalli fuskarta naga kamar tana cikin b’acin rai! Girgiza kaina nayi kawai saboda nasan abunda yake damun ta. Haka aka kawo mana abun kari muka karya Mimi sai faman salo-salo take taki sakin jikinta, nace.” Wai ke Mimi meye haka ne.”? Kallona tayi tare da fadin “me nayi kuma”? Tsaki naja nace ” ban sani ba.” Dan murmushi tayi tace.” Kin fada masa kuwa”? Cikin mamaki nake kallonta domin nagane inda ta dosa. Nace.” Mimi ina ta kaina yaushe na samu damar fada masa kina sonsa don Allah ki cire shi daga zuciyar ki, mu shafe babinsa a RAYUWAR mu.” Munnu tace.” Yau ranar mai da martani yazo. Kuna min dariya akan Shamsu kema gashinan so ya sark’e miki wuya hahahahaha” ta k’arasa maganarta tana kyalkyala dariya.
Mimi idonta yayi rau-rau kamar zatayi kuka na kalleta cike da mamaki girgiza kaina nayi nace.” Wallahi duk isa da k’asaitar namiji bai isa in masa kuka ba akan ina son shi kome ye sai dai ya gani a aikace,lallai Mimi a inda ba asan ma kina yi ba kike shirin yin kuk………kafin in k’arasa sai ga hawaye shar-shar yana kwaranya a fuskar Mimi.Ni da Munnu muka zuba mata kallo cike da mamaki!
Ita ko Mimi tun lokacin da taji Asma’u na bawa Munnu labarin abunda guy nan yayi mata taji wani irin kishi na cin zuciyarta wani k’aton Abu yazo ya tokare mata a mak’ogwaro sosai take jin kishin Asma’u saboda shirme irin nata ma cikin zuciyarta tana fad’in “dama ita yayiwa abunda yayi wa Asma’u n.” Cikin fusata! Na dinga balbalawa Mimi masifa nace.” Mimi ko kukan jini zakiyi bazan fad’a masa ba dama ni nace zan fada masa to yanzu na fasa fada masa idan kin damu kije da kanki ki fada masa aikin banza aikin wofi, yanzu akan shi kike kuka ? Mimi kinyi asara Wallahi. ” Munnu tace.” Kinga Asma’u ki k’yaleta mana saboda ke baki san masifar so ba shiyasa kike fad’in haka ni da ita duk mun San meye so saboda haka ki k’yaleta taji da abu guda.” Mik’ewa nayi nace.” Sai kuje Ku k’arata ke da ita kune wahallalu.” Futa nayi na barsu. ruwan Wanka na hada na shiga nayi a gurguje na futo, sunanan inda na barsu suna maganganu k’asa-k’asa nace.” Ke Munnu zo ki d’auko min kaya ga rigar nan na cire.” Da sauri ta mik’e ta bude akwatin kayanta tare da fad’in” gashinan zab’i Wanda yayi miki.” Ina mutukar son atampah a rayuwata nan na hango atampar Munnu da take masifar so. Wata supar ita na nuna, sai na ko a jikinta ta Ciro ta bani, na karb’a ina duba dinki nace “Allah yasa ta shige ni” domin dai munnu bata da wani kib’a duk cikinmu na fisu cika da kwarjini, da k’yar na zura rigar dake zani ne mara ado sai na daura kawai na zauna ina shafa mai a nutse nace.”Mimi ki tashi kiyi Wanka mu tafi ko inyi tafiya ta ne.”? Banza tayi min.nima sai na share ta na cigaba da kwalliya ta. Minti biyar tsakani ta mike ta futa na bita da kallo cike da tausayi wai Amjadu zata ce tana so har da kuka tabd’ijam Mimi ta had’u da jaraba.